Babban burin dake cikin zuciyara shi ne ganin Karamar Hukumar Tarauni ta dogara da kanta ta fuskanr kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da cigaban al’ummar yankin, jawabin haka ya fito daga bakin tsohon sakataren Hukumar bada tallafin karatu na Jihar Kano, kuma wanda ke yiw ajam’iyyar APC takarar shugabancin karamar hukumar Trauni Alhaji Abubakar Zakari lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Honarabul Abubakar Zakari ya ce na wakilci na karamar Hukumar Tarauni a majalisar dokokin Jihar Kano a baya, don haka na san karfin karamar Hukumar ta fuksar tattalin arziki, sannan na sa irirn albarkatun da Allah ya horewa wannan karamar Hukumar, musamman ganin karamar hukuma ce dake kwaryar birni, akwai abubuwa da yawa da ake gudanarwa wanda idan aka kula dasu kwarai, za’a samu kudaden masu kauri da za’a iya ci gaba da harkokin mulkin wannan karamar Hukumar ba tare da an zubawa kason Gwamnatin tarayya ido ba. Wannan tasa zamu zauna da masu kishin cigaban wannan yanki domin fito da ngartattun hanyoyin samar da kudaden shiga wanda za’a ci gaba da yiwa al’umma luguden ayyukan alhairi.
Da yake tsokaci kan batun hadin kan jama’ar Tarauni, Abubakar Zakari cewa ya yi ina tabbatar maka da cewa Karamar Hukumar Tarauni na ickin yankunan da Allah ya yiwa albarkar zaman lafiya, sannan kuma muna da dattajai na gaske masu kishin wannan karamar Hukuma, wannan tasa ba’a jin yawan yamutsa gashin baki a tsakanin jagororin wannan karamar Hukuma. Yace yanzu haka da ake kokarin gudanar da zaben kananan Hukumomi, mu a karamar Hukumar Tarauni alhamdulillahi kanmu a hade yake, jiran lokaci kawai muke ayi jana’izar Jam’iyyar PDP, Kasacewar kwananta ya kare a siyasance.
Akarshe Alhaji ABubakar Zakari ya jinjinawa al’ummar Karamar Hukumar Tarauni bisa kyatata masa zato d suka yi, wanda kuma yake kara tabbatar masu da cewa da yardar Allah ba zai basu kunya ba, zamu tabbatar da yin aiki tare idan Allah ya bamu wnanan dama muka lashe zaben dake gabatoa. Injin Abubakar Zakari.
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano