Connect with us

MANYAN LABARAI

Babban Taron Kamfanin LEADERSHIP Na Shekara:

Published

on

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Wa Gwamnoni Bulala

  • Kila A Sha Wuya Kafin Jihohi Su Fahimci Gaskiyar Lamari

      – Sam Nda-Isiah

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kalubalanci Gwamnonin tarayyar kasar nan cewa kar su tsaya jiran sai an yi garambawul ga tsarin mulkin kasa ko sake fasalin kasar kafin su fara cin gajiyar albarkatun da Allah ya huwace wa jihohinsu.

Ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara da Rukunan Kamfanin LEADERSHIP ke gabatarwa duk shekara da ya kunshi muhimman jawabai kan cigaban kasa da kuma ba da lambobin yabo ga hazikan mutanen da suka ba da gudunmawa ga bunkasar Nijeriya a cikin shekara.

Mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa lokaci ya yi da jihohin za su fara aiki tamkar kasashe masu cin gashin kansu, kasancewar hanyoyin da ake samun nasara a cikinsu na iya sauya a koyaushe.

“Muna fuskantar wani zamani da jihohinmu ya kamata su dage da gasa a tsakaninsu wurin samun wadanda za su zuba manyan jari a cikinsu. Wannan ba sabon abu ba ne, tuntuni wasu sun dauki salon haka a duniya. Ku yi tunanin irin tagomashin da Nijeriya za ta samu ba tare da bata lokaci ba.

“Jiha za ta iya saukaka wa masu zuba jari wurin mallakar fili, da rajistar filin, da biyan haraji da samun karfin sadarwar intanet kuma idan ta yi haka za ta iya zama zakaran gwajin dafi, sannan wadanda suka tsananta wa masu zuba jarin za a bar su a baya suna tsintar hula, domin duniya za ta cigaba ba tare da su ba.” Ya bayyana.

Farfesa Osinbajo ya kuma fito wa jihohin da wata mafita idan wannan ya gagara inda ya ce, “idan wannan dabarar ta zama da tsauri, ku duba yiwuwar shiga tsundum a dama da ku a bangaren sadarwar zamani wanda tabbas ba ya bukatar nauyayan abubuwa”, yana mai buga misali da cewa fasahar sadarwar ta ba da gudunmawa ga habakar karfin tattalin arzikin Nijeriya tun a shekaru 20 da suka gabata.

Wakazalika, mataimakin shugaban kasan ya ce a halin yanzu wajibi ne ko wace gwamnatin jiha ta san yadda za ta yi ta bunkasa kudadenta na shiga da kuma tsimin kudaden da ake kashewa ba gaira ba dalili a sassan da ba za su kawo habakar tattalin arziki ba da kuma duba matakan da za a dauka domin rayuwar gaba ta yi kyau.

“Ya dace Gwamnoni su rika yin tunanin abubuwan da za a ci gajiyarsu ba a a tsakanin shekara hudu ko takwas kawai ba. Wajibi ne a dukufa ga shimfida turba mai kyau.”, in ji shi.

Farfesa Osinbajo ya kuma nunar da cewa a nata bangaren, Gwamnatin Tarayya tana fadada hanyoyin samun kudin shiga ciki har da kara yawan masu biyan haraji daga milyan 14 zuwa milyan 20 daga cikin ‘Yan Nijeriya masu gudanar da kasuwanci da sauran abubuwa na cigaban tattalin arzikin al’umma.

Har ila yau, a fannin aikin gona ya ce suna kara shimfida turbar bunkasa sashen, da samar da ayyukan yi da rage shigo da kayan amfanin gona daga waje da bunkasa fitar da su domin sayarwa a kasashen duniya.

Ya ce tun da filayen noma a karkashin yankunan jihohi suke, jihohin da suka mayar da hankali a kan aikin gona sun samu cigaba ta fuskar inganta rayuwar al’ummarsu, tare da nunar da cewa Jihohin Kebbi da Jigawa sun kara bude wa manomansu hanyoyin samun kudin shiga.

Shi ma a nasa jawabin, bako mai gabatar da lacca a taron, tsohon Gwamnan Jihar Kuros Ribas, Donald Duke ya yi gargadi game da rashin katabus din jihohi wajen samar wa kansu mafita da kuma kyautata jindadin rayuwar al’ummominsu.

Ya ce irin wannan sakacin babbar barazana ce ga makomar kasar, don haka ya yi kiran daukan kwararan matakai domin habaka tattalin arzikin kasa.

Tsohon Gwamnan ya kuma bayyana bukatar kara aukin kudin da ake kashewa a bangaren samar da abubuwan more rayuwa wadda a cewarsa hakan na da alaka sosai da samun kudin shiga mai tsoka.

Bayan ya kawo misalan jihohin da suke da masana’antu na kashin kansu, Donald Duke ya ce kafa masana’antu babbar dabara ce ta samun kudin shiga ga ko wace jiha a fadin tarayyar kasar nan.

