Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Uncategorized

Ba Zan Taimaka Wa Ma’aikatan Bogi A Karamar Hukumar Kalgo Ba — Namashi Diggi

by Tayo Adelaja
September 23, 2017
in Uncategorized
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo, Alhaji Umar Namashaya Diggi ya bayyana cewa ba zan taimaka wa duk ma’aikatan bogi da ke cikin karamar hukumarsa ba  a Jihar Kebbi.

Shugaban ya yi wannan bayani ne  a lokacin da ya kammala wata ganawa ta siri da ya gudonar tare da Sarikin Gwandu da daraktocin  karamar hukumar Kalgo, iyaen kasa da kuma kansilolinsa da ma sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kalgo. Taron ya gudona ne a sakatariyar karamar hukumar Kalgo a wannan mako. Tare da cewa, makasudin shirya ganawar domin neman hadin kai don daidaita matsalolin da ya tarar a karamar hukumar tasa.

Diggi ya bayyana wa manema labarai cewa ba zai taba amincewa da duk  wani ko wata da a ma’aikatan bogi a  karamar hukumar Kalgo ba, ya ce  abin takaici ne  da ban mamaki kan yadda  aikin kananan hukumomi ya lalace saboda son ran da ake  sa wa  a  aiki gwamnati, “Saboda haka ni ba zan yarda da hakan ba a wannan karamar hukumar ba”, in ji shi.

Har  wa yau, ya ce “A matsayina  na shugaban hukumar Kalgo ba zan amince da  wannan tsarin biyan albashin dubu biyar  ba da na tarar  a lokacin da na karbi madafun iko a hukumar. Ya zama wajibi a matsayina na zababben shugaban karamar hukumar Kalgo, ya zama  dole n yi iya kokarina na ganin cewa na dawo da martabar aikin karamar hukumar kamar yadda ka’idar aikin gwamnati take da yaddar Allah”.

Ya ci gaba da cewa, ba zai lamunci yadda wasu ma’aikata ke karbar albashi kawai ba tare da aikin komai ga karamar hukumar. Tare da cewa, “Insha Allah zan gyara wannan matsalar ta yadda kowane ma’aikaci za a dubi matsayinsa na aiki, idon ba a bisa ka’ida yake  ba za a daidaita masa zama kamar yadda doka ta tanada”.

Bugu-da-kari ya ce,  “Daga  wannan wata na  Satumba da muke ciki   duk wanda  ba  ma’aikacin halas ba ne a karamar hukumar Kalgo, to ba zai samu albashin wannan watan ba. Domin na fito da wata takarda wadda za ta bayyana ma’aikaci na gaskiya. Lokaci  ya yi na samar da canji ga  ma’aikatun kananan hukumomin  a Jihar Kebbi”.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamna Al-Makura Ya Jinjina Wa Tsohon Sarkin Garaku

Next Post

Kungiyar ‘Yan Barandon Shanu A Benin Ta Yi Sabon Shugaba

RelatedPosts

Gwamnatin Kaduna Ta Yi Wa Karnuka 6,250 Allurar Rigakafin Cutar Rabis

Gwamnatin Kaduna Ta Yi Wa Karnuka 6,250 Allurar Rigakafin Cutar Rabis

by Sulaiman Ibrahim
21 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Gwamnatin jihar Kaduna ta samu nasarra...

Garkuwa

‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

by Muhammad
7 days ago
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta samu nasarar kubutar da...

Caca

Caca: An Kashe Mutum Uku Akan Naira 50 A Imo

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Rabiua Ali Indabawa, An bayar da rahoton kashe samari...

Next Post

Kungiyar ‘Yan Barandon Shanu A Benin Ta Yi Sabon Shugaba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version