Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Babban Alkalin Jihar Nasarawa Ya Saki Mutum 14

Alkalin-alkalan jihar Nasarawa, Mai Shari’a  Suleiman Dikko, ya saki mutum 14 wadanda suke zaman jiran shari’a a gidan kurkukun dake Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

Wadanda aka saki din sun hada da, Likita Emmanuel, Baba Dogs, Ali Ibrahim, Henry Andrew, Abubakar Ali, Abubakar Danjuma, Nasiru Usman da Musa Yahuza, sauran sun hada da; Umar Ibrahim, Danladi Shabu, Ali Jubrin, Peter John, Mohammed Abdullahi da Ibrahim Lolo.

Mai shari’a Dikko, ya bayyana cewa sakin mutanen da ya yi a yau Talata, hakan da yayi yana daga cikin ikon da doka ta bashi, ya yi bayani cewa ya kai ziyara gidan kurkukun ne don rage cunkoson da gidan kurkukun ya yi, da kuma tabbatar da ba’a ajiye wadanda basu da wani laifi ba.

‘Duba da yadda aikata laifuka suka yawaita a jihar musamman a yankin Mararraba, dole sai an hada hannu don tabbatar da anyi adalci.’ Dikko ya shawarci wanda aka saki da su zama masu hali na gari kuma su guji aikata wani laifi da zai sa a dawo da su gidan kurkukun.

Exit mobile version