Shi kuwa babban mai gayyatar taron, shugaban Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Sam Nda-Isiah, ya ce wadanda aka ba su lambobin yabo a taron sun cancanci yabo saboda irin matakan da suka tsallaka kafin su yi nasarar zama zababbun da za a bawa.

Ya bayyana cewa, saboda hanyoyi masu nagarta da kamfanin ke bi wajen zakulo wadanda za a baiwa lambobin yabon na LEADERSHIP tun daga shekarar 2008 da aka fara, har yanzu taron ba shi da na biyu wurin daraja da kima a fadin kasar.

Ya nunar da cewa ba da jimawa ba jihohi za su daina rugawa wurin Gwamnatin Tarayya suna neman a taimake su da kudi domin ita ma kanta gwamnatin za ta shagaltu da batun warware kalubalenta na tarayya. Yana mai cewar, “kyakkyawan albishir a nan shi ne ko wace jiha a Nijeriya za ta iya tsayuwa da kafafunta da arzikinta, kawai dan kankanen zurfin tunani shugabannin jihohin za su yi a cimma haka”.

Sam Nda-Isiah ya kara da cewa “Duniya tana sauyawa, mu ma kasarmu tana sauyawa, kuma duk wani shugaba da bai yi la’akari da wadannan sauye-sauyen ba ba abin yarda ba ne a wurin jama’a.

“Wadanda suke shugabanci da wadanda suke da niyyar yi a matakin jiha wajibi ne su fahimci cewa kida ta canja kuma dole rawa ta canja. Ya zama wajibi gwamnatocin jihohi su yi tunanin hanyoyin da za su samar wa kansu da kudi domin su rayu. Gwamnatin Tarayya ba za ta cigaba da taimakon jihohin kamar wasu shagwababbun yara ba”, a ta bakinsa.

Ya kara da cewa, “Watakila za a sha wahala kafin jihohi su fuskanci gaskiyar al’amari. Jihar Legas ta bi hanya mai wahala wajen cimma wannan burin nata lokacin da Shugaban kasa Obasanjo ya kulle asusun kananan hukumomin jihar saboda wasu dalilai na kashin kansa, a wannan lokacin ne gwamna mai ci wato Bola Tinubu ya yi tunanin mene ne mafita.

“Duk jihohi ya kamata su gane hanyoyin shigar kudaden su, misali Legas su babbar hanya shigar kudade gare su ita ce harajin manyan kamfanoni, wasu jihohin kila nasu a albarkatun karkashin kasa ne, wasu kuma kila filayen noma.

“Duk jihar da ta ce wai tana jira a yi wa kundin tsarin mulki gyara don ta samu hanyoyin tara kudaden shiga to ba ta yi dabara ba, gwamma ma su nemi izinin hako ma’adanan karkashin kasa daga gwamnatin tarayya. Abin takaicin shi ne babu jihar da ta ke kokarin yin hakan, akwai jihohin da noma ta fara taimaka wa tattalin arzikin su, wannan farar dabara ce.

“Bostwana yar karamar kasa ce a kudancin Afirka amma tana da arzikin dutsen lu’u-lu’u, kamar yadda jihohin Nijeriya da dama suke da arzikin ma’adanai, shugabannin Bostwana sun yi farar dabarar gayyato wani kamfanin kasar Afirka ta Kudu mai suna De Beers domin taimaka wa tattalin arzikin kasar su ya habaaka, in Nijeriya ta yi irin yadda Bostwana ta yi, to lallai za a samu cigaba sosai a fannin tattalin arziki”.

A cigaba da jawabin shugaban kamfanin; ya kuma ce “Akwai wani misali ma a yankin Atalanta ta kasar Amurka, suna da filin tashi da saukar jiragen sama da ya fi kowanne zama mafi jigilar jirage a duniya, wannan filin jirgin karamar hukumar Atalanta ce ta gina da kan ta.

“A bayan Atalanta na daga cikin matalautan garuruwa da ke jjhar Georgia ta kasar Amurka, shugabannin garin suka nema wa kansu mafita, cikin ikon Allah sanadiyyar wannan tunanin yanzu suna daga cikin manyan masu arziki a kasar Amurka gaba daya.

“Wannan kadan ne daga ciki, amma akwai hanyoyi da daman gaske, na dan sosa mana inda yake yi mana kaikayi ne, ina fatan gwamnatocin jihohi zasu fara muhawarar samar wa kansu mafita. Lokaci ya yi da jihohi za su daina fafutika wajen raba arzikin kasa, abin da shugabannin baya suka yi kenan lokacin ba bu batun kudin rarar man fetur, wannan kokarin nasu ya sanya yanzu yankunan kasar nan suke tsaye da kafafunsu”.

Daga bisani ya yi godiya ga mahalarta bikin tare da addu’ar Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

Taron na jiya Alhamis shi ne na shekarar 2017 wanda ya kunshi ba da lambobin yabo ga mutanen da suka yi zarra a shekarar wajen taimaka wa cigaban kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: