Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya Ya Nemi Hadin Gwiwa Da NIS Kan Bayanan Sirri

“NIS Za Ta Iya Biyan Bukatar Nijeriya A Sashen Bayanan Sirri”

Wakilin Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede, DCG Isah Idris Jere (na biyu a hagu), Janar Leo Irabor (na biyu a dama), ACG Muhammed Aminu (na farko a hagu) da ACG Modupe Anyaelechi (ta farko a dama) yayin ziyarar

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya, Janar Leo Irabor ya nemi hadin gwiwa da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta fuskar bayanan sirri domin inganta tsaron kasa.

Babban hafsan ya yi kiran ne a lokacin da ya ziyarci shalkwatar hukumar ta NIS a ranar Laraba inda aka zagaya da shi katafariyar cibiyar fasahar sadarwar zamani ta hukumar.

Bayan ya gane wa idonsa irin kayan aiki na zamani a kan tattara bayanai da tantance su da sanya ido da aka samar a cibiyar ta fasaha, Irabor ya yi kiran samun hadin gwiwa tsakanin NIS da rundunonin soji da sauran jami’an tsaro domin cin gajiyar bayanan sirrin da NIS take samarwa da suke da matukar alfanu ga ayyukan tsaro na sojoji da sauran jami’an tsaro.

Babban hafsan ya yaba wa shugaban hukumar ta NIS CGI Muhammad Babandede bisa kyakkyawan shugabancinsa kana ya yi alkawarin bai wa hukumar goyon bayan da ya kamata domin kara samun ci gaba

Da yake mayar da jawabi, Babban Mataimakin Kwanturola Janar na NIS, DCG Isah Idris Jere wanda ya tarbi babban hafsan sojin a madadin shugaban NIS, ya gode masa bisa ziyarar da ya kawo, kana ya yi alkawarin cewa NIS a shirye take wajen musanyar bayanan sirri da rundunonin soji da sauran jami’an tsaro.

Jere ya bayyana cewa cibiyar wacce ta kasance mafi muhimmanci cikin dimbin ayyukan ci gaba da NIS ta yi, tana da rantsattsun kayan aiki da za ta iya biyan bukatar kasar nan ta fuskar tattara bayanan sirri saboda kayan aikin da ta girke a sassan ayyukanta da suka hada da filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa, iyakokin kasa na kan-tudu, ofisoshin fasfo, sashen ‘yan sandan duniya da kuma ofisoshin jakadancin Nijeriya a kasashen ketare inda jami’anta suke aiki daban-daban.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James ta nunar da cewa ziyarar ta yi armashi sosai.

 

 

Exit mobile version