A bisa lalacewar tarbiyyan ‘ya’ya mata da kuma gurɓacewar rashin karatunsu hakan yana matuƙar jawo wa ƙasar nan ci baya ta fuskoki daban-daban a bisa haka ne ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a kan yi iya ƙoƙarinsu wajen shawo kan matsalar da sha’anin ilimi ke fuskaganta. La’akari da cewar gwamnatoci a kashin gansu ba za su iya shawo kan matsalar da harƙar ilimi ke fuskanta baki ɗaya ba, dole sai suna samun taimaka daga wasu.
A bisa haka ne wata budurwa mai suna Alheri Yusuf ta tashi tsaye domin ganin yanda matsalar ke neman zama ruwan dare ta ce za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen tallafa wa ‘yan uwanta yara da kuma mata ta fuskacin inganta sha’anin iliminsu, inda ta kafa wata cibiya mai suna ‘ALHERI YS FOUNDATION’ domin taimaka ta fuskacin ƙarfafan yara da mata ta fuskacin ilimi.
Wakilin Leadership A Yau, ya nemi ƙarin bayani kan manufar budurwar inda ta bayyana manufarta na kafa wanan cibiyar da kuma aikace-aikacen da take gudunarwa, inda kuma shaida cewar ta kafa wannan cibiyar ne tun a farko-farkon shekara ta 2016 inda ta samu nasarar gudanar da abubuwa da daman gaske.
A ta bakinta “Da ya ke akan samu matsala yanzu ka ga yara ba sa zuwa makaranta idan ka bincika sai ka samu dalilin ba wata dalili ba ce da zai hana yaro zuwa neman ilmi illa dai rashin kuɗi ko wani tallafi da makamantansu. A bisa haka ne na kafa wannan ƙungiyar domin taimaka wa yara ta fusakacin iliminsu da kuma ba su ƙarin guiwar neman ilimi”. Ta bayyana
“Yanzu idan ka lura masu karatun bokon nan da shi ne duniya take tafiya, to mu kuma ‘ya’yan talakawa an barmu a baya, ta yaya za mu yi sai mu dage mu sanya a zuciyarmu za mu nemi ilimi duk wahalarsa”. A bayyana
Cibiyar na ta na ‘Alheri YS Foundation’ wacce take aiki tare da ƙungiyar ‘Nigerian Women Association of Georgia’ inda ta bayyana cewar tana samun tallafi da haɗin guiwa ne daga wannan ƙungiyar matan inda ta ce ta samu nasarar gudanar da aiyuka da daman gaske.
Ta ci gaba da cewa “ka san babbar matsalar da ke damun sha’anin ilimi shi ne talauci musamman ga mu ‘ya’yan talakawa. Yanzu idan za ka shiga cikin makarantun firamare za ka tarar yaro ya ɗauki littafi guda ɗaya yana ɗaukan darasi kusan biyu wani ma fiye a cikin littafi guda, wanda hakan na jawo ya yara su gagara fahimtar abubuwa da dama, ko kuma ka samu yaro ya ɗauki ilimin zane ya je ya sa a cikin ilimin lissafi ba komai ya jawo hakan ba illa yana rubuta dari biyun a cikin littafi ɗaya”.
Ta ci gaba da cewa “A bisa haka ne ni da wannan ƙungiyar tawa muka tashi haiƙan wajen rage yawaitar wannan matsalar, a bisa haka ne na kaddamar da wani kamfen mai suna ‘ONE SUBJEC-ONE BOOK’ ma’ana dai kowace darasi da littafinta, kuma dukkanin makarantun da na je na kan yi ƙoƙarin baiwa yara tallafin littafi da kuma wayar musu da kai nan illar haɗa darasi a waje guda”. Ta bayyana
A kan wannan gaɓar ne kuma sai Alheri Yusuf ta yi ƙira ga iyaye da su daure suke saya wa ‘ya’yansu littafan da suka dace domin baiwa ‘ya’yan nasu zarafin gane karatu cikin sauƙi kuma cikin hanzari a cewarta samar ya ɗalibai abubuwan karatun da suka kamata na matuƙar taimaka wa wajen ƙara ma yaro kwarin guiwa kan neman ilimi “Yaro yana son a ba shi kayyakin karatu waɗanda za su jawo hakalinsa wajen karatun nan, yanzu misali wani ya samar wa ɗansa littafin ABC zuwa Z mai inganci ko kuma mai jan hankali, a kowani lokaci zai ke kasancewa da wannan littafin daga haka har ya haddace abun da ke nema cikin sauƙi, a don haka ina ƙira ga iyaye a daure duk da na san halin da ake ciki, amma ilimin yaranmu suna da muhimmanci a gare”. In ji Alheri
Ta fuskacin yanayin taimakon da take baywa sha’anin ilimin yara kuwa, ta shaida cewar takan duba yanayin ƙarfi iyaye ne ko kuma sakacinsu “wata rana ina tafiya sai na ga wata yarinya tana ta zabga kuka, na tsaya na tambayeta wai an korota daga makaranta alhali ‘yan uwanta sun tafi makarantar, na tambayeta nawa ne kuɗin nan sai ta faɗa min wani luɗi ne ƙalilan amma a sakamakonsa ta rasa yanda za ta yi, iyayenta ba su da shi ne ko irin ‘ya’yen nan ne waɗanda ba su damu da ilimin ‘ya’yansu ba, nan take na ce mu je gidansu yanzu haka ina ci gaba da kula da karatun wannan yarinyar domin ta samu ilimi yanda ya kamata. Sannan kuma na kan shiga unguwa na duba yaran da basu zuwa makaranta na taimaka musu”. In ji ta
Alheri Yusuf ta kuma bayyana cewar tallafin nata bai tsaya haka ba, domin kuwa takan sayi kayyakin karatu da suka haɗa da littafai da sauransu inda take rabawa ga ɗalibai ‘yara domin inganta musu koyo da koyarwa.
Da take magana kan haɗin guiwar da ke tsakaninsu da ƙungiyar ‘Nigerian Women Association of Georgia’ ta ce wannan ƙungiyar na ƙoƙarin tallafa wa mata kan ilimi, inda suke baiwa ɗalibai tallafin karatu da kuma sauran abubuwan da suka dace “nan ba da jima wa ba wannan ƙungiyar za ta sake baiwa ma wasu ɗalibai tallafin karatu a jihar Bauchi, tallafin zai taimakesu sosai ta fuskacin ilimin nasu”. A cewar Alheri Yusuf
Daga bisani shugaban cibiyar Alheri YS ta kirayi jama’a da su haɗa kai da cibiyoyin taimaka wa jama’a domin inganta rayuwar al’ummansu.