Abdulrazak Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Babandede Ya Jagoranci Taron Dora Kwangilolin NIS A Sikeli Na Shekarar 2021

by Abdulrazak Yahuza Jere
February 12, 2021
in LABARAI
2 min read
Babandede Ya Jagoranci Taron Dora Kwangilolin NIS A Sikeli Na Shekarar 2021
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A kokarinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana cikin ayyukanta kamar yadda yake kunshe a manufar yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tarayya, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) ta gudanar da taron dora ayyukan kwangilolinta da aka aiwatar da wadanda ake kan gudanarwa, a sikeli, na shekarar 2021.

An gudanar da taron ne a ranar Laraba 10 ga Fabarairun 2021 ta hanyar hoton bidiyo.
Taron wanda hukumar take yi a duk shekara da shugabanta na Yanzu CGI Muhammad Babandede ya kirkiro, babbar manufarsa ita ce baza komai a faifai don tabbatar da ba a yi kumbiya-kumbiya da kashe-mu-raba a cikin ayyukan da hukumar ke yi ba.
Da yake jawabi a taron, CGI Babandede ya bay
Yana cewa makasudin kiran taron shi ne tsettsefe dukkan ayyukan kwangilolin da aka gudanar a 2020, da duba matakan da wadanda ake kan yi suka kai da kuma makudan kudin da aka biya, kafin daga bisani a duba rahotannin tantance ayyuka na manYan ofisoshin hukumar na shiyyoyi da jihohi na shekarar 2021.
Babandede ya nunar da cewa a baya, akan biya kudin kwangiloli ta man
Yan ofisoshin hukumar na jihohi amma sannu a hankali sai a yi watsi da su ba za a yi aikin ba. Ya ce wannan ne ya sa ya kirkiro da tara dukkan manYan jami’ai na shiyyoyi da kwanturololi na jihohi da kuma jami’an sashen bayar da kwangiloli da ke shalkwatar hukumar duk shekara a wuri guda, domin su duba kundin baYanan daukacin kwangilolin don tantancewa.
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na NIS DCI Sunday James ya fitar, ta yi baYanin cewa manYan jami’ai na shiyyoyi guda bakwai ne kacal suka halarci taron gaba da gaba, yayin da dukkan kwanturololi na jihohi suka halarci taron ta hoton bidiyo.
… Hukumar Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10
Babban Kwalejin Horas da ManYan Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) da ke Sakkwato ta yaye masu mukaman kananan da manYan mataimakan Kwanturola Janar da suka halarci kwas na 10.
Shugaban Hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya taya jami’an da aka yayen murna tare da yin kira a gare su, su yi aiki da abubuwan da suka koya da kuma kara wa hukumar cigaba, kasancewar ana sa ran ganin abubuwa da dama na kwazon aiki daga gare su a matsayinsu na shugabannin gudanarwa da ke tsakiya.
Babban Kwamandan Kwalejin ACG Isiyaku Yusuf ya gode wa shugaban hukumar Muhammad Babandede saboda goyon baya da gudunmwar da ya bayar da suka taimaka kwas din na 10 ya samu nasara, duk da cutar Kwarona ta kawo cikas ga abubuwa da dama.
Sanarwar da jami’in hulda da jama na NIS, DCI Sunday James ya fitar ta bayYana cewa an yi bikin yaye manYan jami’an ne ta hoton bidiyo wanda ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro da ke Sakkwato da Kwanturololin hukumar na jiha da kuma wasu kalilan daga cikin man`Yan shugabannin al’umma na Sakkwato.
Wakazalika mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad III ya albarkaci bikin yayewar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Layin Dogo Daga Nijeriya Zuwa Nijar: Wace Rawa Hukumar NIS Za Ta Taka?

Next Post

Editan Jaridar Rariya Aliyu Ahmad Zai Angwance Yau

RelatedPosts

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

by Abdulrazak Yahuza Jere
7 hours ago
0

  Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ayau...

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

by Abdulrazak Yahuza Jere
8 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim A karon farko a 2021, farashin mai...

Naira

Naira Na Shirin Sake Faduwa Warwas – FMDQ

by Abdulrazak Yahuza Jere
15 hours ago
0

Za Ta Iya Kai Wa Dala 500 Cikin Mako Mai...

Next Post
Editan Jaridar Rariya Aliyu Ahmad Zai Angwance Yau

Editan Jaridar Rariya Aliyu Ahmad Zai Angwance Yau

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version