Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

BABBAN LABARI: Ilimi Muka Zo Ba Al’ummar Katsina

by Tayo Adelaja
September 11, 2017
in MANYAN LABARAI
12 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Sirrin Dakile Barayin Shanu
  • Hanyoyin Da Muke Samun Kudin Aiki

Gwamnan jihar Katsina, Mai Girma Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshiki kuma gishirin rayuwa. Sannan ya ayyana wasu matakai da gwamnatin jihar ta dauka wurin dakile barazanar barayin shanu, da kuma irin ziyarar mamaya da gwamnan ke kaiwa a wuraren da ake gabatar da ayyuka a fadin jihar. Wakilan Leadership A Yau na Katsina, El-Zahraddeen Umar da Sagir Abubakar ne suka tattauna da gwamnan a gidan gwamnatin jihar.

Ranka ya dade an taba yi maka tambaya akan me gwamnatinka ta sa a gaba. Sai ka ce, ilimi ne mafi fifiko na daya, na biyu, kuma na uku a wurin gwamnatinka, mene ne dalili?

samndaads

Wato na farko dai, idan ka lura, mu a matsayinmu na Musulmi da kuma ainihin dangantakan Musulunci da mutanenmu. Annabin tsira (SAW) da ya zo, sako na farko, ce mishi aka yi yayi karatu da sunan wanda ya halicce shi, kuma Allah (T) ya ce ka bauta mishi, ka sanshi kafin ka bauta mishi. Hanyar da za ka bi ka sanshi kuma ta ilimi ne.  Sannan kuma idan ka kalli, ko a yau al’ummar da ta fi kowacce cigaba za ka ga cewa ilimi ne ya kaisu ga wannan mataki. Kuma babu wani mutum da zai yi wani abu wanda ya fi saninshi. Tunda ko haka ne, idan har kana son al’ummarka ta tsira a duniya, ta tsira a lahira sai da ilimi. Idan ka ba mutum ilimi, ka gama mishi komi.

Zai yiwu saboda rashin sani, mutum na zaune bisa kasa, ko bisa wani wuri wanda yake akwai arziki a wurin, amma babu ta yadda za a yi ya san cewa arzikin na nan idan bashi da ilimin sanin cewa a wannan wurin fa akwai arziki. Noma, tun lokacin da mutum ya fara yin haura da magirbi, shi kanshi ilimi ne. sannan kuma shi kanshi iri, da ilimi ne ake samun irin da ya cancanta, shi ya sa yanzun za ka samu gonar da take bada buhu 10 tana iya bada buhu 100, ilimi ne. sutura da muke sawa ilimi ne. komi na rayuwar dan Adam, lahira da duniya magana ce ta ilimi. Saboda haka duk mun ga a gaban idonmu da hankalinmu mun ga mutanen da suke zuwa nan Nijeriya ake sa su aiki, suke tafiyar da rayuwarsu. Amma da suka je suka samu ilimi yanzun su ke taimakon Nijeriya, ba Nijeriya ke taimakonsu ba. Ba kuma wani abu ke garesu ba, ba man fetur ko zinare ke garesu ba. Ba azurfa ko tagulla ke garesu ba, abin da suka samo kawai shi ne ilimi. Don idan ka yi ilimin, duk wadannan abubuwan da na lissafo, Allah zai baka su ta hanyar ilimin. Idan kuma ba ka yi ilimin ba, zai kasance ma kana tare dasu amma baka sansu ba.

Mun muhimmanta sashen ilimi ne saboda mun hango tashin hankalin da ke tattare da lamarin. Na farko dai  yaranmu basu cin jarabawa. Idan yara basu cin jarabawa, ka ga kenan ba zasu wuce makarantar gaba da Sakandare ba. Yanzun fa ta kai don ka yi digiri na farko ba yana nufin kana da tabbacin samun aiki bane, daidai yake da takardar Sakandire. Idan ka yi digiri na biyu ma sai ka ci shi a wani murabba’i ne za a kira ka intabiyun aikin tarayya ko irin manya-manyan kamfanonin nan, ko kuma ma za a amince maka ka koyar a wata makarantar gaba da sakandire.

 

Zuwa yanzu me za a iya cewa gwamnatinka ta yiwa harkar ilimi?

