Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home TATTAUNAWA

Babban Burinmu Shine Magance Yaduwar Cututtuka A Jihar Nasarawa – Shugaban Kungiyar Likitoci

by Muhammad
February 18, 2021
in TATTAUNAWA
5 min read
Cututtuka
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

uttukaShugaban Tsangayar Likitocin Asibitin Dalhatu Araf dake garin Lafia, babban birnin jihar Jihar Nasarawa, DAKTA IKIRAMA HASAN, ya bayyana yadda suke kokarin magance matsalolin cututtuka masu yaduwa cikin al’umma a jihar. Da yake zantawa da Wakilin LEADERSHIP A YAU, ZUBAIRU M. LAWAL, dangane da cece-kucen da ake ta yadawa dangane da matsalolin dake faruwa cikin asibitin da batun cututtuka da batun zuwa yajin aikin da likitoci ko kokarin yi. Dakta Ikirama Hasan ya warware komai dangane da zargin da ake yi, kamar haka:

 

Me za ka ce game da maganganun da ake yi cewa, akwai likitocin da suke kamuwa da cututtuka a asibitin Dalhatu Araf?

Duk da abubuwan da suka faru masu ban al’ajabi da jita jita da yake yawo cikin mutane, ya zama wajibi muyi bayani, ga masu yada labarai har zuwa kunnuwar al’umman jihar Nasarawa.

A watan nuwamban shekaran 2020 da ya wuce, Ma’aikatan lafiya ta nan jahar Nasarawa ta sanar da sake bullar wannan cuta da kafi sani da korona bairos (Covid-19) wanda yake da saurin yaduwa. Matakin farko da muka dauka shine yadda zamu kare Ma’aikata na musamman da aka gayyato su wadanda aka fi sanin su da ( RRT) da (IPCC) wadanda suke kokari wajen dakile yaduwar cututtuka. Asibitinmu ya yi namijin kokari wajen fitar da kudi domin gudanar da ayyukan kariya ga Ma’aikatan jinya dake aiki a nan kamar:

  1. Horar da ma’aikata: Daukacin ma’aikatan an basu horo na musamman akan cutar Korona a zango na farko. Shine aka sake horar dasu a watan Nuwamba da kuma watan Disamba na shekarar 2020. akan cutar Zazzabin Lassa da kuma Shawara da yadda za’a shawo kansu gani da ansamu bulluwar cutar a fadin kasa baki daya.
  2. Wayar da kan al’umma: Sashin dake hulda da mutane na asibitin ya gama shiri kuma ya fitar da bayanansa.
  3. Kayayyakin kariya na musamman: An ware kudi kan asiyo kayayyakin da ya kamata da kuma inda ya dace abasu.
  4. Takunkumin fuska: Asibitin ta bada takunkumin kariya na fuska na watanni da dama. bugu da kari akwai suturan kariya na marasa lafiya da kuma masu tayasu jinya. An gargadi ma’aikatan asibitin kan lallai su tabbatar cewa masu cutar korona da masu tayasu jinya sun sanya kayan kariya da kuma takunkumi.
  5. Kwamiti masu wayar da kai akan hanyoyin da za’abi ganin an kaucewa kamuwa da cutar korona. An riga an nada kwamitin kuma an basu horo dan ganin anbi doka da oda.
  6. Daidaito a cunkoson jama’a, an gayyaci mutane da dama a fannin tsaro don ganin an karfafasu da tabbatar sun sanya mutane sunbi doka ba tare da sun kawo cunkoso ba a asibitin.
  7. (RRT) ta fidda tsari da shiri musamman ga ma’aikatan kiwon lafiya na korona Bairus na gwaji da kuma kulawa dasu. Duk ma’aikacin da aka tabbatar ya kamu da cutar korona Bairus akwai kulawa da za’a bashi na musamman na komai da komai.

Sashen kula da marasa lafiyan korona sun fidda adadin malaman kiwon lafiya da zasuyi aikin kulawa da masu cutar korona Bairus. Kungiyoyi dabam dabam na ma’aikatan Asibitin Dalhatu Araf sun hada kai domin gudanar da ayyukan kiwon lafiya tare da kowa domin dakile yaduwar cututtuka dake barazana ga lafiyan al’umman Jihar Nasarawa.

 

To, Ina zargin cewa wasu kungiyoyin na ganin a dakatar da duk ayyukanjinya a Asibitin?

Wannan shawarar da kungiyar ARD ta bayar na ganin an dakatar da aikace aikace bai samu kar buwa ba. Batutuwan an riga da an mikasu ga cibiyar bincike na asibin tare da hadin gwiwa na kungiyar RRT da IPCC. Sai dai bayan kwanaki kadan da gudanar da taro, kungiyar ARD ta umurci mutanenta dasu dakatar da aiki har sai an kira taro na gaggawa kuma a dakatar da kowani aikace-aikace. Wannan ya biyo bayan umurni da kungiyan Malaman kiwon lafiya na Hakori na Najeriya sukayi (MDCAN) wanda suka umurci mutanenta da su cigaba da aiki amma kuma su kauracewa inda ake basu horo. A lokaci guda an samu rarrabuwa bayan da wasu ke cewa a dakatar da aiki wasu kungiyoyin suna cewa mutanensu su cigaba da aiki kamar yadda aka saba. Wannan shine lokaci mai wahala da asibitin ta samu kanta ganin yadda cutar keta yaduwa a cikin al’umma.

