Abubakar Abba" />

Babban Bankin Nijeriya Ta Samar Da Dala Biliyan 39 Don Karfafa Naira A 2018

Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewar, daga cikin watan Janairun zuwa watan Disambar shekarar data gata ya zuba kimanin dala biliyan 39.9 don kare darajar naira a kasuwar musayar kudade ta kasar waje. F
Fashion bakin da akayi akan kudin musayar da aka zuba a cikin tattalin arzikin kasar nan a zango na hudu na roton CBN ya sanar da cewar, an zuba dama biliyan 39.9 don a daukaka darajar naira.
Dama can, wani lokacin CBN yana samar da dauki a kasuwar ta musayar kudi kimanin sati uku da suka shige, inda daukin yake taimakawa wa sassan kasuwanci a kasuwa da kuma ga sauran fannonin masana’antu kamar fannin noma, masana’antu da kuma matsakaitan sana’oi.
Masu mu’amala suna bukatar kudin musayar na kasar waje don biyan kudin makaranta, kudin asibiti, na tafiye-tafiyen BTA da sauran su.
A bisa fashin bakin da akayi akan daukin ya nuna cewar, CBN ya zuba jimlar kimanin dala biliyan 10.97 a kasuwar ta musayar kuaden kasar waje a farkon zangon 2018.
A lokacin zango na biyu, adadin ya ragu daga dala biliyan 3.09 zuwa dala biliyan 7.89, inda kuma a zango na uku na 2018 kudin da CBN ya zuba suka kai dala biliyan 3.99 a zango na biyu daga biliyan 7.89 zuwa dala biliyan 11.88.
A zango na hudu kuma, fashion bakin da akayi akan tattalin arzikin kasar nan ya nuna cewar, CBN ya zuba dala biliyan 9.18 a kasuwar ta musayar kudi.
Bugu da kari, fashion bakin da akayi na zango na biyu CBN ya zuba dala biliyan 10.97, inda hakan ya nuna cewar, CBN ya samar da dala biliyan 1.58 saboda saye da sayarwar da akayi a kasuwar ta musayar kudi, inda kuma aka samar da dala miliyan 740, da dala biliyan 2.55 da kuma dala biliyan 6.11 na musaya ga masu sayar da kudaden kasar waje.
Har ila yau, daukin da aka bayar na dala biliyan 7.89 CBN ya yi hakan ne a zango na biyu, inda kuma aka samar da dala biliyan $1.8 da dala biliyan 1.04 ta musaya da dala biliyan 1.5 ga BDC da kuma kwangilar dala biliyan 3.47.
A zango na uku na shekarar data gata, CBN ya samar da daukin dala biliyan 11.88 da dala biliyan 2.16 da dala biliyan 1.23 da dala biliyan 2.41 ga BDC da kuma kwangilolin dala biliyan 3.24.
Har Ila yau,a zango na hudu na 2018, CBN ya samar da daukin dala miliyan 820, dala miliyan 130 dala biliyan 2.98 ga BDC da dala biliyan 2.98 da kuma dala biliyan 3.15 ta kwangiloli.
Rahoton ya ce, jimlar dala biliyan 9.18 CBN ya sayar ga dilolin da aka amince dasu a zango na hudu na 2018, inda hakan ya nuna cewar, ya kai kashi 16.1 na raguwa a zango na uku na 2018, amma kashi 80.6 yafi ma sama da aka zayyana na 2017.
An kuma bayar da daukin dala biliyan 3.15 data kai kashi 34.3; sai sayar da BDC da ya kai dala biliyan 2.98, inda ya kai kashi 32.5 na masu zuba jari da masu fifar da kaya masu ya kai dala biliyan 2.09, inda ya kai kashi 22.8 said kuma cinikayya a tsakanin bankuna ta kai dala miliyan ,82, inda ta kai kashi 8.7 sai kuma hada-hadar musaya ta kai dala biliyan 0.13,inda ta kai kashi 1.5.
Musayar ta naira da kuma dala ta ragu da kashi 0.2 zuwa naira 306.70 daidai da dala a karshen Satumbar 2018.
Har ila yau, sashen BDC, ya ragu da kashi 0.9 zuwa kashi 0.01 a cikin zangon da ya wuce na 2017 zuwa naira 362.42/daidai da dala kuma na masu zuba jari da fitar da kaya masu ya kai naira 364.27 daidai da dala, inda ya kai kashi 0.5 hakan kuma ya nuna cewar an samu raguwa a zangon da ya gabata na 2017.
Fashin bakin da akayi akan tattalin arzikin kasar nan ya nuna cewar kudin da suka shigo daga kasar waje sun kai kashi 2.8 daidai da dala biliyan 27.64 a karshen Disambar 2018.
Bugu da kari, fannin mai ya samu jimlar dala biliyan 3.02 ya nuna cewar, an samu raguwar kashi 14.5 a zangon da ya gabata.
Acewar rahoton, an samu dala biliyan 11.49 a ranar 31 ga watan Disambar shekarar data gata a fannin da baida nasaba da mai, inda ta naira zuwa kashi 22.5 sama dana zango na uku.
Dogon fashin bakin da akayi na rahoton ya nuna cewar, kudin musayar na kasar waje sun kai dala biliyan 13.13, inda hakan ya nuna cewar sun ragu da kashi 6.1 kasa dana zangon da ya gabata.
Da yake yin jawabi akan tsarin na kudin musayar kasar waje wani farfesa a jami’ar jihar Nasarawa Farfesa Uche Uwaleke, ya yi kira ga Babban Bankin Nijeriya CBN da ya samar da dabaru don baiwa masana’antu dake cikin kasar nan daukin da ya dace, inda kuma ya yi nuni da cewar CBN ya taimaka matuka wajen samar da tsare-tsare wajen ciyar da masana’antun dake kasar nan, musamman yadda ya hana shigo da kayayyaki guda 41 da aka haramta shigowa dasu cikin Nijeriya.

Exit mobile version