Babban Taronta A 26 Ga Fabarairu: Ko APC Za Ta Tsallake Siradi?

APC

Daga Sharfaddeen Sidi Umar,

A wannan lokacin da Jam’iyyar APC da ke mulkin kasa ta tsayar da ranar gudanar da babban taronta na kasa a bayyane yake yadda kallo ya koma kan jam’iyyar musamman ganin ko za ta samu galabar tsallake siradi bisa kalubale da shingayen da ke gabanta ba tare da samun tarnaki da rarrabuwar kawuna ba.

Jam’iyyar APC wadda ke kan wa’adin mulki a zango na biyu bayan nuna wa jam’iyyar PDP da ke mulkin kasa a wancan lokacin kofar fita daga Fadar Mulki a 2015, a mabambantan lokuta ta yi ta canza lokacin gudanar da babban taronta na kasa wanda zai bayar da damar zaben sababbin shugabannin jam’iyyar.

Daga karshe dai Shugaban Rikon Kwarya na Jam’iyyar APC, Mai Mala- Buni wanda shi ne Gwamnan Jihar Yobe ya bayyana ranar 26 ga Fabrairu a matsayin ranar da jam’iyyar za ta zabi sababbin shugabannin da za su yi mata jagora a Babban Zaben 2023 wanda guguwarsa ta fara kadawa a sararin samaniya. Buni ya bayyana hakan ne a wajen taron mata na kasa na Jam’iyyar APC a Abuja a ranar Talata.

Bayan kasancewarsa sharar fagen babban zaben 2023, zaben shugabannin muhimmi ne ga jam’iyyar wanda zai tabbatar da makomar ‘yan takarar da ke muradin samun tikitin APC a takarar Shugabancin Kasa, ciki kuwa har da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da jagoran APC, Bola Tinubu da sauransu da dama da ke fatan hawa kujerar da Shugaba Buhari yake kai.

A yanzu haka Jam’iyyar wadda ta fitar da jadawalin sayar da fom din takara, ta shata ranar 14 ga Fabarairu a matsayin ranar da za ta fara sayar da fom, yayin da ranar 20 ga watan mai kamawa za ta kasance ranar tantance ‘yan takara. Tun da farko dai jam’iyyar APC ta fada a rikicin shugabanci a yayin da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka kori Komred Adams Oshiomole daga jan ragamar jam’iyyar wanda ya fara jan zarenta a 2018 tare da kai jam’iyyar ga nasara a zaben 2019.

Hayagagar Oshiomole ta faro daga dakatar da shi a jam’iyyar daga mazabarsa a Edo, gurfanar da shi a gaban kotuna daban[1]daban wadanda suka dakatar da shi, juya masa baya da na hannun daman Shugaba Buhari suka yi ta yadda daga karshe a ranar 16 ga Yuni 2020 Kwamitin Koli na jam’iyyar a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ya rushe shugabannin zartarwar jam’iyyar wanda hakan ya kawo karshen shugabancin tsohon Gwamnan na Edo.

Jam’iyyar APC wadda tun a watan Yuni 2020 take a hannun Mai Mala Buni a shuganacin rikon kwarya tare da alhakin shirya babban taro, ta kasa gudanar da taron duk kuwa da shata yin hakan a lokuta da dama wanda a kan hakan ‘ya’yan jam’iyyar da dama suka shigar da kara kotu domin haramta wa Buni ci gaba da rikon jam’iyyar, lamarin da a yanzu haka yake a gaban kotu bayan kwamitinsa mai mutum 13 ya kwashe watanni 19 a Shugabancin Jam’iyyar.

LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewar tun a Oktoba ne jam’iyyar APC ta gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu, Jihohi da Kananan Hukumomi wanda aka gudanar ba tare da wani tarnaki ba a wasu jihohin, yayin da kuma aka samu rarrabuwar shugabancin jam’iyyar da assasa rassan bangaranci a wasu Jihohin.

A siyasance kasa dinke baraka da gudanar da amintaccen zaben shugabancin jam’iyyar a matakin Jihohi zai shafi gudanar da babban taron jam’iyyar a matakin kasa wanda hakan ba karamar illa ba ne ga ci gaba da dorewar jam’iyyar saboda zai kara karfafa wa jam’iyyun adawa musamman PDP da ta sha alwashin kawo karshen mulkin da ta kira na kama-karyar APC. A Jihohi 13 kama daga Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Kano, Ekiti, Oyo, Kuros- Riba, Abia, Delta, Ribas, Kwara, Osun da Ogun jam’iyyar ta dare gida biyu ta hanyar bayyanar shugabanni biyu da hedikwatar jam’iyya biyu wanda ya zama silar gurfana a kotuna daban-daban domin warware gardamar zabukan. A wasu Jihohin bangarorin jam’iyyar suna a karkashin jagorancin Ministocin Buhari kamar a Ribas, Kwara da Bauchi, a yayin da wasu Jihohin bangarorin ke karkashin jagorancin tsofaffin Gwamnoni a wasu Jihohin kuwa a karkashin jagorancin Sanatoci kamar a Sakkwato da Kebbi

A bisa ga wannan rikita- rikitar shugabancin da ta dabaibaye jam’iyyar a iya cewa ta-na -kasa[1]ta-na-dabo a babban zaben na watan gobe, domin kuwa dukkanin bangarorin da ke ikirarin shugabancin jam’iyyar za su bayyana wajen zabe da jerin mutanen su domin kada kuri’a.

