Abubakar Abba" />

Babban kalubalen Mu Har Yanzu Ba’A dauki Aikin Masu Adana Bayanan Marasa Lafiya Da Mahimmanci A Nijeriya Ba— Mami

Alhaji Ibrahim Mohammed Mami shi ne Shugaba kuma Magatakardan Hukumar Adana bayanan marasa lafiya ta kasa wato HRORBN. Mami wanda kuma shi ne mai rike da sarautar gargajiya ta Rani Ikin-makum kupa da kuma sarautar gargiya ta Garkuwan Kufa Abugi a hirarsa da Wakilinmu AUBKAR ABBA a Kaduna, ya yi bayani kan nasaririn sa, kaluble da sauran su.
Wanne manyan nasarori ka samar a hukumar ?
Alhamdulillahi, da makarantun da muke dasu da suke koyarwa da wannan karatun gaskiya basu wuce a manyan Asibitocin koyarwa da muke dasu a a Nijeriya ba, a lokacin guda 14 ba. Daga baya Kwaleji wadda akafi sani da School of Health Technology, suma suka fara koyar da wannan bangaren.
Amma, daga lokacin da muka hau wannan matsayin zuwa yanzu, kafin mu hau muna da makarantu daga 32 zuwa 33 da aka basu izini su koyar, toh, amm yanzu a fadin Nijeriya baki daya, ko a Arewacin Nijeriya yanzu makarantun sun kai 40, Kudu ma suna da kusan 35.
Kaga idan ka hada, zaka ga muna da kusan 100 da suke koyar da wannan fannin a manyan Asibitoci da Kwalejojin Health Technology da kuma masu zaman kansu. Sannan kuma an sake wayarwa da al’umma kai akan shi, kan ya ya aikin yake, menene amfanin sa kuma me ake samu idan anyi shi.
Toh, da jama’a da yawa basu sanshi ba, musamman mutanen mu na Arewacin Nijeriya basu san wadannan makarantun ba alhali sana’a de wacce ta dade kamar yadda aka san aikin Likita ya dade tare suke tafiya.
Sai dai, sanin Hukumar a kuma san da zamanta a matsayin sana’ar da za’a je a koya shine kurum Likitoci suka riga mu, amma don aikin Likita ba zai yuwu ba sai ya rubuta cewa ga abinda yake damun maras lafiya, ya karbi sunan sa, shekarun sa, ya yi masa gwaje-gwaje da sauransu, in ya dauka ya zama bayaban ayyukan Asibiti, toh kaga kuwa, za’a iya cewa tare suke tafiya danjuma ne da dan Jummai.
Mun kuma bode ofishoshi a shiyoyi biyar na Nijeriya, shiyya ta shida ya rage mana a yanzu muke kai in Allah ya yarda, itama zamu bude ta. Mun kuma taso daga Legas mun dawo Abuja. kuma a lokacin da muka fara wannan aikin, muna da ma’aikata na dindin 6 na wucin gadi 20.
Toh, da muka samu da mukazo, guda 20 din nan sai mukayi kokari aka mayar dasu na dindin daga baya da dama ta samu za’a koma kan tsarin IPPIS sai muka nema a bamu damar mu dauka don mu cike gurbi, shi minister na wancan lokacin ya bada dama muka kara shigowa da mutanen.
A takaice, dai daga lokacin zuwa yanzu, muna da ma’aikata 200 da wani abu, kaga ko anan an samu nasara wajen rage rashin aikin yi a kasar nan.
Wanne manyan kalubale ne sukafi ci maka tuwo a kwarya ?
Babban kalubalen da muke fuskanta shine, har yanzu ba’a dauki aikin da mahimmanci ba, musamman shugabannin Asibiti wadanda aka dora masu alhakkin daukar ma’aikata. Toh, idan ba’a daukar ma’aikata kwararru don su gudanar da wannan aikin, kasan ba’a bai wa wannan aikin mahimmanci ba, toh, ko wannan babban kalubale ne.
Wadanda basu yi karatun ba, mafi yawancin Asibitocin su zaka ga gani suna yin aikin, toh kaga an dauki ma’aikatan ba abune da zaka je kace a kore su daga aikin ba, dole ka kyale su suci gaba da aikin duk da basu da ilimin da izini na dokar da zasu yi wannan aikin. Muna gargadin su cewa, laifi ne.
Toh amma, rashin aikin yi ya zama matsala da zaka tarar Asibitin na gwamnati su basu bayar da mahimmanci wajen daukar amar jama’ian jinya shi yasa ba’a daukar shi ma’aikacin mai tara bayanan kuma duk wannan abun da kake yi in baka adana bayanan na marasa lafiya, to kasan aikin banza kake yi. Kuma saboda rahin kwarraun masu adana bayanan na marasa lafiyar, sai kaga mutum yaje Asibiti ana neman Katin shi ba’a samu ba.
Wadanne iri matakai hukumar ke dauka kan wadanda ba kwararru a fannin ba ?
Mun dauki hanyoyin na wayar da kan jama’a da kuma su kansu masu daukar irin wadannan ma’aikatan da basu da takardar sheda kuma gwamnati ta bamu goyon baya ta yi doka cewar, masu yin aikin da basu da kata kwarewa, haka ya sabawa doka ne, sannnan su kansu masu daukar irin wadannan ma’aikatan, yanzu Asibitoci da sukafi daukar suna kokarin ganin in dai zasu sa ma’aikata, sanya wa kwararrun ma’aikatan amsu adana bayanan na marasa lafiya.
Ko a kwanan baya naga Gwamnatin Kaduna ta nemi ma’aikata naga harda ma’aikatan masu adana bayanai a ciki.
Mataslar mu yanzu wadanda basu da cikakkiyar kwrewawa a fannin, sune a wurin, amma sababbin da zasu dauka yanzu gaskiya ana kokartawa wajen daukar kwararrun, kuma munce duk wanda bai dauki kwararrun ba, zamu rubuto mashi zamu je dubawa zamu rubuta masu mu basu dan lokaci cewar, su basu dama suje suyi karatun mu basu lasisi. Ana samun nasara amma ba kamar yadda ake so ba.
Ka gamsu da kokarin da ma’aikatan hukumar keyi wajen gudanar da aikinsu ?
Sune keda damar sanin wanda ya chanchanta a bashi lasisi ko suyi masu rijista wato don a sanya su a cikin kundin ayyuka kuma su basu izini. Matsalolin biyu ne, akwai ma’aiktan wadanda aka koyar dasu kan wannan aikin akwai kuma wadanda basu da ilimin yin wannan aikin kuma duk suna hade ne suna aiki agu daya.
Su wadanda basu da ilimin aikin basu san darajar maras lafiya ba balle bayanan da ake Tarawa. Amma daga lokacin da muka fara tura tura ma’aikatan mu suna zagayawa, suna fadakar dasu kuma muka bude makarantu domin aikin sub a zai hana su zuwa makaranta ba daga Juma’a zuwa Asabar a koya maka zuwa shekaru uku a baka takardar shedar kammala karatu, kuma wadanda basu da ilimin, yanzu suna zuwa yin karatun.
Daga gun kwararrun ma’aikatan mu, ba ‘a samun matsala daga gun su. A takaice, zan iya cewa mun gamsu kan yadda suke aikin su a yanzu.

Exit mobile version