Tsohon dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Maroune Fellaini, ya bayyana cewa bazai sake aiki tare da mai koyarwa Jose Mourinho ba duk da cewa wasu rahotanni sun sake danganta shi da komawa Tottenham.
Dan wasan Belgium din ya kasance daya daga cikin ‘yan wasan da Mourinho yafi so a lokacin da suna kungiyar Manchester United sai dai tun bayan komawar Mourinho Tottenham akace ya fara zawarcin tsohon dan wasan Eberton din.
Har ila yau, Fellaini, ya bayyana cewa bashi da burin barin kungiyarsa ta Shandong Luneng Taishan ta kasar China saboda haka maganar sake komawa domin aiki tare da Mourinho bata da tushe ballantana makama.
“Mourinho mutum ne na musamman a rayuwa ta kuma ina tura masa sakon waya shima yana tura min sannan muna kiran juna a waya ya karbi aikin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham saboda haka ina masa fatan alheri” in ji Fellaini
Ya cigaba da cewa “ Nasan babban mai koyarwa ne wanda kuma duk inda yaje yana samun nasara saboda haka ina masa fatan alheri sannan ina masa fatan samun nasara a aikin da yake gabansa amma a halin yanzu ina farin ciki a inda nake”
Fellaini mai shekara 32 a duniya ya zura kwallaye 22 cikin wasanni 177 din daya bugawa Manchester United tun daga kan tsofaffin masu koyar da kungiyar da suka hada da Dabid Moyes da Luis Ban Gaal da Mourinho
Sai dai ya bar Manchester United a watan Janairun wannan shekarar bayan da kungiyar ta kori Mourinho a watan Disambar shekarar data gabata kuma kawo yanzu ya zura kwallaye 12 sannan ya taimaka an zura guda biyar cikin wasannin daya bugawa kungiyarsa.