Babban Burina Na Karatu Na Zama ‘Nurse’ – Sadiya Abdullahi

Sadiya Abdullahi

Akan ce Dan’adam a duk inda yake ba a raba shi da buri. Tabbas haka ne, bakuwarmu ta Adon Gari a wannan makon ta bayyana cewa babu abin da take buri na karatu a rayuwa illa ta zama malamar asibiti. Kuma tana nan ta dage tana neman damar da za ta cika wannan buri. Har ila yau, a cikin wannan tattaunawa da ta yi da wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM, ta yi bayani a kan muhimmancin sana’o’i ga rayuwar ‘yan mata har ma da matan aure. Ga dai yadda hirar ta kaya kamar haka:

 

Da fari  za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki

Sunana Sadiya Abdullah, ni haifaffiyar Jihar Neja ce dake Karamar Hukumar Suleja, na yi firamari a Suleja na yi sakandiri a Kaduna road, to Alhamdulillah yanzu na gama.

 

Malama Sadiya Abdullah matar aure ce ko kuma ba matar aure ce ba?

A’a ni ba matar aure ce ba ce, amma muna niyyar yi in sha Allahu.

 

An kusa auran kenan?

A’a kin san aure mukaddari ne na ubangiji muna sa rai, na ce idan Allah ya kawo za mu yi ina fatan Allah ya ba ni miji nagari.

 

‘Yar kasuwa ce ko ma’aikaciya?

A’a ni ba ma’aikaciya ba ce ina ‘yan kananun sana’o’i dai.

 

Wana irin kasuwanci kike yi?

To ina dan siye da siyarawa kamar haka, kayan yara har ma da na manya. Takalma na yara da na manya hijabai sarkoki kome dai da kikasani na rayuwa idan mutum yacemin yana So ni kuma zanje nasiyo saina dan dora nawa na saida masa haka nakeyi.

 

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?

Eh to abin da ya ja hankalina har na shiga wannan kasuwancin shi ne bai wuci ina samun dan toro sisi ba, sannan kin sa mu ‘yammata auran waccan ya taso idan ba ka da kudin Anko, to ya za ka yi sai dai ka dora wa iyaye nauyi, idan iyayen naka ba su da shi ba za ka iya shiga cikin abokai ba sai a yi babu kai, amma idan kana ‘yar sana’arka ba ka rasa abin da za ka rufa wa kanka asiri ba.

 

Ba ki fada mana matakin karatunki ba?

To matakin karatu na tun da na gama sakandiri ban je gaba ba, ina saran insha Allahu zan tafi makaranta idan na samu saboda ni ina da burin yin karatu in sha Allahu.

 

Wane irin kalubale kika taba fuskanta a sana’arki?

Eh to ba zan ce na taba fuskantar kalubale ba, sannan kuma ba zan ce na taba fuskantar kalubale ba, da ma shi mai nema yana tare da nasara ko in ce sa’a, sannan kuma yana tare da rashin sa’a, dole ne wata rana za ka ci riba wata rana kuma ka fadi, wata rana ma ka samu wanda zai hana ka kudin, wani kuma kafin ya baka sai ya wahalar da kai, ranka idan ya yi dubu sai ya baci haka sana’a ta kunsa sai kina da hakuri za ki iya yin ta.

 

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?

E gaskiya na cimma nasara tun da Alhamdulillah ina samu daidai gwargwado, na gode wa Allah, sai dai fatan Allah ya kara kawo kasuwa mai albarka.

 

A da can da kike karama mene burin ki?

Lokacin da nake karama ina da burin na zama likita yanzu ma ban fidda rai ba insha Allahu idan na kuma makaranta abin da zan karanta kenan.

Wane abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?

Abin da ya fi faranta min rai akan sana’a ta shi ne ina samun masu sayan kayana akai-akai ina jin dadin haka sosai, sannan kuma ina jin dadin idan wacce ta sayi kayana ta biya ni da wuri ko kuma daga an dauka a bani kudina ba sai ya kai wani lokaci ba.

 

Tawacce hanya kike bi wajan tallata sana,arki?

Ina tallata sana’ata wajen ‘yan uguwarmu haka, sannan kuma idan na sayo kayan ina daukan hotonsu na sa akan sutasus dina, da haka de nake tallatawa.

 

Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?

Ina so mutane su rika tunawa da ni da alkhairi na, wanda kuma na bata wa ina neman yafiya a gare shi.

 

Ga fita saro kaya sannan kuma ga siyarsu, kila kuma ba za a rasa wani dan aiki da kike yi wa mamanki ba, ko kila ma ke kike yin aikin gidan baki daya, ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?

Eh gaskiya ni nake aikin gidanmu kusan gaba daya ko ma na ce gaba daya, amma duk da haka wannan ba ya hana ni samun hutu idan na gama aikina, sai na dan kwanta na huta kafin wani aiki, kuma kasuwa ba kullun nake zuwa ba sai an nemi kaya.

 

Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?

Allah ya min albarka.

 

Wanne irin goyon baya kika samu daga wajen iyayanki da ‘yan uwanki?

Gaskiya sai dai na ce alhamdulillah iyayena suna da fahinta sosai sun ba ni goyon baya a kan sana’ata ba wata matsala haka ma ‘yan uwana.

 

Kawaye fa?

Su ma ba ni da wata matsala da su.

 

Me kika fiso cikin kayan sawa, da kayan kwalliya?

Abin da na fi so cikin kayan sawa shi ne dogowar riga, sannan kuma ina son kwalliya sosai

 

A karshe wace irin shawara za ki ba wa ‘yan uwanki mata?

Shawarar da zan bawa ‘yan uwana mata shi ne zama haka ba zai yi ba mu dage da ‘yan kananun sana’o’i ba za ki rasa taro sisi a hannunki ba ko budurwa ko matar aure ba sai kin jira sanda miji ya baki ba.

Exit mobile version