Wannan ita ce ƙarashen hirar da muka faro muku makon jiya da fasihin mutumin nan mai suna ADAMU ISA HUSAWA wanda Allah ya yi masa baiwar ƙere-ƙeren na’urori daban-daban. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da hazaƙin.
Waɗanne ma’aikatu ka taɓa kai rubutu neman tallafi ba ka samu ba?
Tun a zamanin gwamna Isa Yuguda a lokacin da aka fara tunanin ma za taimaka min shi ne a lokacin da muka je wani taron baje kolin fasaharmu, na samu nasara a mataki na biyu, wanda hakan ya bani damar tafiya wani gasar ƙasa-da-ƙasa a Indonosiya a can ma na je na yi nasara na dawo.
Bayan nan na zo na je Brazil na kuma je Ƙatar duk kuma gasar baje fasaha ne ya kaini, bayan waɗannan ƙasashen kuma na je Afrika Ta Kudu, kuma na je Singafo, kuma ina dawo wa Nijeriya da sakamako mai kyau a duk fitar da na yi. Dukkanin waɗannan fitar da na ke yi zuwa gasa ƙasashen waje gwamnatin Isa Yuguda ce ke ɗaukar nauyin fitarmu. A wannan lokacin ne aka tashi kamar za a taimake ni amma abun ya zama wani abu daban.
Ganin ka ce shi gwamnan Isa Yuguda ya ɗauki nauyinku wajen fita ƙasashe don ganin kwazon ka. Ba ka yi tunanin sake zuwa gare shi domin neman taimako ba?
A lokacin akwai waɗanda suke shugabantar irin hidimar da muke yi na baje kolin ƙere-ƙere, su ne ke da alhakin kaiwa gwamnan jiha rahoton waɗanda suka ci da waɗanda suka yi ƙoƙari, kasantuwar irinmu suna da yawa shi gwamna a rubuce ake ba shi kawai. Wasu lokutan ma muna gani ba yaran da suka ci ba ne ake kai su, sai a canza sunan waɗanda suka ci a sa sunayen wasu a biya masu su fita, don haka gaskiya ban samu damar ganin shi gwamnan ba har ya sauka.
Irinka ba ku taɓa zuwa maa’aikatar mata da matasa domin neman tallafi ba?
Ina jin tun lokacin da na dawo daga ƙasashen waje, mun je mun rubuta takardun da aka ce mu rubuta mun rubuta amma shiru. Kai a wannan gwamnatin ma kawai taron da aka shirye mana ta asusun bankin duniya wanda suka shirya akan harkar ƙere-ƙere muna dai sa ran samun wannan tallafin don inganta wannan sana’ar.
Ka bayyana cewar kana fitar da na’urori har wasu jihohi, shin akwai wata alama da kake sanyawa a jiki ne wanda ke nuna kai ka ƙera abun?
Eh muna da sifika da muke mannawa a jikin duk manyan na’urar da muka ƙera da kanmu. Da kuma sanya addireshinmu da lambar wayarmu da sunan kamfaninmu, dukka muna sanyawa a jikin. Sannan kuma mukan sanya HCC da siga mai kyau.
A daidai wannan lokacin, mene ne ya fi damunka a wannan sana’a?
Abun da ya fi damuna na ɗaya dai shi ne rashin isassun kayan aiki, wanda sai na yi ta buga-buga, na je can na je nan ina neman aron kayan haɗa wata na’urar, ina da wasu na’urorin amma gaskiya ba su kai ma rabin abubuwan da na ke da buƙata ba. na biyu kuma zan iya zama na ƙirƙiri abu, na zana yadda zan yi amma kuma yinsa sai ya zama min matsala, domin ta yadda zan sayo kayayyakin sai ya zama matsala a gare ni, saboda duk lokacin da zan yi abu a farko ya kan ci min kuɗi sosai. Idan na gama duba basirata na gagara fitar da abun da na ke so a sakamakon rashin kayan aiki sai na ji abun ya fita min a kai, amma da duk lokacin da na gama zana abu a takarda kawai ƙaddamarwa ya rage min ai da ci gaban ba a ma magana.
Yanzu da kake iya fitar da wasu abubuwa har su yi aiki, shin burinka ya cika ko kana da saura a nan gaba?
Gaskiya ni fa ina da buri da yawa, domin yanzu haka da na ke magana da kai ina da abubuwa a ƙasa waɗanda na yi zane a kansu kawai na bar su haka nan. Wanda sai na samu sarari kafin na kai ga yin su. Misali, babban burina ina son idan na yi tunani ina son na ƙera wani abu duk yadda zan yi na samu kayayyakin aiki da kuɗaɗen da za su gudanar min da waɗannan ayyukan, gaskiya wannan shi ne burina ina sa yin abu na yi kawai. Ina kuma da burin duk bayan wata biyu na ke fitar da sabon abu wanda kowa zai ke amfana da shi. Sannan abu na uku kuma ina son koyar da wasu irin wannan fasahar da Allah ya yi min, ina da buri koyar da matasa sosai.
Kana da wani kira ga gwamnatoci wajen taimaka wa ire-irenku masu baiwa haka?
Eh akwai kira na sosai ma kuwa, tun da yanzu haka an maida hankali kan yadda za a dogara da kai ne, kamar sana’ar hannu da irin namu nan. Maganar gaskiya gwamnatoci ya kamata suke dubawa sosai, domin da irin ƙere-ƙere da fasahar nan ne fa ƙasashen waje suka ci gaba. Yanzu idan mun ce da man fetur kaɗai muka dogara, sai mu kalli ƙasashen da su kuma ƙere-ƙere suke tafiyar da komai su kuma kuma dogara, don haka ina kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai da su taimaka wa dukkanin matasan da suka tarar masu baiwa ko fasaha irinmu. Wasu ƙasashen idan suka samu irin matasa masu baiwar nan, sukan ja su ne su ajiye su guri guda suna lura da su gudanarwa da kuma mene ne za su iya tagaza wa ƙasarsu a bisa haka har a samu waɗanda za su iya fitar da muhimman abubuwan da za su taimaki ƙasar.
Mene ne shawarka ga matasa?
Shawarata ga matasa ita ce su rungumi abun yi, su kuma jure wa dukkanin abun da suka sanya a gaba. Su kasance masu yin abubuwan da za su taimaki al’ummanmu.
Tun da kake irin wannan sana’ar mene ne ya fi burgeka?
Abun da ya fi burge ni na ga na yi abu mai wahala kuma na sha wahala sosai amma bayan na fitar da abun da na ƙera jama’a su zo su yi ta murna suna amfana da wannan abun da ne ƙera ɗin. Gaskiya na yi abu a yi amfani da shi, shi ne ya fi sanya ni farin ciki na kuma ji daɗi sosai.