Jamila Zhou" />

BABBAN BANGO: Alakar Kwararrun Aikin Gona Na Kasar Sin Da Kasashen Afirka Ta Yi Karfi

Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin tana karkashin jagorancin ma’aikatar aikin gona ta kasar Sin, ita kuma cibiyar nazarin kimiyya da ta kai matsayin koli ce a kasar Sin, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, cibiyar ta dukufa kan aikinta na yin nazari kan kimiyya game da aikin gona a yankuna masu zafi, domin kara samun ci gaba har ta zama cibiyar kimiyyar kasa wajen nazarin aikin gona a yankuna masu zafi.

Kana domin biyan sabbin bukatu yayin da ake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta fitar da sakamakon da ta samu zuwa ga kasashen Afirka, sassan biyu wato kasar Sin da kasashen Afirka suna gudanar da hadin gwiwa a fannin, haka kuma kokarin da suke yi ya taimakawa kasashen Afirka matuka wajen yin amfani da albarkatun aikin gona na yankuna masu zafi, tare kuma da cimma burin daga matsayin kasashen a fannin tabbatar da tsaron abinci a nahiyar ta Afirka.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin tana mai da hankali kan aikin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha dake shafar aikin gona a yankuna masu zafi, kana ta taba daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da goma dake tsakaninta da wasu kasashen Afirka kamar su Kwadibuwa da Najeriya da jamhuriyar kasar Kongo, kuma ta kammala aikin gina cibiyar gwajin fasahar aikin gona ta kasar Sin a kasar ta jamhuriyar Kongo a shekarar 2009.

Dang Duanmin, kwararren aikin gona ne dake aiki a sashen nazarin albarkatun tsirrai na yankuna masu zafi ya taba aiki a cibiyar gwajin fasahar aikin gona ta kasar Sin dake jamhuriyar kasar Kongo. Yayin aikinsa a kasar, ya yi kokarin koyarwa al’ummun kasar dabarar da ta fi dacewa yadda suke dasa shuke-shuke, kuma ya samu sakamako mai gamsarwa.

Dang Duanmin yana mai cewa, “Bayan kokarin da muka yi, wasu manoman da suka dasa kayan lambu a jamhuriyar kasar Kongo sun kubuta daga kangin talauci, har sun samu wadata.  A wancan lokaci, mun yi hayar wasu manoma daga kauyukan dake kusa da cibiyarmu ta gwajin fasahar aikin gona, mun yi gwaji a gonaki tare da su, mun dasa shuke-shuke tare da su, makasudin aikinmu shi ne domin koyar musu yadda za su iya yin amfani da dabarar da ta fi nagarta yayin da suke shuka tsirrai.  Misali yadda ake zuba ruwa cikin gona, aikin yana da muhimmanci, saboda lokacin zuba ruwa da kuma yawan ruwan da za a zuba, za su kawo babban tasiri wajen girman tsirrai, kana mu kan gaya musu cewa, dole ne a zuba ruwa a hankali, don kada a lalata shuke-shuken.”

You Wen, wadda aka haife ta a lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta kammala karatunta na Faransanci a kwalejin koyon harsunan waje ta Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin a shekarar 2008, har kullum tana kaunar aikin gona, a don haka bayan da ta kammala karatunta, sai ta tsai da kuduri cewa, za ta samu wani aikin dake da nasaba da aikin gona a yanki mai zafi. A shekarar 2011, You Wen ta samu damar yin aiki a cibiyar yin gwajin fasahar aikin gona wadda kasar Sin ta kafa a jamhuriyar Kongo, ta kasance mace daya kacal wadda ke aiki a cibiyar a wancan lokacin, shi ne karo na farko da ta je nahiyar Afirka.  Duk da cewa, ta gamu da matsaloli da dama yayin da take aiki a jamhuriyar Kongo, amma ta daidaita dukkansu tare da abokan aikinta.

You Wen tana mai cewa, “Hakika aikin gona yana da muhimmanci matuka, idan ana gudanar da aikin gona a kasar waje domin samar da taimako ga masu bukata, to aikin zai fi ba da ma’ana, ni ma ina sha’awar aikin, shi ya sa ina so in godewa tsarin samar da taimako ga kasashen Afirka da gwamnatin kasar Sin ta tsara, saboda na samu damar ne daga wajen, da gaske ina kaunar aikin, na yi kokari, na samu amincewa da kuma yabo daga al’ummun kasashen Afirka.”

