Babban Kalubalen Da Ke Janyo Wa Noma Koma-baya A Nijeriya, Cewar Masana 

manoma

Abubuwa da dama suna ia zamo wa fannin aikin noma babban kalubale, inda hakan zai kuma iya haifar da tabka babbar asara ga manoman da ke a Nijeriya, musamman kananan manoma da kuma wadanda sababbin shiga cikin fannin ne.

Hakan ne ya sa, wasu manoma da masu ruwa da tsaki a fannin da ke a kasar nan sunyi nuni da cewa, rabar kayan aikin gona ba akan lokaci ba, na janyowa fabnin nakasu a Nijeriya.

Sun kuma sanar da cewa, kayan aikin gona su ne mafarin gona kuma bai kamata a rarraba su da wuri ba idan har za a cimma manufar gwamnati na wadatar abinci da kuma fitar da kayan amfanin gona, inda su ka ci gaba da cewa, ayyukan gona lokaci-lokaci ne kuma ya dogara ne da yanayi, musamman a sassan duniya inda noma galibi ake ciyar da ruwa.

Sun yi gargadin cewa, duk wani yunkuri na yin watsi da lokacin noma, zai haifar da mummunan karancin kudaden da yakamata manoma su samu, musamman kananan manoma da kuma matsalar karancin abinci a cikin kasar nan.

Wani manomi a jihar Benue, Bitalis Tamongu, ya ce, akwai bukatar a dinga rabar da kayan aikin na noma akan lokaci don ka da manoma su dinga tabka asara, inda ya ce, muna bata lokaci wajen jiran kayan aikin gonar buhu biyu na takin zamani da karamin tallafin da su ke bayarwa ga manoma ba su isa ba, inda yace, wani lokaci, mukan saya daga kasuwa don saduwa da lokaci, amma su na da tsada.

Buhu daya na takin yakai kimanin nair 10,000, kuma hakan ya na shafar kudaden mu ne ba daidai ba, inda ya kara da cewa, ka san noma ya dogara ne akan lokaci, inda ya ci gaba da cewa, dole ne ku shuka, amfani da takin zamani da ciyawa a lokacin da ya dace don samun yawan amfanin kasa.

Ya ce, don haka, idan kayan masarufi su ka yi latti, amfanin gona ba zai yi kyau ba kuma yana hade da mummunan tasirin hakan kamar yunwa da talauci, da sauransu, inda manomi a jihar Benue Bitalis ya ce, za a iya magance matsalar idan har gwamnati ta fara aiwatar da rarraba wa hanyoyin kafin lokacin noma.

Ya yi kira da a kara yawan kasafin kudin aikin gona da kuma wadataccen kayan masarufi ga manoma na cikin gida don yin tasiri, inda kuma ya bukaci a fadada hanyar rarrabar da kayan ta hanyar yanar gizo, inda yace, yakamata manoma su bude shagunan a cikin al’ummomin da su ke kiwo a duk fadin kasar tare da adana su ta hanyoyin domin manoma su samu damar shigowa cikin sauki.

Ita ma wata manomi a jihar Nasarawa, Uwargida Mary Daniel, ta goyi bayan ra’ayin Bitalis, tana mai cewa, yakamata a yi la’akari da mata manoma a cikin abubuwan da su ke samarwa yayin da su ne mafi yawan manoma a kasar nan, inda tace, mata manoma sun fi na maza, amma babu abin da ya kai yawancinmu.

Ta bayyana cewa, yakamata gwamnati ta tallafa wa mata saboda takin zamani ganin cewar ya na yi masu tsada kwarai da gaske, inda ta kara da cewa, yakamata a samar da abubuwan da za a shigo da su cikin lokaci domin hadu wa da lokacin noman.

Shi kuwa Shugaban kungiyar manoman Shinkfa ta kasa Kabir Ibrahim (AFAN), ya ce yakamata gwamnati ta ba da kwarin gwiwa ga manoma domin baiwa su damar yin noma a matsayin wani kasuwanci.

A cewar Shugaban kungiyar manoman Shinkfa ta kasa Kabir Ibrahim kamar taki da magungunana yakamata a bai wa manoma cikin wadataccen adadi, a kan kari da kankantar farashi.

Wani mai ba da fatawa, Noel Keyen, wanda shine babban sakatare a kungiyar masu samar da takin gargajiya da kuma kungiyar masu samar da kayan gona ta Nijeriya (OFPSAN), ya bayyana jinkirin da aka samu game da samar da kayan gona a matsayin abin damuwa, inda ya ce, hakan zai yi mummunan tasiri kan girbi da kuma tsarin habaka tattalin arzikin gwamnati da sauransu.

Ya ce, don magance matsalar rarar kayan gona na zamani, dole ne gwamnati ta yi shirin gaba tare da nuna himma ga manufofin samar da kudaden ta hanyar ba da tallafin tare da Babban Bankin Nijeriya (CBN) don tabbatar da biyan lokaci zuwa gaggawa dillalai suna shigar da kaya.

 

Exit mobile version