Da farko da muka zo, abin da muka ce, shi ne, bari mu kalli tushen abin, ma’ana Firamare da Sakandare. Sai muka sa kwamitinmu ya je duk firamare din da ke jihar Katsina, muka basu kayan aiki da motoci wadanda zasu iya shiga wurin da ke da wahalan shiga. Kuma muka ce su kidaya mana adadin yaran da ke zuwa Firamare, da adadin yaran da ke Sakandare. Sannan su kawo mana yawan azuzuwa, yawan malamai a duk makarantun da ke jihar Katsina. Muka ce kuma suyi kokari su bamu hasashen mafita. Ko a lokacin abin da suka ce, shi ne a yi kokari a gina azuzuwan da zasu dauki yara 50, a cike guraban malamai, sannan a siyi kayan koyon, sannan a horas da malamai kuma a samu malaman. Ko a wancan lokacin abin da ake bukata ya wuce Naira biliyan 40. Saboda shi malami, ba lallai bane ka samo shi, dole sai ka bashi horo, tunda idan ka ce siyo shi za ka yi, ba lallai bane ka samu duk malaman da kake bukata.

Kuma wani abu wanda muka fahimta shi ne, mafi yawan daraktocin da ake da su, da kuma sakatarorin din-din-din duk malaman makaranta ne asalinsu. Saboda haka kullum kwashe manyan malaman ake yi, maimakon a ce an yi tsari wanda malami yana iya kaiwa dukkan matsayin da zai kai, yana malumtan kuma yana samun albashin da ya dace, toh yanzu haka idan ka je ma’aikatu sai ka tarad da daraktoci kusan goma sha wani abu a wuri guda, wai babu yadda za a yi sun zama daraktoci sun gama kuma su koma aji. Alhali kuma mun ga shugabannin jami’o’i bayan sun kammala wa’adinsu suna komawa aji ne. Saboda haka babu dalilin da zai sa a ce don ka kai mataki na 16 a jiha kuma wai ba zaka koma aji ka koyar ba. Daga nan ka zama babban mutum, ko a baka darakta ko wani babban mukami, wanda ya gwada kamar malaman sun yi yawa ne, alhali kuma babu malaman. Wanda a hakikanin gaskiya daga Firamare zuwa Sakandare muna da tawayar da ta kai dubu 16, babu ajin da ya gaza a wancan lokacin dalibai 98. Wadansu wuraren har 258 mun samu. Daga Firamare har Sakandare din. Sannan azuzuwan basu zauno, lokacin da muka gudanar da bin diddigin yadda muhallan suke, musamman ma Firamare, kusan kaso 70% na muhallan sun lalace, kuma babu wata makaranta daya da bata bukatar gyara. Wadannan kaso 70% din sun lalace, ba zai yiwu ma ka kira su da azuzuwa ba.

 

Yallabai, ganin cewa kun samu ilimi a cikin wannan hali, da kuma irin kokarin da kuke yi. Ya zuwa yanzu kun ci kaso nawa a gyaran da kuke yi?

A shekarar da ta gabata, ainihin azuzuwa wadanda muka gyara sun fi 1,000, sannan mun gina sama da azuzuwa 798 a firamare kawai, yanzu mun kammala kusan Sakandare 13, wadanda bamu fara aikinsu ba, daga Sandamu, sai Kurfi. Amma dukkan sauran makarantun kwana na mata mun gyara kuma mun yi sabbin gine-gine ta yadda zasu iya daukan dalibai. Haka kuma zuwa shekara mai zuwa zai zama babu wata makaranta da bamu gyara ba. Sannan mun gyara yanayin tsarin azuzuwa, ta yadda cunkoso zai ragu. Yanzun mun yi kusan kaso 70%.

Tun daga yankin Funtuwa, mun kammala makarantu irinsu Makera, Dantankari, Dandume, Kabobo, zamu kuma fara Daudauwa. Muna gina sabuwar makaranta a Kadisau, sannan mun samu makarantar soji duk a Faskarin. Kankara gyaran makarantu ya kai kaso 70%. Haka nan ma a Malumfashi, a Dutsinma ma an kai kaso 65%. A Kaikai da Shargalle da Batagarawa, da Ajiwa, da Jibiya duk an gama. Yanzu aikin da zamu bayar sune na Sandamu da Baure.