Bayan kokarin da kwararrun aikin gona na kasar Sin suka yi, al’ummun kasashen Afirka da dama, ciki har da jamhuriyar Kongo, suna mallakar fasahar aikin gona ta zamani, hakan ya taimake su matuka wajen samun hatsi mai albarka. Bisa wannan dalilin ne, al’ummun kasashen Afirka sun nuna babbar godiya ta hanya mai halayyar musamman ga kwararrun aikin gona na kasar Sin

Dang Duanmin ya gaya mana cewa, kafin tashinsa daga janhuriyar kasar Kongo bayan da ya kammala aiki a cibiyar gwajin fasahar aikin gona ta kasar Sin dake kasar, ya samu tsarabar ban kwana mai daraja da aminansa na kasar nan dake nahiyar Afirka suka ba shi.  Yana mai cewa, “Ba zan manta da lamarin ba har abada, saboda tsarabar ta burge ni kwarai, a wancan rana, dagacin kauyen ya zo wurin da muka sauka da wani katon keke wanda ke cike da ’ya’yan itatuwa da dama, misali kwakwa da gwanda da ayaba.  Ya ce, ‘mun gode muku kwarai, kun zo kasarmu daga kasar Sin mai matukar nisa, domin koyar da mu fasahohi, da tunani, da ilmomi na zamani, ba mu san adadin godiyar da za mu nuna muku ba, kun sani cewa, muna fama da kangin talauci, babu abubuwa da yawa, ga shi mun kawo muku ’ya’yan itatuwa masu dadi, muna fatan za ku karba, mu ma muna fatan za ku sake zuwa kasarmu idan kun samu dama a nan gaba, mun gode’.”

Hao Chaoyun, shugaban ofishin kula da kimiyya da fasaha na sashen nazarin abun kamshi da abun sha na cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin ya taba halartar babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka gudana a watan Oktoban shekarar 2017, shi ma yana kaunar aikinsa sosai.

Yayin da yake takalo magana kan aikin samar da taimako ga kasashen Afirka da cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin take yi, ya bayyana cewa, yankunan dake dacewa da shuka tsirrai na yankuna masu zafi a kasar Sin ba su da yawa, amma daukacin yankunan a fadin duniya sun kai muraba’in kilomita miliyan 53, a don haka kasuwar cinikin tsirrai na yankuna masu zafi tana da girma.

Hao Chaoyun yana ganin cewa, kamata ya yi cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin ta sanya kokari domin samar da hidima nagarta ga aikin gona na kasar Sin, ta yadda za a ciyar da aikin gonan kasar gaba yadda ya kamata.  Ban da haka kuma, ya zama dole cibiyar ta yi kokarin yada sakamakon da ta samu zuwa ga kasashen waje domin samar da hidima gare su, dalilin da ya sa haka shi ne domin aikin yana da babbar ma’ana a fannoni biyu.  Ya ce, “Da farko dai, idan cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin ta taimakawa sauran kasashen duniya a fannin raya aikin gona a yankuna masu zafi, to, lamarin zai kara habaka tasirin kasar Sin a fadin duniya, haka kuma zai kara kyautata kwarjinin kasar Sin a fadin duniya kamar yadda ake fata.  Na biyu, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen aikin gona zai taimakawa kasashe masu tasowa domin su daga matsayinsu na fasahar aikin gona, har za su iya samar da kayayyakin aikin gona masu albarka kuma masu inganci, da haka al’ummun kasashe masu tasowa za su samu alfanuwa, har zaman rayuwarsu zai kyautatu sannu a hankali.”

Tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kwararrun aikin gona na kasar Sin wadanda suka tafi kasashen Afirka domin samar da taimako ga al’ummun nahiyar sun karu sannu a hankali, kokarin da suke yi ya amfanawa al’ummun kasashen Afirka matuka, kwararrun su ma sun samu sakamako mai gamsarwa daga aikin.  (Jamila Zhou, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

 

 

 

Exit mobile version