Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya.
Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da kuma kungiyar AU.
A karkashin taken “garambawul ga tsarin shugabancin duniya: sabbin rawar da za a taka da kudurori na hangen nesa ga hadin gwiwar Sin da Afirka,” taron ya mayar da hankali ne kan yadda hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai da kungiyoyin kwararru zai iya ba da gudummawa wajen tsara shugabanci na duniya mafi adalci da ya hade kowa da kowa.
Taron ya kuma kunshi fitar da wani rahoto na kwararru mai taken “gina sabon tsarin shugabancin duniya–yin aiki tare don neman samar da tsarin shugabancin duniya mai adalci da ma’ana,” da kuma kaddamar da turbar sadarwa ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa mai lakabin “hadin kai a cikin zukata, hanya da kuma aiki–shirin aiki kan karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2026.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)













