Daga CRI Hausa
Daga ranar 30 ga watan Maris zuwa ranar 2 ga watan Afrilun bana, babban sakataren kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, gami da wasu jakadun kasashen waje da jamian diflomasiyyar kasashe 21 dake kasar Sin, sun kai ziyarar aiki a wasu sassan dake jihar Xinjiang, ciki har da Urumqi, da Kashgar, da Akesu, inda suka binciki yadda ake raya tattalin arziki, da inganta rayuwar alumma, da kyautata muhallin halittu, gami da tabbatar da yancin bin addini a wurin.
Jamian diflomasiyyar sun hada da na kasashen Iran, Pakistan, Rasha, Nepal, Azerbaijan, da Armenia, da Tajikistan da Belarus da suransu. Zangon farko da suka yada a jihar Xinjiang, shi ne bikin nune-nunen ayyukan yaki da taaddanci da kokarin kawar da masu tsattsauran raayi, inda jakadu da dama suka jinjina gami da marawa gwamnatin kasar Sin baya a wannan fanni.
A nasa bangaren, jakadan kasar Pakistan dake kasar Sin, Mista Moin ul Haque ya bayyana cewa:
Yau na kalli nune-nunen, inda na kara fahimtar tarihin jihar Xinjiang, musamman kara samun fahimtar yadda gwamnatin kasar Sin take kokarin dakile ayyukan taaddanci da kawar da masu tsattsauran raayi. Ina tare da gwamnatin kasar Sin, don mu shawo kan taaddanci, wanda shi ne makiyinmu dukka.
Har wa yau, jamian diflomasiyyar sun ziyarci wasu wuraren ibada, ciki har da cibiyar karatun Alkurani mai girma ta Xinjiang, da babban masallacin dake birnin Urumqi mai suna White Mosque, da masallacin Etigar dake birnin Kashgar, inda suka zurfafa musayar raayi game da aikin horas da malaman addinin Musulunci, da yadda ake gudanar da ayyukan ibada da kuma tabbatar da yancin bin addini na alumma.
A nasa bangaren, jakadan kasar Iran dake kasar Sin Mohammad Keshavarzzadeh ya bayyana cewa:
“Na ga musulmi a wajen suna zuwa sallah a masallatai daban-daban, wato rahotannin da wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya masu kyamar kasar Sin ke kokarin yadawa game da Xinjiang, ba su da tushe ko kadan balle makama. Ziyarar gani da idonmu na da matukar muhimmanci. Wato ban ga wasu manyan bambance-bambance tsakanin jihar Xinjiang da sauran sassan kasar Sin ba.” (Mai Fassara: Murtala Zhang)