Ba Zan Taba Mantawa Da Arsenal Ba A Rayuwa Ta, Cewar Wenger

LONDON, ENGLAND - FEBRUARY 10: Arsene Wenger, Manager of Arsenal reacts prior to the Premier League match between Tottenham Hotspur and Arsenal at Wembley Stadium on February 10, 2018 in London, England. (Photo by Laurence Griffiths/Getty Images)

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai horar da yan wasan Arsenal Arsene Wenger, ya yi bankwana da kungiyar cikin yanayi na kewa bayan kammala wasan da Arsenal din ta lallasa kungiyar Burnley da kwallaye 5-0 a filin wasa na Fly Emirates dake birnin Landan.

Wasan na ranar Lahadi ya baiwa Arsene Wenger damar samun nasarar jagorantar kungiyar ta Arsenal samun nasara a wasanni 475 daga cikin wasanni 826 da kungiyar ta buga a karkashinsa a gasar firimiya

Wenger ya fara jagorantar Arsenal a wasan farko da ta lallasa kungiyar Blackburn Robers da kwallaye 2-0 a flin wasa na Ewood Park.

A jimlace cikin shekaru 22 da ya shafe yana horar da Arsenal, Wenger ya jagoranci kungiyar lashe kofunan gasar firimiya guda  3 da kuma kofunan gasar FA suma guda  7.

Magoya bayan kungiyar Arsenal ba zasu manta da kakar wasa ta shekarar 2003/2004 ba, lokacin da kungiyar ta kammala baki dayan wasanninta a gasar ta firimiya ba tare an samu nasara akanta ba a karkashin mai horarwa Arsene Wenger.

Wenger ya bayyana ranar Lahadin data gabata a matsayin wata rana da bazai taba mantawa da ita ba a tarihin rayuwarsa kuma ya bayyana godiyarsa da farin cikinsa bisa halin dattaku da magoya bayan kungiyar suka nuna masa a ranar ta Lahadi.

 

 

Exit mobile version