Khalid Idris Doya" />

Babban Burina Shi Ne Ganin Sojoji Cikin Walwala, In Ji Buratai

Babban shugaban sojin Nijeriya, Liyutanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya shaida cewar tabbatar da kyautata jin daxi da walwalar sojojin qasar nan shine babban abu muhimmi da shugabancinsa ta sanya a gaba.
Babban shugaban sojin Nijeriya, ya shaida hakan ne a jiya a Bauchi a lokacin da ke qaddamar da fara amfani da wasu sabbin gine-ginen wuraren kwana na sojoji da aka gina da kuma wasu gidajen kwanan sojoji masu muqamin Sajan Manjo (Warrant Officers) da kuma masu muqamin Sajan da aka gina wa sojoji a shalkwatan Rundunar sojin Nijeriya ta 33 da ke Barikin Shadawanka a cikin garin Bauchi.
Janar Tukur Buratai ya na mai qarawa da cewa wasu tulin aikace-aikace da gine-gine yanzu haka suna ci gaba da gudanuwa a sauran sassan Barikokin da suke faxin qasar nan domin tabbatar da sojoji masu matsakaitan muqamai sun samu wuraren kwana da suka dace domin qara musu himma da azama a bakin aikinsu.
Ya na mai shaida cewar samar da irin waxannan gidajen zamanin suna qara kyautata Barikoki a kowani lokaci, a bisa haka ne ya jawo hankulan waxanda suka amfana da gidajen da cewar su tabbatar da sun kula sosai da wuraren da aka basun bisa la’akari da dumbin kuxaxen da aka kashe wajen gina wuraren kwanan garesu.
Tukur Buratai ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga manyan jami’an soji da qananan sojojin qasar nan da su ci gaba da biyayya da bayar da haxin kai ga Rundunar soji da tabbatar da kyautata aqala a tsakanin rundunar soji da sauran vangarorin tsaro domin tabbatar da kai harqar tsaro matakin da ya dace a Nijeriya.

Shugaban Sojin qasar nan ya nanata cewar tabbatar da jin daxi da walwalar sojojinsu shine a gaban shugabancinsa, yana qara wa da shaida musu cewar zai ci gaba da tabbatar da hakan.
Da ya ke tasa jawabin a wajen bikin, Kwamandan Rundunar Armoured Corps da ke Bauchi, Manjo Janar James Olubumi Akomoleke ya shaida cewar samar da irin wannan gine-gine masu gayar alfanu, sun biyo yunqurin shugaban sojin Nijeriya na tabbatar da kyautata walwala da jin daxin sojoji ta hanyoyin da suka dace musamman kyautata Barikokin soji.
Shi kuma kwamandan shalkwatan sojin Nijeriya ta 33 da ke Bauchi, Birgediya Janar M T Durowaiye ya nuna cewar wannan bikin da qaddamar da gine-ginen suna daga cikin shirin shugaban soji Tukur Buratai na tabbatar da kai aikin soja zuwa matakin kwarewa domin kyautata aiki da baiwa sojoji damar gudanar da aiyukan da suke rataye a wuyayensu.
Brigadier General Durowaiye ya ce yanzu haka wasu aiyukan da suke kan gudanarwa domin faxaxa aikace-aikacen wasu gine-gine na ci gaba da gudanuwa domin tabbatar da cimma manufar da aka sanya a gaba na kyautata wa sojoji aikinsu da jin daxinsu.
Ya jinjina wa qoqarin shugaban nasu a bisa samar da shirye-shiryen da yake yi na kai aikin soji zuwa matakin da suka dace.

Shugaban Sojin kasar nan ya nanata cewar tabbatar da jin dadi da walwalar sojojinsu shine a gaban shugabancinsa, yana kara wa da shaida musu cewar zai ci gaba da tabbatar da hakan.
Da ya ke tasa jawabin a wajen bikin, Kwamandan Rundunar Armoured Corps da ke Bauchi, Manjo Janar James Olubumi Akomoleke ya shaida cewar samar da irin wannan gine-gine masu gayar alfanu, sun biyo yunkurin shugaban sojin Nijeriya na tabbatar da kyautata walwala da jin dadin sojoji ta hanyoyin da suka dace musamman kyautata Barikokin soji.
Shi kuma kwamandan shalkwatan sojin Nijeriya ta 33 da ke Bauchi, Birgediya Janar M T Durowaiye ya nuna cewar wannan bikin da kaddamar da gine-ginen suna daga cikin shirin shugaban soji Tukur Buratai na tabbatar da kai aikin soja zuwa matakin kwarewa domin kyautata aiki da baiwa sojoji damar gudanar da aiyukan da suke rataye a wuyayensu.
Brigadier General Durowaiye ya ce yanzu haka wasu aiyukan da suke kan gudanarwa domin fadada aikace-aikacen wasu gine-gine na ci gaba da gudanuwa domin tabbatar da cimma manufar da aka sanya a gaba na kyautata wa sojoji aikinsu da jin dadinsu.
Ya jinjina wa kokarin shugaban nasu a bisa samar da shirye-shiryen da yake yi na kai aikin soji zuwa matakin da suka dace.

Exit mobile version