Connect with us

HANTSI

Babban Kuskuren Da Maza Ke Tafkawa Yanzu Idan Za Su Kara Aure    

Published

on

Ko wani maigida babu abun da ya kai masa kwanciyar hankali da zaman lafiya a cikin gidansa muhimmanci musamman idan mata biyu gare shi. Domin rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali yana dakile wa magidanci lissafi tare da sanya shi cikin shakku da yawan tunani. Wanda wannan zai iya kawo masa cututtuka da saurin tsufa.

Mafiya yawan maza yanzu suna tafka wani babban kuskure yayin da za su kara aure, wato kushe matarsu ta gida a wurin amaryansu. Duk wani sirrin uwargidasai ya fada mata har da ma na shi, kuma ya kasa fada wa ita amaryar halayen uwar gidan na gari saboda a ganinsa hakan bai kamata ba. Idan ta zo ta hada kai da matarsa ta gida za ta zama irin ta, ta ki masa irin biyayyar da yake so.

Ita kuma amarya lokacin da za ta shigo da gadara da takama za ta shigo saboda a ganinta ke uwargida ba ki da kima da daraja, kuma ke ba matar arziki bace sai ita. Ita yanzu ‘yar gaban goshin mai gida ce wacce ta iya biyayya da ladabin aure. Sai ka ga yarinya karama tana ci wa uwargida mutunci tana taka ta, shi kuma yana goyon bayata.

Daga nan kuma namijin ba zai sake samun kwanciyar hankali ba. Saboda idan uwargida ta kasa jurewa sai gidan ya koma filin dambe. Ana nan kuma ita wannan amaryar za ta gama daukin ta, sai ka fahimci cewa ashe uwargidanka ma ta fi wannan yarinyar ladabi da iya zaman aure.

Sai ka so ta kwantar da kai ta bi uwargida su zauna lafiya. Kana ganin za ta bi ta? Shi ya sa tun farko ba a son namiji ya bata gidansa.

Idan za ka auri mace ba a ce kada ka sanar wa matan irin abubuwan da kake so ba, za ka iya fada mata wasu abubuwan da kake so ita ta rinka maka wanda kila ka yi ka yi da matarka amma ta ki, sai ka sanar mata cewa ni ina son abu ka za, amma kada ka fada mata cewa matarka ta gida ba ta yin maka. Ya kamata ma ka fada mata alkairin uwargida shi ma dai ba kullum ba saboda idan ka cika koda uwar gidanka a wurin amarya za ta ga ita kamar baka son ta sai uwargida, ka ga ka sanya mata kishinta tun kafin ta shigo. Dole sai ka yi taka tsan-tsan, komai ya zama dai-dai wa daida.

Haka nan akwai wanda shi ma in zai kara aure in ya ga matarsa ba ta da kishi sai ya fada mata komai na amarya, idan gidansu talakawa ne yana musu alkairi duk sai ya fadi. Tana shigowa ita kuma uwargida harhada abubuwan gori da cin mutunci sai a yi ta rigima. Ba abun sha’awa bane namiji ya zama ba shi da sirri kuma baya iya bakinsa, don zai haddasa masa matsaloli kala-kala a cikin gidansa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: