- Minista Ya Tona Asirin Masu Daukar Nauyinsu
- Tufka Da Warwara Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Siyasa
Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano da Abubakar Abba, Kaduna.
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biyafara a matsayin kungiyar ‘yan-adda.
Gwamnatin ta bayyana cewa yanzu ta samu izinin Babbar Kotun tarayya da ke Abuja, bayan da ta kai batun gabanta cikin gaggawa domin samun sahalewar kotun bayan da Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan takardar haramta kungiyar. Ministan sharia’a kuma Babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, ya tabbatar wa BBC cewa izinin kotun ya ba su damar ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar ma su fafutukar kasar Biyafara, wasu marasa kishi ne a kasar nan suke daukar nauyin su don su yi wa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhar zagon kasa da sunan neman ‘yancin alummar Gabas Maso Yamma.
Ministan ya yi nuni da cewa, dole ne ‘yan kasa su san cewar kungiyar an kafa ta ce da nufin kwatowa inyamurai ‘yancin su ba, sai dai kawai don a yi amfani da ita a wargaza kasar da karkatar da hankalin ‘yan kasa a kan kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen samar da ayyukan more rayuwa ga ‘yan kasa.
A cewar Ministan,” kungiyar wasu ne da zan iya danganta su ‘yan siyasar da ta kare ma su suka rasa abin yi, sai kuma gungun wadanda suka tabka satar dukiyar kasa.”
Ya ce, ma su daukar nauyin na su, sun yi imanin cewar ta hakan ne kawai za su iya wargaza kasar nan.
“Bari ku ji in fada muku, mun san cewa kungiyar nan tana samun tallafin kudi daga mutane da yawa a kasar waje, suna samun makudan kudi a hannun wasu mutane da ke Nijeriya kuma suna karba daga hannun wasu da ke wajen kasar nan. Karshen Magana ma dai bari ku ji, shalkwatar samun kudinsu a kasar Faransa take, kuma abin da na fada kenan a kwanan baya.
A baya Nijeriya ta taba antayawa rikicin yakin basasa da ya janyo asarar rayuka da dama gami da dukiya. Wanda daga bisani hakan ya haifar da cututtuka tare da kuncin rayuwa da tsananin talauci. Duk da Ojukwu da ya jagoranci yakin ya tsallake zuwa wata kasa domin neman mafaka, daga baya ya dawo ya nemi afuwa an kuma yafe masa tare da ba shi dukkan hakkokinsa na aikin soja. Daga bisani, Hhar takarar shugaban kasa ya nema a jam’iyyar APGA.
A wata tattaunawar faifan bidiyo da aka taba yi da shi, an tambaye shi dangane da kiraye-kirayen da wasu matasa ‘yan bana bakwai ke yi masa a kan ya dawo a kara tayar da kura na raba Nijeriya. Sai Ojukwu ya kada baki ya ce; ‘Suna cewa kai ne ka jagoranci yamutsin da aka yi na baya, yanzu ma ka kara jagorantar mu a kara tayar da hankali. Da gaske cikin alfahari na jagoranci yakin baya, amma a halin yanzu ban yi tsammanin akwai bukatar kara maimaita jagorantar raba Nijeriya ba’
Duk da wannan gargadi na Ojukwu hakan bai hana Nnamdi Kanu sabunta wannan kudiri ba, wanda Hakan ya sa shi barin birnin Landan zuwa Nijeriya ya fara hada kan matasa masu jini a jika. Ba tare da bata lokacin ba gwamnatin Nijeriya ta kama shi tare da garkame shi a gidan yari. Wannan ya janyo matsin lamba daga wasu bangarori na lallai sai an sake shi, wanda shugaban kasa Mmuhammadu Buhari ya ayyana cewa, ba zai sake shi ba kasancewarsa mamallakin fasfo da yawa da idan ya arce bai san inda zai kama shi ba. Wane tudu wane gangare yayin da shugaban kasa ya ke birnin Landan neman lafiya, sai kotu ta bayar da belinsa gami da ayyana masa wasu sharudda. Sakin sa ke da wuya ya ci gaba daga inda ya tsaya, ba tare da kiyaye wancan sharudda da kotu ta gindaya masa ba. Lamarin ya kazanta ta yadda ya rika jagorantar tawagar matasa daga gari zuwa gari a matsayin fafutukar kafa kasar Biyafara.
Rundunar sojoji sun kai dauki dangane da kisan gilla da ake yi wa ‘yan arewa mazauna yankin Inyamuran, kana kuma lokaci guda suka ayyana kungiyar a matsayin ‘yan ta’adda. Rahotanni na cewa madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da iyayensa sun bata. Hakan na faruwa ne bayan sojoji sun kai samame gidansa a kauyen Afaraukwu da ke jihar Abia ranar Alhamis da maraice. Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa dakarun tsaron hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun mamaye gidan mahaifin Kanu inda suka rika yin harbe-harbe. Sai dai sojojin Nijeriya sun ce ba ya gidan lokacin da suka je.
- Sojojin Nijeriya Sun Ayyana IPOB A Matsayin ‘Yan Ta’adda
Rundunar sojin Nijeriya ta ayyana madugun kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra da magoya bayansa a matsayin ‘yan ta’adda. Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar tsaron kasar Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce kungiyar, “ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasa”. Ta kara da cewa, “Bayan mun yi nazari a tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama’a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta’addanci ne”.
Ayyana wannan kungiya a matsayin ta ‘yan ta’adda na nufin za a iya kama su sannan a garkame su. Sai dai matsalar da hakan za ta iya janyowa ita ce ta yadda rundunar sojin ta gaza gane irin goyon bayan da IPOB ke da shi a kudu maso gabashin kasar. Kazalika, sanya su a cikin jerin ‘yan ta’adda na nufin dakarun sojin za su fuskanci kungiyoyin ‘yan ta’adda uku wadanda suka hada da Boko Haram da tsagerun yankin Naija Delta da kuma su.