Abin a nan shi ne, zai zama bamu da wani nauyi akanmu da ya wuce mu fadada zuwa kauyuka. Sannan mun aika da wadanda suke da kwarewar koyarwa a tsarin kananan hukumomi, sannan mun dauki sabbin malamai 1,196 a Firamare da Sakandare. Wanda wannan kawai ya cike gurbin ne da kaso 25%. Muna sa ran zuwa shekara mai zuwa mu cike gurbin ya kai da kaso 50%, saboda ba zai yiwu a iya cike guraben dari bisa dari ba. Su malamai dole ne a horas dasu, saboda wasu zaka gansu da takardan koyarwa amma kuma basu da kwarewar.

Haka kuma don tabbatar da cewa an yi abin da ya kamata, sai muka sake gabatar da jarabawar sharer fage ta ‘Mock’ a Sakandare. Saboda babu hikima a ce baka shirya dalibi domin ya fuskanci wata jarabawa ba, kuma ka kaishi domin yayi wannan jarabawar, dole ne ya fadi. Wai kai kawai don kana son ka ce ka yaye dalibai 10,000. Toh don ka yaye dalibai 10,000 amma kuma baka samu abin da ake so ba, ina amfaninshi?

Abin da muka zo muka taras shi ne sama da dalibai dubu 46,000 ne suke zana jarabawar kammala Sakandare duk shekara. Abin da muke samu kuma 10% ne, kuma wannan ya hada har da makarantun kudi. Sannan wadanda ke makarantun kudin nan, ‘ya‘yan manya ne, su kuma ‘ya‘yan talakawa suna makarantun gwamnati basu da wata dama.

 

Natsuwa da kayi da gyaran da kuka yiwa makarantun gwamnati ne ya sa ka sa ‘ya‘yanka?

Abin da muka ce, zamu dauko ‘ya‘yanmu mu sanya su a makarantun gwamnati, don mu tabbatar da cewa an yi abin da ya dace. Wannan ma zai sa jami’an gwamnati su mayar da hankali wurin gyaran makarantun, a maimakon kowa yayi abin da ya ga dama don ‘ya‘yansu na makarantun kudi, ina mai tabbatar maka da cewa yau makarantunmu na gwamnati a jihar Katsina sun fi duk wata makarantar kudi. Dama kuma abin da za a kashe a gyara makarantun bai taka kara ya karya ba. Kawai dai an yi sakaci ne. kuma ba sakacin gwamnati kadai ba, laifin al’umma ne gabadaya. Wasu iyayen basu ma san ko ‘ya ‘yansu na zuwa makaranta ba, ko basu zuwa. Don haka yanzu da muka ce sai danka ya ci jarabawa sannan zamu biya mishi kudin jarabawar karshe, sai gashi sakamakon jarabawar WAEC ta wannan shekarar ta fito fes. Yanzun zaka ga mutane sun fara mayar da hankali akan lamurran makarantun gwamnati. Akwai makarantar da na je, tana da yawan dalibai sama da dubu 7,000 amma idan hedimasta ya kira PPA bai fi mutum 50 suke zuwa ba, saboda iyayen basu damu da batun ilimin ‘ya’yansu ba.

 

An shaidi jihar Katsina da zaman lafiya, wadanne hanyoyi kuka bi wurin tabbatar da wannan shaida da aka yiwa jihar?

Lokacin da muka zo, ana fama da satar Shanu da garkuwa da mutane da kashe – kashe a nan jihar Katsina. Shekarar da daga ita sai shekarar zabe, akwai lokacin da rana guda aka kashe mutum fiye da dari da doriya, akwai lokacin da aka samu mutane fiye da goma sha aka yi musu yankan rago a garin Gidan Maidan. Muna gwamnatin nan akwai lokacin da barayi suka je suka tayar da gari guda, kullum batun kenan satar Shanu. Kullum sai an kawo mana rahoton sirri na fafatawa da barayi, da kashe – kashe. Wannan ne abin da muka zo muka samu na faruwa a jihar Katsina.

