A jiya Alhamis ce, babban bankin Nijeriya ya shelanta cewa ya zuwa yanzun ya kwato naira bilyan 60 daga bankunan da suka aikata laifukan cirewa masu hulda da su kudade ba bisa ka’ida ba.
Babban bankin ya ce har ma kuma ya mayar wa da mutanan da aka cirewa kudaden kudaden su.
Hakan yana zuwa ne a lokacin da babban bankin y ace ya fara wani shiri na samar da guraban ayyuka milyan 10 a nan da shekaru biyar ta hanyar zuba jari a fannin Noma, ta hanyar amfani da wasu kayan amfanin gona guda 10.
Da yake Magana a wajen taron yini biyu a kan harkokin banki a Owerri, ta Jihar Imo, daraktan sadarwa na babban bankin, Mista Isaac Okoroafor, cewa yay i an samu nasarar kwato kudaden ne ta hanyar amfani da matakan tsaro na babban bankin.
A cewar sa, an kwato kudaden ne a sakamakon kuken da sama da masu hulda da bankuna 13,000 suka kai a kan cewa bankunan suna cire masu kudade ta hanyoyin da ba su kamata ba.
Okoroafor, ya kuma bayyana cewa babban bankin ya dauki matakan ladabtar da bankunan da suka aikata laifukan, sannan kuma babban bankin ya tsaye a kan ganin ba wani banikin da ya zalunci masu hulda da shi.
Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga masu hulda da bankuna da su kai karan dk wani bankin da ya cuce su ta hanyar cin masu kudade ba bisa ka’ida ba.
A kan haka, mai Magana da yawun babban bankin ya bayyana cewa sama da ayyuka milyan 10 ne bankin zai samar a Nijeriya a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Ya kara da cewa, ayyukan da za a samar sun shafi wasu kayayyakin amfanin gona ne kamar Auduga, Rogo, Manja, Cocoa, Masara, Tumaturi, kiwon Kaji, Kiwon Kifi, Kiwon dabbobi da samar da madara.
“Za kuma mu samar da irurruka masu bayar da sakamako mai kyau ga manoma.
“Za kuma mu samar masu da hanyoyin sarrafa su ko kuma masu siyan amfanin gonan na su tun ma daga gonakin na su da zaran sun girbe su.
“In muka koma a kan noman rogo kadai a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar nan, wannan zai samar da akalla guraban aiki milyan guda.
“Manufarmu ita ce mu bunkasa ayyukan noma a duk sassan kasar nan kamar yanda abin yake a can baya. wannan kuma shi ne hanya mafi sauki wajen gina ingantaccen tattalin arziki,” in ji shi.