Babban Taron Kasa Kan Raya Tattalin Arziki Ya Fidda Hanyoyin Daidaita Tattalin Arziki

Daga CRI Hausa,

Daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Disamba, babban taron kasar Sin na shekara-shekara kan raya tattalin arziki ya gudana a Beijing.

Mafi yawan manyan kafafen yada labaran kasa da kasa sun dauki Kalmar “daidaitawa” daga cikin jawabin bayan taron wanda kasar Sin ta fitar da yammacin ranar 10 ga watan Disamba. Taron ya fitar da wata alama mai karfi game da daidaita tattalin arziki.” Kafar yada labaran Singapore “Lianhe Zaobao” ta yabawa wannan tsarin. Ita ma kafar yada labarai ta Bloomberg ta maimaita kalmar “daidaitawa sau 25 a cikin sanarwar bayann taron na bana.(Ahmad)

Exit mobile version