Abdulrazak Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Babandede Ya Yi Gargadi A Kan daukan Aiki Na Bogi Da Sunan NIS

by Abdulrazak Yahuza Jere
January 31, 2021
in LABARAI
1 min read
Babandede Ya Yi Gargadi A Kan daukan Aiki Na Bogi Da Sunan NIS
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya jawo hankalin ‘Yan Nijeriya su yi kaffa-kaffa da wata tallar daukan aiki da ake yayatawa a shafin intanet na bogi da sunan hukumar ta NIS.
Babandede ya ce hukumarsa tana nesanta kanta da wannan tallar wadda ya ce an tsara ne da nufin damfarar ‘yan kasa nagari. Don haka ya shawarci ‘Yan Nijeriya su kiyayi mu’amala da shafin na daukar aiki na bogi
Kamar yadda Babandede ya fada a cikin wata sanarwa da ta fito daga jami’in hulda da jama na NIS Sunday James, a duk lokacin da hukumara za ta dauki sababbin jami’ai takan tallata abin ne a sanannun manyan jaridu na kasa da gidajen talabijin da kuma shafinta na intanet mai adireshin: www.immigration.gob.ng kuma kyauta ne ba ko kobo.
Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda suka nemi aiki da hukumar da suka rubuta jarrabawa za a tuntube su ta hanyoyin sadarwa daban-daban da aka tantance amma ba ta shafin intanet na bogi ba.
CGI Babandede ya yi kira ga jama’a su kaurace wa mu’amala da wadannan mutanen tare da kai rahoton duk wani abu da ba su gane kansa ba game da daukar aikin NIS ta shafin intanet na hukumar: nis.serbicom@nigeriaimmigration.gob.ng, ko lambar waya: 07080607900 ko Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC ko kuma sauran takwarorinta da ke fadin kasar nan.
Har ila yau a cikin sanarwar, Babandede ya jaddada cewa daukar aikin NIS kyauta ne ba a biyan ko kobo imma ga wani ko ga hukumar, “don haka muna shawartar al’umma su guji biyan kudi ga kowa… NIS ba za ta tabe neman wani ya biya ko kobo ba a kan daukan aiki.”

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ohanaeze Ta Jinjina Wa Shugaba Buhari Shugabannin Rundunonin Tsaro

Next Post

Dubai: Za A Samar Da Allurar Rigakafin COVID-19 Kirar Kasar Sin Ga Jama’a A Kyauta

RelatedPosts

Garkuwa

An Kama Sojan Da Ke Kai Wa ‘Yan Ta’adda Kayan Sojoji A Zamfara

by Abdulrazak Yahuza Jere
14 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim "An kama wani jami’in soja da budurwarsa...

Aikin Wutar Mambilla  A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

Aikin Wutar Mambilla A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

by Abdulrazak Yahuza Jere
17 hours ago
0

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun nuna rashin jin dadin...

Bindiga

Gwamna Ortom Ya Yabawa Umarnin Buhari Na Hana Mallakar  AK47 Ba Bisa Ka’ida Ba

by Abdulrazak Yahuza Jere
18 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom a ranar...

Next Post
Dubai: Za A Samar Da Allurar Rigakafin COVID-19 Kirar Kasar Sin Ga Jama’a A Kyauta

Dubai: Za A Samar Da Allurar Rigakafin COVID-19 Kirar Kasar Sin Ga Jama’a A Kyauta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version