Kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya soki lamirin kalaman aware na jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te, yana mai zargin Lai din da yaudarar al’ummar Taiwan, da karkatar da tunanin sassan kasa da kasa.
Chen Binhua, ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga kalaman da aka jiyo Lai na yi, yayin zantawa da wata kafar watsa labarai ta Amurka. Chen, ya ce tun kama aikin Lai a matsayin jagoran yankin Taiwan sama da shekara guda, ya rika furta kalamai irin na ‘yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan, tare da ingiza fito-na-fito da rashin jituwa tsakanin Taiwan da babban yankin Sin.
A lokaci guda, Lai ya rika aikata wasu matakan rashin gaskiya masu nufin mika Taiwan ga wasu sassan ketare, lamarin da ya yi matukar gurgunta moriyar kamfanoni da jama’ar yankin na Taiwan, da jefa tattalin arziki da ci gaban Taiwan cikin mummunan hatsari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)