Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Babban Taron NIS Zai Inganta Matakan Tsaron Kasa Da Tattalin Arziki – Babandede

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bude babban taron mahukuntan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa na shekarar 2019 a Legas.

Babban taron na kwana uku an tsara shi ne ta yadda zai kara wa mahalartansa wadanda suka kunshi kanana da manyan mataimakan shugaban hukumar ta NIS, kaifin basirar aiki. Mahalartan dai sun fito ne daga manyan ofisoshin shiyyoyin NIS guda takwas da kuma shalkwatarta da ke Abuja.

Har ila yau, babban taron zai zama wani fage da za a yi kyakkyawan tsari na cimma wasu muradun aiki na Hukumar NIS daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Taron zai kuma tattauna batutuwan da suka jibanci dabarun aiki ga mahukuntan na NIS, sabon tsarin biza, bitar matakan yin fasfo na zamani, tsaron kan-iyakokin kasa, ba da rahoton halin da ake ciki game rajistar baki da sauransu.

Sanarwar da Shugaban NIS, Muhammad Babandede ya fitar ga manema labarai ta hannun jami’in yada labarun hukumar, Sunday James, ta bayyana cewa Ministan ya ba da umurnin cewa wajibi ne taron ya mayar da hankali kan manyan maunufofin gwamnatin Shugaba Buhari da suka kunshi tsaro, tattalin arziki da rikon amana wurin tsara ayyukan da ake muradin gudanarwa.

Haka nan, ya bukaci NIS ta kasance a sahun gaba wajen tabbatar da tsaron kan-iyakokin kasa domin samun bunkasar tattalin arziki da mayar da Nijeriya kasa mafi dadin zuba jari ga masu zuba jari na kasar waje ba kuma tare da sakaci da tsaron kasa ba.

Da yake gabatar da jawabinsa a taron bayan budewa, Shugaban Hukumar ta Shige da Fice, Muhammad Babandede ya yaba da kamun ludayin ministan cikin gidan wanda ya ce yana da himmar yin abu da kansa ba tura dan sako ba.

“Ina wa mai girma Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola barka da zuwa wannan taron wanda kwata-kwata bai wuce mako daya da ya karbi ragamar shugabancin ma’aikatar cikin gida ba. Ya zama wajibi in yaba da kwarin gwiwarsa da dukufa ga aiki ta hanyar gane wa idonsa yadda abubuwa ke gudana, kwana daya da rantsar da shi ya ziyarci shalkwatar hukumarmu kuma ya kewaya ko ina. Mai girma minista, muna godiya gare ka bisa amincewa ka bude wannan taron mai muhimmanci.”

Babandede ya bayyana wa mahalarta taron cewa shekaru uku da suka gabata sun yi irin wannan taron a Kano inda aka fitar da tsare-tsaren aiki na hukumar daga shekarar 2016 zuwa 2019.

“Tsare-tsaren da aka yi ba sun yi mana kyakkyawan jagoranci ga ayyukanmu ba ne kawai, har ila yau sun ba mu damar yin waiwaye adon tafiya ga ayyukanmu domin ganin ko muna yi kamar yadda ya dace cikin tsarin da aka yi domin gano wuraren da suke da bukatar gyara a gyara, da tilasta bin matakan da aka tsara ko bullo da wasu sababbin dabaru da za mu yi aiki da su don sauke nauyin da ke wuyanmu. Don haka, wannan taron wata dama ce da za mu yi waiwaye adon tafiya mu ga ko kwalliya ta biya kudin sabulu da kuma sake tsara abubuwan da za su yi mana jagorancin ayyukanmu a shekaru masu zuwa.”

A cewar Babandede, ko shakka babu yin hakan zai kara musu kwazon inganta ayyukansu, kana ya hori mahalarta da kar su manta cewa duniya na sauyawa cikin hanzari, yana mai cewar, “abin da ake ganin babu kamarsa a jiya, za a wayi gari ya zama ba komai ba. Fasahar sadarwa ta zamani na ci gaba da sauya alkibilar da duniya ke fuskanta.. don haka wannan taron ya samar da wani muhimmin sarari gare mu da za mu yi waiwayen ayyukanmu ciki da waje da nufin yin gyarar fuskar da ta kamata matukar muna son kasancewa cikin wadanda ake damawa da su a duniya.”

Shugaban na NIS ya ce da gyarar fuskar da za a yi ne za a auna tare da tabbatar da an samu nasarar abin da aka umurci ministan cikin gida ya yi a sashen tsaro, tattalin arziki da kuma rikon amana da gaskiya da wannan gwamnatin ta sanya a gaba.

Ya ce babban taron zai fi mayar da hankali a sassan aikin fasfo, dabarun kula da kan iyakokin kasa, sauya fasalin biza da gudanar da sauran ayyuka.

Babandede ya kuma bayyana cewa an samu ci gaba a kokarin yi wa sha’anin fasfo gyarar fuska tun daga lokacin da aka yi Taron Koli na Shugaban NIS na shekarar 2017 a Abekuta, inda aka inganta tsarin fasfon.

Ya kara da cewa, “bayan an bi matakan da suka dace, shugaban kasa ya amince da sabon fasfon da aka inganta kuma aka kaddamar da shi a zauren majalisar zartarwa a hukumance a ranar 15 ga Janairun wannan shekarar. Sannu a hankali sabon fasfon zai maye gurbin tsohon da ake da shi, an cimma nasarar hakan ma a shalkwatarmu da ofishinmu na Ikoyi. Mun kuma kimtsa tsaf mu yi hakan a Kano nan da makwanni biyu masu zuwa. Mun samu nasarar inganta fallayen takardun fasfon, fadada matakansa, bullo da fasfo da zai yi aiki na tsawon shekara 10 da kuma wasu abubuwa na tsaro masu yawan gaske.’’