Kallo zai kasance ga bangaren da zai samu damar shiga zabe, haka ma bangaren da duk aka haramta wa zaben za su ja daga ta yadda yana iya yiyuwa su kasance ‘yan adawar cikin gida da ke iya haifar da illa ta hanyar zagon kasa. Haka ma bangarorin da ba su samu nasara ba, na iya ballewa zuwa jam’iyyar PDP tare da taimaka mata ga lashe zabe wanda hakan babban tarnaki ne ga APC

A haka, babban kalubalen da ke a gaban jam’iyyar shi ne tsayar shugabanni nagari wadanda suka san ciki da wajen siyasa, wadanda ke iya rungumar kowa a tafi tare, cikin sanin makamar shugabanci, lakantar hanyoyin neman jama’a, hakuri, jajircewa da kokarin daukar kwaram da kwaramniyar siyasa.

Idan har APC wadda ta kwace mulki a hannun PDP bayan kwashe shekaru 14 saman madafun iko ta kasa zaben shugabannin da za su jagoranci hada kan Jam’iyyar, dinke barakar da ke akwai har ta kasa zaben shugabannin da za su kai ta a tudun- mun tsira, to hakan karara zai bai wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP damar mayar da mulki a hannunta musamman bayan samun nasarar gudanar da nata babban taron da ya samar da Sanata Iyorchia Ayu cikin nasara ba tare da baraka ba kamar yadda aka yi tsammani tun da farko.

LEADERSHIP HAUSA ta kalto cewar a watan Yuni 2020 ne Shugaba Buhari ya kaddamar da shugabancin rikon kwarya na APC wanda aka dora wa alhakin gudanar da babban taronta na kasa a watan Disambar wannan shekara. Sai dai a yayin da lokacin ya cika na watanni shida ba tare da samun nasarar gudanar da taron ba, an sake kara wa’adin kwamitin rikon kwarya na Buni zuwa wasu watanni shida a Yunin 2021.

Haka ma a yayin da lokacin ya cika a karo na biyu, an sake kara wa’adin kwamitin a karo na uku zuwa Disambar 2021 wanda a lokacin ma, Gwamnan na Yobe ya kasa gudanar da babban taron tare da dagawa zuwa Fabrairu, watan da mai girma zai dauki girmansa a shugabancin jam’iyyar. A yau duk da cewar aski ya riga ya zo gaban goshi amma Jam’iyyar APC ba ta bayyana yadda tsarin shugabancin jam’iyyar zai kasance ba wato yankunan da ‘Yan Majalisar Zartarwar Jam’iyyar za su fito ba.

A yayin da ake hasashen sabon Shugaban jam’iyyar zai fito daga yankin Arewa- Maso- Yamma, yana iya yiyuwa jam’iyyar ta bayar da mukamin shugaban jam’iyyar ga Arewa-Ta- Tsakiya wanda hakan zai canza lissafin zaben.

A yanzu haka dai jigogin APC 11 ne suka ayyana aniyarsu ta darewa saman shugabancin jam’iyyar duk da cewar ba a kai karshen yankin da zai yi takara ba. Wadanda suka nuna sha’awar takarar sune; tsofaffin Gwamnonin Nasarawa, Zamfara, Bauchi, Borno da Gombe wato Tanko Al-Makura, Abdul’aziz Yari, Isa Yuguda, Ali Modu Sheriff, Kashim Shettima da Danjuma Goje. Sauran sun hada da; Ministan Lamurran Musamman, George Akume, tsohon Mataimakin shugaban rusasshiyar jam’iyyar CPC, Salihu Mustapha da Muhammad Sa’idu -Etsu da Silbester Moniedafe da Sanata Sani Musa. Sai dai a bisa ga al’adar APC ta zaben tsofaffin Gwamnoni a Shugabancin Jam’iyyar zai yi wahala wanda ba tsohon Gwamna ba ya samu shugabancin jam’iyyar.

Haka ma dukkanin tsofaffin Gwamnonin da suka fito takarar suna fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa da karkatar da kudaden al’umma daga Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci wanda hakan babban kalubale ne ke fuskantar jam’iyyar da ke ikirarin canji da yaki da cin hanci idan ta damka wa daya daga cikin tsofaffin Gwamnoni jan ragama da akalar jam’iyyar.

