Abaya Ojukwu ya taba jagorantar yakin assasa kasar Biyafara, amma a karshe ba a cimma komai ba, face zubar da jini, asarar rayuka da dukiya da kuma jefa kasa cikin yunwa da fatara gami da mawuyacin hali. Babban abin takaici a wannan lokacin shi ne Ojukwu da iyalin gidansa babu wanda a ka yi wa rauni; gabadaya ya tattara su ya tsallake zuwa wata kasar su ka ba shi mafakar siyasa.
Wannan yaki ne ya janyowa kabilar Igbo bakin fentin da har gobe ya na bibiyar su a kasar, ya kuma kassara matasansu ga shiga ayyukan ta’adaddanci iri daban-daban, wanda har gobe an yi mu su tazara a sha’anin mulki da fannin ilimi da dama a Najeriya, su kuma su ka yiwa sauran manyan kabilun kasar tazara da fice a fannin aikata miyagun lafuka.
Daga bisani Ojukwu ya dawo gida Najeriya sun ci abinci a teburi daya da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon, wanda a baya shi ya yake shi. Ma’ana; a ka yafe ma sa bayan ya nemi afuwa gami da biyan sa kudadensa na ritaya, sannan ya samu ’yancin watayawa da walwala har ta kai ga ya nemi takarar shugabancin kasa.
Maimakon wannan ya zama wani babban darasi ga Igbo da sarakunansu zuwa shugabannin siyasa da dattawansu, sai su ka zama kurame, bebaye kuma makafi ga wata sabuwar guguwa makamanciyar wacce ta faru a baya.
A wata tattaunawar faifan bidiyo, Ojukwu ya bayar da amsa ga wadannan matasa masu tashen balaga cewa, “su na ta cewa, kai ne ka jagoranci na farko, me zai hana yanzu ma ka sake jagorantar mu? Sai na ce shakka babu, cikin alfahari na jagoranci na farko, amma ba na tsammanin akwai bukatar kara maimaici.”
Kamata ya yi dattawan Igbo da sarakunansu zuwa jagororin siyasa da mahukuntansu su dauki wannan magana ta Ojukwu da matukar muhimmanci. Amma sai su ka yi kunnen uwar-shegu kowa ya ja bakinsa ya tsuke.
Nnamdi Kanu da ba a Nijeriya ya rayu ba, ya na da fasfo da yawa, ya na da izinin zama a wata kasa bayan wannan, ya zama Dujal mai ’yar ganga ga ’ya’yansu. Ya rika kada mu su gangar yaki su na yi ma sa sujada cikin ladabi da biyayya.
Da gwamnati ta kama shi lauyoyinsu su ka rika zuwa kotu su na kare shi a matsayin maras laifi. Jagorinsu su ka rika shiga su na fita, sai da a ka nemi alframa a ka bayar da belin sa. Sannan da ya fito a ka rika turuwar zuwa a na hoto da shi a matsayin wani gwarzo.
Wasu ma da su ka zurfafa soyayyarsa su ka kai shi matsayin abin bauta. Su ka rika ihun a ba su kasar Biyafara ko su kona Najeriya. Su ka rika ikirarin sun tara makaman yakar kasar. Su ka rika dandazo su na tafiya yankinsu su na tarewa domin shirin yaki, wanmfda ba su san shi ba.
Yau sun tsokano jami’an tsaron Najeriya, an bi su za a hukunta su, hankalin kowa ya tashi, manya da sarakunansu zuwa ’yan siyasa kowa ya na rokon kada a shafe su daga doron kasa, wanda a baya su na ji su na gani su ka yi biris.
Su kuma matasan da Nnamdi Kanu yak e zugawa, ya kamata su lura da cewa, ire-iren wadannan mutane da ke tunzura matasa su dauki makami, su na yi ne ko dai a matsayin ’yan kwangila ko kuma masu neman su yi amfani da su su zama masu fada a ji a kasar ko kuma a cikin al’ummarsu.
Abin lura a nan shi ne, shin iyalin Ojukwu sun kasa samun ilimi ko kulawa da kyakkyawar lafiya duk da cewa ya jagoranci yadi? Amsar it ace a’a. To, haka ma iyalin Nnamdi Kanu ba za su fuskanci wannan matsala ba a yanzu ko nan gaba. Iyalin mabiyansu ne kadai za su fuskanci hakan.
Wannan darasin ba wai a ka Ibo kadai ya ke ba, hatta a Arewa ma yakamata matasa su hankalta da masu saka su su aikata wani mummunan abu, don biyan wata bukata ta kashin kai. Duka yaudara ce!
Da fatan wannan zai zama kuskure na karshe da za su ga wani dan kabilar Ibo zai yi makamancin wannan su taka ma sa birki.