Abdulazak Yahuza Jere" />

CGI Babandede Ya Kaddamar Da Muhimman Ayyuka Biyu A Shalkwatar NIS

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da kalar fentin hukumar da aka sani a hukumance a sabon katafaren ginin fasahar sadarwar zamani da ake dab da kammalawa a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Babandede ya samu rakiyar tawagar mahukuntan NIS da kuma Injiniyoyin da ke kula da aikin na Kamfanin Julius  Berger, kamfanin da yake gudanar da kwangilar aikin.
Wakazalika, CGI Babandede ya qaddamar da famfon ruwa da aka gina a sashen da aka kebe na musamman don harkokin kasuwanci a shalkwatar hukumar. Duka abubuwan biyu dai an kaddamar da su ne a rana guda, yau kenan.
Shugaban na NIS, ya yaba wa tawagar Injiniyoyin hukumar bisa kwazon da suka nuna wajen kula da sanya ido a kan aikin domin ganin ana gudanarwa cikin inganci kamar yadda aka san Kamfanin Berger da yi.
Ya sake jaddada bukatar kammala aikin da kyau da kuma amfani da kaya mafi inganci da suka amsa sunansu a ko ina cikin duniya a gine-ginen fasahar sadarwa wadanda za su tabbatar da lakabin da za a yi wa ginin na “Farin Watan Immigration Sha-kallo”, da zai rika janyo hankulan masu yawon bude ido da sauran masu kawo ziyara.
Exit mobile version