Ajiye aiki a matsayin Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin APC da Salihu Lukman ya yi a farkon makon nan kan batun babban taron jam’iyyar da tsayuwarsa kan lallai bai kamata Kwamitin Buni ya wuce watan gobe ba kamar yadda shi kansa Shugaba Buhari ya jaddada da ayyana aniyar takara da Tinubu ya yi da nuna alamun takara da Osinbajo ya yi, ‘yar manuniya ce da ke nuna za ta tafasa ta kone a zaben.

Kundin masu zabe da ya fara shiga hannun kafafen yada labarai ya nuna ‘yan jam’iyyar APC, 4509 ne za a tantance domin kada kuri’a a zaben ta yadda yankin Arewa Maso Yamma yake da kaso mafi yawa na wakilai masu zabe 1059 sai yankin Kudu-Maso-Kudu da ke da 959 a yayin da Kudu- Maso- Yamma ke da wakilai 897, sai Arewa ta Tsakiya da ke da 714, Arewa- Maso-Gabas tana da wakilai 562 sai kuma Kudu Maso[1]Gabas 560.

Ya zuwa yanzu, al’ummar kasa da musamman ‘yan jam’iyyar APC, da babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun sa ido domin ganin yadda babban taron APC zai gudana, shin za a gudanar da zaben cikin nasara ko kuwa za a samu hayaniya da rarrabuwar kawuna? Lokaci kadai zai nuna.

…Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Jam’iyyar Da Tauraruwarsu Ke Haskawa

| Daga Yusuf Shuaibu,

Gabanin ranar 26 ga watan Fabrairu da jam’iyyar mai mulki za ta gudanar da babban taronta wanda zai ba ta damar samun sabon shugaba, akwai manyan ‘yan takara guda hudu da tauraruwarsu ke haskawa wajen neman shugabancin jam’iyyar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni jam’iyyar suna lalubo hanyar da za su zabi daya daga cikin wadannan manyan ‘yan takara domin samun sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa. Manyan ‘yan takaran guda hudu sun hada da tsofaffin gwamnonin Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura da Sanata Abdullahi Adamu da tsohon mataimakin rusasshiyar jam’iyyar CPC, Saliu Mustapha da kuma tsohon ministan ma’adanai da bunkasa karafa, Abubakar Bawa Bwari.

Sanata Abdullahi Adamu shi ne shugaban kwamitin sulhu na jam’iyyar APC, yayin da Bwari ya kasance ministan Buhari a farkon wa’adin mulkinsa, ana tunanin zai fi nuna sha’awarsa a tsakaninsu.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa na la’akari cewa su suka fi cancanta da su gaji shugaban kwamitin riko kuma gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni. Ana tunanin jam’iyyar ta bai wa bangaren Arewa ta tsakiwa wannan takara wanda har ta fitar da ‘yan takara guda hudu da suka fito daga wannan yankin.

Majiya da ke kusa da fadar shugaban kasa ta bayyana cewa alamu na nuna cewa shugaban kasa yana goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Al-Makura. “Yana da wahalar gaske a iya sanin abin da ke cikin zuciyar shugaban kasa, amma dai alamu sun nuna cewa yana goyon bayan Al-Makura wanda ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar CPC,” in ji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa Al-Makura ya samu goyon bayan wanda ya gaji shi a matsayin gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da sauran abokanansa na zama shugaban jam’iyyar APC. “Gwamna Sule ya bukaci mafi yawancin abokanansa da su zabi dan takaransa.

Ya dai fara yi masa yakin neman zabi ne tun da dadewa kafin sauran ‘yan takaran su nuna sha’awarsu na neman shugabancin jam’iyyar,” in ji wani dan majalisa. Sai dai kuma wasu gwamnoni suna goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu. Tsohon gwamnan Jihar Nasarawa wanda shi ne shugaban kwamitin jam’iyyar ya nuna sha’awarsa na tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.

Amma wasu bangare na jam’iyyar na goyon bayan Saliu Mustapha, wanda shi dan asalin Jihar Kwara ne da ya zama shugaban jam’iyyar. A cewar magoya bayan Mustapha, babu wani mutum da ya kai shi cancanta. Wasu kuma suna tare da Abubakar Bawa Bwari, dan asalin Jihar Neja kuma tsohon ministan Buhari a wa’adin mulkinsa na farko wanda a cikin dare daya kwai ya fito neman wannan shugabancin jam’iyyar.

Sauran wadanda suke neman kujeran sun hada da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda da ministan ayyuka na musamma, Sanata George Akume da Sanata Mohammed Sani Musa da Sunny Moniedafe da kuma Mohammed Saidu Etsu.

Exit mobile version