Babban Jami’In WHO Ya Yaba Da Samar Da Rigakafin Sinopharm Ga Kasashe Masu Karamin Karfi

Daga CRI Hausa

Bruce Alyward, babban masanin hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bayyana a ranar 7 ga wata cewa, kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin ya samar da gagarumin tallafi wajen samar da rigakafin yaki da annobar COVID-19 ga duniya, musamman saboda yadda yake samar da rigakafin ga kasashe masu karamin karfi.

Ya ce abin farin ciki ne yadda hukumar WHO ta tattauna da kamfanin na Sinopharm game da yadda za a kara samar da rigakafin, musamman duba da yadda matakin ke taimakawa yaki da annobar a duniya.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version