Ina jin yanzun idan mun gama magana kamata yayi ace na tafi Jibiya. Abin dake faruwa idan kana zaune aka aiko maka cewa an yi ayyukan da ka sa, kai ne zaka biya. Shi yawon duba aikin yana sa idan ka ga akwai bukatar kari a wani wurin zaka yi nan take, idan akwai gyara ma zaka sa a gyara nan take. Kuma shi me aikin da me duba aikin sun san cewa zaka iya zuwa ba tare da ka sanar dasu ba. Idan na tashi zuwa wurin duba aiki bana sanar da Injiniya, bana sanar da dan kwangila, abin da na taras lebura nayi, dashi zamu yi magana. Domin kowanne dan kwangila idan ya san abin da yake yi, ai yana da wakili, sannan kuma kowanne aiki mun sa mai sa ido. Saboda haka idan muka samu babu wakilinka, akwai matsala. Idan ma’aikatan gwamnati ne mun je babu su, mun san akwai matsala. sannan kowa zai shiga taitayinsa, saboda an san ina zuwa duba aiki da ziyarar ba-zata.

 

Yallabai, kafin zuwan gwamnatinka ka yi alkawarin da zaran kun hau za ku sakarwa kananan hukumomi mara. Ina aka kwana kan batun zabe?

Toh da farko dai kafin mu zo, mun dauka ma suna da mara din, da muka zo sai muka ga basu da marar, sai an yi musu marar ma kafin nan a sake ta. Ai tsarin mulki cewa yayi kananan hukumomi ana shugabancinsu ne ta hanyar zababbu. Mun samu zababbu, sai muka taras mafi yawansu sun sa hannu a takardun dake an kwashe kudin kananan hukumomi fiye da Naira biliyan 10 da doriya, wanda yake aka ce su aka ba, su kuma suka ce basu san da zancen ba. Wannan ya sa dokar da ita gwamnatin da muka gada ta yi, ta ba gwamna da majalisa dama cewa a rusa su akan wadannan laifuffuka, wanda a halin yanzu muna kotu. Shugabannin kananan hukumomi, Kansiloli, jam’iyya da mataimakan ciyamomi sun kai mu kara, kara iri hudu suka kai mu, wanda kuma mun kayar dasu a duk sauran kotunan, yanzun sun daukaka kara a kotun daukaka kara. Muna jiran yanke hukunci. Idan mun gama da wannan sannan sai mu dawo mu waiwaiyi abu na gaba.

Gwamnatin tarayya ta bamu biliyan 10 cikin kudadenmu wanda aka ce mu yi ayyuka. Wanda muka sa biliyan 3 a ilimi, biliyan 2 da rabi a kiwon lafiya, biliyan biyu da rabi a ruwa, sannan kuma biliyan biyu a noma. Sannan kuma da kudin shiga da muke samu na jiha, idan mun biya albashi, sauran da suka rage sai mu yi amfani da su. sannan kuma mun samu kudin ‘Paris Club’ mun biya fansho da sauransu. Wadannan ‘yan raran kudaden dasu ne muke aiki. Ina tabbatar maka bayan da Allah ya dora mana lalura ta kananan hukumomi, da sai mun canza fuskar jihar Katsina. Idan da mu muka samu damar da na baya suka samu, da wallahi mun canza fuskar jihar Katsina. Matsalar kawai da muka samu, shi ne na tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

 

Wane sako kake dashi ga al’ummar jihar Katsina?

Muna godiya ga mutanen jihar Katsina bisa addu’o’in da suke yiwa shugaba Buhari, ina yi musu godiya ta musamman kuma ina jinjina musu, domin a duk wasu al’amura nasu; radin suna ko aure, sai ka ji ana yi mishi addu’a. Sannan kiran da nake yi musu, mu fa kofarmu a bude take, duk abin da aka gani ba daidai ba a tambaye mu, indai hakki ne na jama’a zamu bayar da amsa. Ba mu ce bamu kuskure ba, saboda mu ba ma’asumai bane, idan an ga mun yi kuskure a gyara mana. Sannan jama’a sai sun yi hankali da bayanan karya da ke fitowa daga makiyan gwamnati.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

BABBA DA JAKA

Next Post

An Kaddamar Da Jirgin Ethopia A Kaduna

RelatedPosts

Kawuna

Kawuna Ya Turo Ni Kano Don Yin Garkuwa Da Mutane, In Ji Maryam  

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Maryam Muhammad, wadda ta shahara wajen...

Beli

Ka Sake Ba Ni Beli – Maina Ga Alkali

by Muhammad
3 days ago
0

Ya Ce, Da Gaske Ba Shi Da Lafiya Daga Khalid...

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Next Post

An Kaddamar Da Jirgin Ethopia A Kaduna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version