A kokarinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana cikin ayyukanta kamar yadda yake kunshe a manufar yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tarayya, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta gudanar da taron dora ayyukan kwangilolinta da aka aiwatar da wadanda ake kan gudanarwa, a sikeli, na shekarar 2021.
An gudanar da taron ne a yau Laraba 10 ga Fabarairun 2021 ta hanyar hoton bidiyo.
Taron wanda hukumar take yi a duk shekara da shugabanta na yanzu CGI Muhammad Babandede ya kirkiro, babbar manufarsa ita ce baza komai a faifai don tabbatar da ba a yi kumbiya-kumbiya da kashe-mu-raba a cikin ayyukan da hukumar ke yi ba.
Da yake jawabi a taron, CGI Babandede ya bayyana cewa makasudin kiran taron shi ne tsettsefe dukkan ayyukan kwangilolin da aka gudanar a 2020, da duba matakan da wadanda ake kan yi suka kai da kuma makudan kudin da aka biya, kafin daga bisani a duba rahotannin tantance ayyuka na manyan ofisoshin hukumar na shiyyoyi da jihohi na shekarar 2021.
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na NIS DCI Sunday James ya fitar, ta yi bayanin cewa manyan jami’ai na shiyyoyi guda bakwai ne kacal suka halarci taron gaba da gaba, yayin da dukkan kwanturololi na jihohi suka halarci taron ta hoton bidiyo.