Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya jawo hankalin ‘Yan Nijeriya su yi kaffa-kaffa da wata tallar daukan aiki da ake yayatawa a shafin intanet na bogi da sunan hukumar ta NIS.
Babandede ya ce hukumarsa tana nesanta kanta da wannan tallar wadda ya ce an tsara ne da nufin damfarar ‘yan kasa nagari. Don haka ya shawarci ‘Yan Nijeriya su kiyayi mu’amala da shafin na daukar aiki na bogi
Kamar yadda Babandede ya fada a cikin wata sanarwa da ta fito daga jami’in hulda da jama na NIS Sunday James, a duk lokacin da hukumara za ta dauki sababbin jami’ai takan tallata abin ne a sanannun manyan jaridu na kasa da gidajen talabijin da kuma shafinta na intanet mai adireshin: www.immigration.gov.ng kuma kyauta ne ba ko kobo.
Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda suka nemi aiki da hukumar da suka rubuta jarrabawa za a tuntube su ta hanyoyin sadarwa daban-daban da aka tantance amma ba ta shafin intanet na bogi ba.
Har ila yau a cikin sanarwar, Babandede ya jaddada cewa daukar aikin NIS kyauta ne ba a biyan ko kobo imma ga wani ko ga hukumar, “don haka muna shawartar al’umma su guji biyan kudi ga kowa… NIS ba za ta tabe neman wani ya biya ko kobo ba a kan daukan aiki.”