Sabo Ahmad" />

Babban Kalubalen Da ke Gaban Sabuwar Majalisar Tarayya

‘Yan Nijeriya suna da kyakkyawar fata sosai kan majalisar tarayya ta tara da za a asassa nan gaba kadan, inda jama’an suke kallon haka da kyawawan dalilai.
Majalisar da ke shirin ficewa, kamar wacce ta gabata gabanin wannan majalisar, ya dan fi wanda ya gabaceshi kima. Matsalar ita ce, wadannan ‘yan majalisun na daukan iko a bisa mutanen da suka basu zarafin zuwa ga wannan matsayin. Sun yarda da girman darajarsu, sun kuma kasance masu sani kan dokokin da zasu tattake masu lalata lamura da al’ada, sannan a gefe guda kuma basu yi wasa da darajarsu ba.
Al’umma sun kasu kashi biyu a lokacin da mambobin majalisar kasa suka fara kauce wa aiyukan da ke gabansu suna karkatar da kawukansu zuwa ga wasu ababen na kashin kai a maimakon tsayuwa bisa turbar ayyukan da suka dace su yin a samar wa jama’a dokokin da za su ciyar da kasa gaba.
A bisa yadda suka dauki halayensu, sun fara tunanin yanda sauran al’umma ke gudanar da nasu harkokin rayuwar. Su mambobin sun kasance a cikin rayuwa mai gayar kyau sun kuma yi nisa da rayuwar da suka samu kansu a ciki baya wanda shi ne rayuwar da ke daidai da su, irin wadannan sauya rayuwar ta lokaci guda, yana daga cikin abu mafi munin da ke damun al’ummar Nijeriya da suka tura mamba zuwa majalisa domin ya gudanar da aikin ci gaban jama’a sai ya bage da gina kansa, wanda hakan na matukar damun ‘yan kasa.
Makuden kudaden da mambobin majalisa ke biyan kansu a matsayin albashi da alawus ya zama abun mamaki da kunya a lokacin da wani daga cikin ‘yan majalisun ya fallasa tayar irin tulin kudaden da suke biyan kansu da kansu.
Akwai muhawarar da take nuni kan cewar shin a ci gaba da samar da ‘yan majalisu masu cikakken lokaci ko kuma a samar da dan majalisa mai kayadadden lokaci domin samun rage rarar maguden kudaden da ake kashewa da sunan biyan albashin ‘yan majalisu. Wannan muhawar ya gamu da jayayya wanda ya tarar daga jagororin yanzu. Musamman ma, jama’a sun gaza gane dalilan da ake nunawa, musamman a ckin mambobin jam’iyyar da ke mulki.
Lokaci aka ware domin domin asassa dokoki domin tabbatar da kyakkyawar shugabanci a fadin kasa da kuma samar da sauye-sauye masu ma’ana. Muradi da bukatun jama’a su ne hanyoyin bi domin kyakkyawar gwamnati.
A bisa wannan hangen nesar ne ya sanya wannan jaridar ta ga ya dace ta tunatar da majalisar da ke tafe, idan ba su sani ba, ‘yan Nijeriya sun sha wahala sosai sun kuma kai makurar shan wahalar a bangaren siyasa.
‘Yan Nijeriya suna tsananin bukatar majalisar da ke tafe, bayan an rantsar da ita, ya zama an yi gaggawar duba da yanayin da ake ciki domin yin dokokin da za su shiga rayuwar hadi da inganta rayuwar al’umma kai tsaye.
Muna bukatar wannan majalisar kasa ta tara din ta zama madubi mai ban mamaki wajen kyautata shugabanci da samar da dokoki masu ma’ana hadi da gudanar da majalisar cikin gaskiya. Al’umma suna da hakki su san nawa ne kowani dan majalisa ke samu a lokacin da ke ofis. Tsarin kasafin kudin majalisar dokoki ta kasa, kamar sauran shika-shikan gwamnati, ya dace ya zama dukkanin hada-hadar kudi ya zamana a fayyace ake yinsu.
Bayanai akan kudaden da kowane dan majalisa daga cikin ‘yan majalisun ke samu ya zama tilas ake sanin adadin kudin a kowani lokaci.
Dole ne kuma majalisa take fitar da kudaden gudanar da aiyuka ga ‘yan majalisu a mazabunsu ta hanyoyin da suka dace. Ya zama ana daura kudaden gudanar da ayyuka a mazabu bisa hanyoyin da suka dace kuma sahihai wadanda hankali za su kama a kowani bigire.
Yawancin ‘yan majalisu sukan kauce wa aiyukan da jama’a suka turasu majalisa gudanarwa na tsara dokoki da fitar da dokokin da za su ciyar da kasa gaba dukkanin wasu aiyukan da za su kawo tarnaki wa tsara dokokin da za su ciyar da kasa gaba tilas ne a daina ci gaban da yinsu.
Ma fi yawan mutane suna ji suna kuma ganin aiyukan da ya kamata majalisa ta aiwatar, amma sai aiyukan su juyu zuwa ga mugunta mafi muni ga al’umma. Don haka ba mu fatan wannan majalisar ta biye wa irin wannan halayen, muna fatan wannan majalisar za ta tsaya ta yi gyara sosai musamman kan yadda ‘yan majalisu suke mancewa daga ina suka fito.
‘Yan Nijeriya, a ra’ayinmu sun sanya tsammanin cewar majalisar da za su zo yanzu wato ‘yan majalisu ta tara za su kauda kai da biye wa son ransu na kashin kansu za su rumgumi aiyukan da ke gabansu ka’in da na’in domin ci gaban kasa da muradin kasa.
Ana zargin ‘yan majalisun da zasu fita a ‘yan watanni masu zuwa da gaza saurin amincewa da aiyukan gwamnati da kawo jinkiri wajen gudanar da kyawawan aiyukan da za su ciyar da aikin gwamnati gaba. Wanda ma ana zarginsu da shigar da siyasa a cikin harkokin aiki. Don haka muna tunatar da ‘yan majalisu masu zuwa kada su maimaita wannan kuskuren.
Ma fi yawanci duk da ba lallai ya zama dukka gaskiya ba, yana dai da kyau a tabbatar da majalisar sun gudanar da nagartattun aiyukan da zai sanya su zama jagororin al’umma na kwarai.
A tunanin wannan jaridar, muna da tabbacin ‘yan majalisu sun san tsarinsu a cikin demoradiyya. Muna kuma da yakinin cewar za su bi ka’idoji da dokoki kamar yadda wadanda suka zabesu suke da tsammanin hakan daga garesu.
Wadanan tsammanin da jama’an kasa ke yi, ba zai wani dauki lokaci ba idan dai ‘yan majalisun za su fara yin nazari da kuma tabbatar da sun bi ka’idoji da matakan da suka dace wajen ci gaban mazabunsu.
A ra’ayinmu, muna son ‘yan majalisun nan su yi la’akari da karfin tasiri da karfin ikon da suke da su wadanda suke da masaniya akansu domin yin amfani da su da zai kawo ci gaba ga wadanda suka zabesu.
A wasu wurare, ana ilmantarwa da kuma horar da ‘yan majalisu gabanin su fara aiwatar da aiyukansu. A sabili da, gabanin ‘yan majalisan su fara aiki, yana da kyau ya zamana suna da cikakken sani da kara sani kan aiyukansu domin ya zamana an samu kyakkyawar shugabanci na kwarai.
Tsayawa kan ayyukan ‘yan majalisa da kuma jajirce wa a kansu zai kare musu kimarsu da kuma tabbatar da sun ajiye tarihi mai kyau.

Exit mobile version