Sai dai kuma, Muhammad Babandede ya nemi taimakon ministan na cikin gida wajen magance matsalar karancin takardun fasfon wanda ya ce matukar ba a shawo kai ba, duk irin matakan gyarar da za a dauka na hana masu cin karensu ba babbaka a bayan fage, ba za su yi tasiri ba.

Shugaban hukumar ya tabbatar wa da ministan cewa a karshen taron za su samar da takardun bayanan matakan da za a bi wurin neman fasfo da za su dace da umurnin da ya bayar na cewa wajibi ne ayyukan hukumar su mayar da hankali a kan tsaro, tattalin arziki da kuma rikon gaskiya da amana.

Da ya juya kan batun matsalolin da ake fuskanta wajen tabbatar da tsaron kan-iyakokin kasa kuwa, Muhammad Babandede ya bayyana cewa matukar ba su mike haikan wajen kawo sauyi masu ma’ana ba, yana fargabar hukumar ta watsa wa gwamnati kasa a ido musamman ganin cewa ta amince da bukatar da suka gabatar mata ta shirin amfani da na’urorin zamani wurin kula da kan-iyakokin kasa. “Don haka ya zama tilas a samu sauyi kuma ba a wani dogon lokaci ba a yanzu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ana sa rai taron zai samar da kyakkyawan tsarin tafiyar da ayyukan kula da kan-iyakokin kasa da za su yi dai-dai da na matsayin kasashen da suka ci gaba a duniya kuma wadanda za su yi dai-dai da kudirin tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma gaskiya da rikon amana.

Wakazalika, ya ce duk da matsalolin da ake fuskanta a kan-iyakokin kasa, yana godiya ga shugaban kasa da ya amince da shirin kula da kan-iyakoki ta na’urorin zamani, yana mai cewar, “za a aiwatar da shirin cikin shekara biyu inda za a rika kula da kan-iyakokin kasa masu nisan kilomita 4,047 dare da rana. Shirin zai karade cibiyoyin kula da kan-iyakokin kasa 86, da suka kunshi manyan cibiyoyi 6, matsakaita 16 da kuma kanana 64. Za a sanya na’rorin daukar hotunan bidiyo masu inganci a hanyoyin da ake bi da kafa da sauran na’urorin aiki.”

Bugu da kari, Babandede ya bayyana cewa domin magance matsalar daukewar lantarki, za a sanya na’urorin samar da makamashin hasken rana ga daukacin cibiyoyin kula da kan-iyakokin kasan.

 Ta fuskar abin da ya shafi sake fasalin biza kuwa, Shugaban na NIS ya ce bisa la’akari da yadda kasashen waje da dama suka mayar da sha’anin bizarsu ya zama babbar hanyar samun kudin shiga, ya wajaba a tattauna sosai kan yadda za a yi kasuwancin bizar bisa matakansa, kamar bizar da ake bai wa kwararru, da masu yawon bude ido da kuma masu zuba jari.

Haka nan ya ce wajibi ne tsarin bayar da bizar ya kula sosai da abin da ya shafi tsaron kasa, da bunkasa tattalin arziki da kuma bayar da shi bisa gaskiya da rikon amana.

Babandede ya kara da cewa duk da cewa yanzu ba lokaci ne na kuranta kokarin da hukumar ke yi ba, amma kuma wajibi ne ya bayyana nasarorin da suka samu a tsarin bayar da biza ga baki lokacin da suka shigo cikin kasa.

“A lokacin da muka karbi ragamar shugabanci wasu kamfanonin hulda da jama’a ne ke nema wa baki bizar ta hanyar mika bukatarsu ga ofishin Shugaban NIS. Mun fara ne da sauya tsarin zuwa neman bizar ta adireshin imel, amma a yanzu abin ya inganta zuwa shafin intanet. Za a nema ta shafin intanet, a biya ta shafin sannan a amince ta shafin idan mutum ya cancanta. Tsarin bai wa baki biza lokacin da shuka shigo kasa na ‘yan kasuwa ne kawai ba na masu zuwa ziyara ko zama a cikin kasa ba.”

Babandede ya nemi mahalarta taron su yi amfani da ofisoshinsu wajen inganta ayyukan da suka shafi bayar da biza domin cimma kudirin aka sanya a gaba na tsaro da tattalin arziki da kuma gaskiya da rikon amana.

Har ila yau, a cikin jawabin nasa, Babandede ya tabo batutuwan da suka shafi ginin fasahar sadarwa ta zamani da ake yi a shalkwatar hukumar ta NIS wadda ya ce hukumar za ta rika gode wa Shugaba Muhammadu Buhari har abada, kana ya yi tsokaci a kan irin matsalolin da ake samu wurin gudanar da ayyuka a tsakanin jami’an hukumar, inda ya hori shugabannin su tabbatar da an samu sauyi. Kana ya ce a karshen taron za su samar da kundin bayanan da za su inganta ayyukansu na tsaron kan-iyakokin kasa, da bayar da takardun tafiye-tafiye, da biza, da izinin zama a kasa da kuma shige da fice baki a cikin kasa.

Exit mobile version