- Abin Da Gwamnonin Yankin Kudu Maso Gabas Suka Yi
Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Nijeriya sun ba da sanarwar haramta ayyukan kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB a daukacin shiyyar. Shugaban kungiyar gwamnonin, Dabe Umahi na jihar Ebonyi, bayan wani taron gaggawa a Enugu, ya bukaci kungiyar da sauran kungiyoyi irin ta su fayyace abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kuma su aikawa gwamnonin.
“Duk wasu aikace-aikace na kungiyar IPOB yanzu, sun haramta. Ana shawartarta da sauran kungiyoyin da suke jin an yi musu ba daidai ba, su fayyace matsayinsu kan duk wasu batutuwan kasa.”
Gwamonin sun hadar da na Jihar Abiya da na Anambra da na Ebonyi da na Enugu da kuma mataimakin gwamnan Jihar Imo. Sai kuma shugabancin kungiyar Ohaneze Ndigbo mai kare muradan al’ummar Igbo da mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu.
Dabe Umahi ya yi kira ga daukacin gwamnonin yankin su tabbatar da aiki da wannan umarni a jihohinsu. Ya kuma roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Allah ya janye dakarun sojin da ke yankin.
Gwamnan ya ce kungiyarsu ta yi imani da hadin kai da dunkuluwar Nijeriya waje guda, ko da yake tana bukatar sake fasalin kasar. A cewarsa: “Muna nanata muradinmu na sake fasalin Nijeriya, inda za a rika tattauna dukkan batutuwan kasa don samun masalaha cikin ruwan sanyi da nufin tabbatar da adalci da daidaito ga duk dan kasa.”Ya ce kungiyar tana tuntubar gwamnonin arewacin kasar wadanda suka ba ta tabbacin tsare rayukan mutanensu da ke arewa, har ma sun shirya ziyartar juna don karfafa gwiwa.
“Muna tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa ana gudanar da cikakken bincike a kan duk zarge-zargen kashe-kashe da jikkata mutane gami da sauran abubuwa na rashin bin doka da aka aikata a yankin lokacin hargitsin,” in ji Dabe Umahi. Gwamnan ya ce za a dauki matakan da suka dace a kan duk mutumin da aka samu da hannu wajen aikata hakan. Ya ce gwamnoni a yankin Kudu Maso Gabas sun dauki matakai kwarara don kare rayuka da dukiyar ‘yan asali da ma wadanda ba ‘yan asalin yankin ba.
- Mu ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne — ‘Yan Biyafara
Sai dai kuma, ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biyafara sun ce su ba ‘yan ta’adda ba ne.
- Tufka Da Warwara Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Siyasa
Da farko, kafin kotu ta tabbatar da ta’addancin ‘ya’yan IPOB, shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Bukola Saraki, ya ce ayyana kungiyar IPOB mai fafatukar kafa kasar Biyafara a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda da sojin Nijeriya ta yi, bai dace da kundin tsarin mulkin kasar ba. A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bukola Saraki ya ce dokokin Nijeriya sun fitar da matakan da za a dauka kafin a ayyana wata kungiya a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda. Bukola Saraki ya ce yana fatan cewar Shugaba Muhammadu Buhari, zai fara bin hanyar da ta dace wajen ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda domin nuna wa duniya cewar Nijeriya kasa ce wadda ke bin doka a ko wanne hali.
Saboda haka, Saraki ya ce wadanda suke ta magana a kan wannan su sha kuruminsu. Kazalika, Sanata Saraki ya ce dole a jinjina wa rundunar sojin Nijeriya kan kokarinta na wanzar da zaman lafiya a sassan kasar da kuma kiyaye hadin kan kasa. Duk da haka, shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata sojin kasar su bi horarwar da suka samu na mutunta hakkin bil’adama a lokacin da ake takalar su.
Ita kuma a nata bangaren, rundunar sojin Nijeriya ta musanta cewa ta ayyana kungiyar ‘yan aware a matsayin ‘yan ta’adda. Amma kuma yanzu sojojin sun ce sun so ankarar da al’umma ne kawai game da barazanar da kungiyar ke tattare da shi, ba wai sun ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba ne a hukumance. Wasu ‘yan kasar ma da dama da suka hada da masu fada a ji, sun nuna rashin dacewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar tun da farko ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda. Masu sharhi dai na ganin ayyana IPOB a matsayin ‘yan ta’adda ka iya haifar da wata matsalar.
- Me ya hana Saraki magana lokacin da ake zubar da jinin kabilar Hausa-Fulani? Ko kuwa don su dabobi ne, ba mutane ba? Watakil kuma, don ba kabilarsa ba ne, kai tsaye ko?
- Mece ce damuwarsa don an ayyana IPOB a kungiyar ‘yan ta’adda? Ko tsoronsu yake? Zai kuma iya zama neman suna ko?
- Shin me ma yake nufi da “su sha kuruminsu?” Yana nufin zai yi abin da ya saba, na fatali da duk abubuwan cigaban da ake kawo wa majalisar, lokacin da aka kawo batun ‘yan Biyafaran gabansa kamar yadda wasu ke ma sa zargi?
Yanzu dai, an yi walkiya, an ga launin jikin kowa. Ya rage ga talakawa, mu dau mataki, da kuri’unmu, a kan irin wadannan shugabanni marasa kishinmu; marasa amfani a rayuwarmu. Idan kuma son zuciya ya hana mu hakan, to, lallai za mu cigaba da wulakanta, har karshen rayuwarmu.