Babban Burina Shi Ne Samar Da Nagartaccen Shugabanci- Shugaban ICPC

Farfesa Bolaji Owasanoye, Ciyaman na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a yau Alhamis ya bayyana cewa burinsa shi ne samar da nagartaccen shugabanci da sauyi mai amfani a hukumar.

Shugaban ICPC din ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a birnin tarayya Abuja. Ya ce samar da nagartaccen shugabanci yana daga cikin manyan manufar da zai ba da damar cimma burin kafa hukumar.

Owasanoye ya fara aiki ne a cikin watan Fabaraitun 2019 a matsayin shugaban hukumar na hudu tun bayan kafa hukumar a cikin shekarar 2000. Ya tabbatar da cewa burin sabuwar shugabancin hukumar shi ne samar da ingantaccen tsarin shugabancin da zai kawo sauyi a bangaren gudanar da ayyukan hukumar.

Sannan ya yi alkawarin ganin an rage tasirin cin hanci da rashawa a kasarnan.

 

Exit mobile version