 

An ce wasu likitocin sun bukaci a kulle Asibitin Dalhatu Araf saboda cutarna kokarin fin karfinsu?

Haka ne Shugabannin asibitin sunyi yunkuri na ganin an kara karfin ma’aikata a kowani sashi suka mika kokon baransu da cewa duk wani likita na garin yazo ayi aiki tare dashi don ganin an samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jahar Nasarawa. Alhamdulillah duk da muna yaki da yaduwar cutar a cikin al’umma. Mun yaba da kokarin ma’aikatanmu. Muna so daukacin mutane susan da cewa kula da marasa lafiya a sibitimmu shine babban burimmu. Mara lafiya su ne jigo na kowani asibiti. Saboda wannan dalilanne yasa mukaki amincewa mu kulle asibitimmu kamar yadda wasu daga cikin Shugabannin suka bukata ayi saboda wasu dalilai. Bugu da kari, dabarummu na kin haka shine da farko cutar korona na yaduwa kuma shawarar da aka bayar na kulle asibitoci ba shine mafita ba face ya kara yaduwar cutar ta yadda za a rika samun labaran mutuwa mara adadi. Abun takaici ne ace wani bangare na kungiyoyi kamar ARD suce wai mutanensu su kauracewa wajen bada horo saboda bukatu nasu kashin kansu. Bayan ansan wannan kungiya tanada nata mutanen yan sa kai. Wannan kungiya abun data sa gaba shine cimma yarjejeniya na hadin gamayyar kungiyoyi ba tare da ankawo nakasu ba. Idan ana so a cimma nasara, dole sai an yaki mutane masu kawo rudani. Masu kawo matsala a cikin wannan kungiya koda sune masu ba da horo. Sun sanya kansu a matsayin masu fada aji kuma suke amfani da wannan dama suna haifar da damuwa domin cimma bukatunsu na kansu.

Ba wani abu mara kyau wanda mukeyi Kowa yasan munada tsari a cikin asibitinmu. Idan kuma akwai wani damuwane ko kuma matsala sai a tunkaremu dashi amma ba wai a dinga yawo dashi ba har sai ya shigo kunnenmu. Wasu Shugabannin na asibiti sunyi iya bakin kokarin su na suga sun sasanta kuma an cigaba da kawance tare da , wadannan kungiyoyi saboda samun zaman lafiya a yi aiki tare a cikin asibit. Sai dai ba su amince ba da cigaba da kawancen namu. Saboda sunaga sulhu zai kawo musu cikas a kungiyansu saboda abun da suke so ba zai yuhu ba. Masu bada horo da kuma shugabanni sunyi iya kokarin tafiyar da kungiyan bai daya cikin zaman lafiya sai akace ai basu iya ba aka barsu basu da mataimaka. Kamar yadda shugaban ARD yasani masu bada horo da kuma shugabannin akan gudanar da bada horo sunki sauka a mukaminsu sun zauna batare da sun ba wasu dama su gwada fasaharsu ba. Wannan shima ai rashin adalcine wajen gudanar da aikin kungiya. Mun gano manufofinsu shine su hura wuta a cikin Ma’aikatan mu ta yadda zasuyi bare har ta kai ga rufe Asibitin koda al’umman Jihar zasu galabaita. Akwai dayawa cikin hadakan kungiyoyi a DASH. Duk malaman kiwon lafiya an san sunada kungiyoyinsu. Kowani hadakan kungiya tanada shugaba da kuma tsarin jin dadin ma’aikatanta. Daga cikin doktocin da muke dasu akwai kungiya guda uku kamar ARD, MDCAN da NMA. Kowanne cikin wadannan Kungiyar harda na masu goge goge zasu iya kawo ma asibitin cigaba. Rashin su kadai sun isa susa a rufe sashin kula da masu jinyar korona amma basuyi hakaba sun mika wuya domin a tafi tare. Dangantaka dake tsakanin masu bada horo da shugabannin a wani gefe yayi tsami. Ya zama dole a dauki matakai da kuma sulhu dan dakile wannan matsala dayake kasa wanda ya haifar da rashin zaman lafiya da aikace-aikace a asibitimmu.

 

Daga karshe wani kira ka je da shi ga Likitoci?

Ina kira ga likitocin wannan gari dasu bar zaman ta zauna da gindinta sannan su ajiye kudirorinsu sannan suyi bayani ga daukacin mutane cewa asibiti zata cigaba da kasancewa a bude saboda ta cigaba da aikace-aikacenta saboda al’ummar jahar Nasarawa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Tsaro Na Katsina Ya Karrama Malamai Da Limaman Jihar

Next Post

Jihar Gombe Ta Kaddamar Da Tsarin Cigaba Na Tsawon Shekaru 10

RelatedPosts

NIRSAL

Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Mazauna Abuja, Ya Yabawa Manajan Daraktan NIRSAL

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Mataimakin shugaban yan kasuwar na Arewacin Nijeriya, wato ‘Arewa Traders...

Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya

Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Hon. Garba Datti Babawo na daya daga cikin ‘yan majalisar...

Bambancin Hon Sama’ila Yakawada Da Sauran ‘Yan Siyasar Kaduna – Mai Martaba Giwa

Bambancin Hon Sama’ila Yakawada Da Sauran ‘Yan Siyasar Kaduna – Mai Martaba Giwa

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

A cikin makon da ya gabata ne wakilinmu IDRIS UMAR...

Next Post
Jihar Gombe

Jihar Gombe Ta Kaddamar Da Tsarin Cigaba Na Tsawon Shekaru 10

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version