Abba Ibrahim Wada" />

Ba Zan Sayar Da Rigar Maradona Ba, Cewar Steve Hodge

Steve Hodge

Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila, Stebe Hodge ya bayyana cewa, rigar da marigayi Diego Maradona ya sanya ta a wasan kwata-fainal na gasar cin kofin duniya a 1986, ba ta sayarwa ba ce domin ta zama abar tarihi.

Wannan na zuwa ne bayan mako guda da yin watsi da kiraye-kiraye daga sassan duniya da ake yi masa matsin lambar akan dole sai ya sayar da rigar bayan rasuwar tsohon gwarzon dan wasan na Argentina.

Shi dai Hodge da Maradona sun yi musayar rigunansu jim kadan da kammala wasan na gasar cin kofin duniya a wancan lokaci da aka gudanar a kasar Medico kuma yanzu haka an rataye wannan riga a gidan ajiyen kayayyakin tarihi na kwallon kafa da ke birnin Manchester a Ingila.

Hodge ya bayyana cewa, ya yi ajiyar wannan riga tsawon shekaru 34, kuma kiris ya rage ya sayar da ita, yana mai cewa, mutane da dama sun sha kwankwasa masa kofar gidansa baya ga masu kiran sa da wayar tarho domin tuntubar sa kan ko zai yi gwanjon rigar.

Wannan riga ta shahara ce saboda da ita ce Maradona ya jefa kwallon da ta yi waje da Ingila a wasan cin kofin duniya shekararu 34 da suka shude saboda haka zaifi kyau ace an ajiye ta a gidan tarihi domin ci gaba da kallonta.

An Zargi Likitan Marigayin Da Kashe Shi

Daga kasar Argentina kuma hukumomin kasar ne suka gurfanar da likitan Diego Maradona a gaban kotu inda ake tuhumar sa da laifin kisan kai, kwanaki 4 bayan mutuwar gwarzon dan wasan duniyar.

Masu gabatar da kara a garin San Isidro kusa da birnin Buenos Aires sun sanar da cewar ‘yan Sanda sun kai samame asibiti da gidan Leopoldo Lukue domin tattara shaidu kafin su gabatar a gaban kotu.

Binciken ya biyo korafin da ‘ya’yan Maradona guda uku suka gabatar da suka hada da Dalma da Giannina da Jana sakamakon irin kular da likitan ya baiwa mahaifin su lokacin da ya gamu da bugun zuciya.

Lukue wanda yaki cewa komai kan tuhumar da ake masa, ya wallafa hotan sa da na Maradona lokacin da ya bar asibiti ranar 12 ga watan nan, kwanaki 8 bayan yi masa aiki a sibitin da yake duba dan wasan.

Maradona ya rasu ne ranar Laraba sakamakon bugun zuciya duk da cewa da farko an yi nasarar yin tiyata a kwakwalwar tsohon dan wasan kwallon kafar na Argentina kuma kocinta a farkon watan Nuwamba sai dai daga nan ne aka sanar cewa za’a yi masa magani kan jarabar shan barasa.

A matsayinsa na daya daga cikin shahararrun ‘yan kwallon kafar duniya, Maradona shi ne kyaftin na Argentina lokacin da ta lashe Kofin Duniya a shekarar 1986, inda ya buga wasa mai kayatarwa.

Maradona ya buga wasa a kungiyar Barcelona da Napoli lokacin da yake kan ganiyarsa, inda ya lashe Kofunan Gasar Serie A da kungiyar kwallon kafar ta Italiya sannan ya zura kwallo 34 a wasanni 91 da ya buga wa Argentina, inda ya wakilci kasar a gasar cin Kofin Duniya sau hudu.

Maradona ya jagoranci kasarsa a shekarar 1990 inda suka kai wasan karshe a kasar Italiya, ko da yake sun sha kashi a hannu Yammacin Jamus, amma ya sake jagorantarsu zuwa Amurka a 1994, sai dai an kore shi saboda samunsa da laifin shan kwayoyin kara kuzari.

Lokacin da ya komo karo na biyu domin sana’arsa ta kwallon kafa, Maradona ya sha fama da jarabar shan hodar ibilis kuma an haramta masa buga wasa tsawon wata 15 bayan gwajin da aka yi masa a shekarar 1991 ya nuna cewa yana shan kwayoyi.

An rufe Maradona kusa da mahaifansa a makabartar Bella Bista da ke wajen Buenos Aires sai dai an samu turmutsutsi, bayan da dubban mutane suka yi jerin gwano don ganin gawar a fadar shugaban kasa.

Daga karshe sai da ‘yan sanda suka bada hayaki mai sa hawaye, su ka kuma canza wa akwatin gawar Maradona wuri, bayan da jama’a suka balla kofar dakin da ta ke ajiye ta don yi masa ganin karshe.

An haifi Diego Armendo Maradona ranar 30 ga watan Oktoba na shekara 1960 wato ya mutu kenan ya na shekaru 60 da haihuwa, kuma an haife shi a wani gari mai suna Lanus dake karkashin mulkin babban birnin Buenos Aires.

Maradona ya na daya daga cikin yara hudu da iyayensa suka haifa. Tun ya na dan shekaru 11 a duniya a fara daukar hankalin jama’ar kasar Argentina game da irin hukumomin kwallo da ya lakanta, saboda haka wani mai koyar da ‘yan wasan Argentina ya dauke shi a cikin kungiyar kwallon yafa kanana ta kasar da ake kira Cebollitas.

Maradona yana da shekaru 12 ya taba yin hira da wai gidan Talbijin inda ya ce shi burinsa a duniya shine idan ya girma ya halarci gasar cin kofin kwallo ta duniya tare da kungiyar kwallon Argentina kuma ya dauko kofi.

A lokacin da ya cika shekaru 16 a duniya ya shiga kungiyar kwallon matasa ta kasa, inda ya zama jagoran ‘yan wasan kuma daga lokacin daya shiga wannan kungiyar har ya fita ba su taba cin wani kofi ba na kasa da kasa, amma ya saka kwallaye a raga har sau 115 a cikin wasanin 166 da ya buga.

Maradona ya fara samun damar farko a cikin kwallo a shekara 1979 a lokacin da aka yi gasar kwallan matasa ta duniya inda aka zabe shi dan wasan da ya fi buga wasa mai kyau a wannan shekarar.

Ya buga wasa a manyan kungiyoyin kwallo daban-daban kamar Barçelona ta Spain da kuma SSC Napoli a kasar Italiya inda ya taimakawa kungiyar wajen nasarori daban-daban da wannan kungiyoyin kwallo su ka samu.

Exit mobile version