Dan majalisar wakilai, mai wakiltar kananan hukumomin Toungo, Jada, Mayo-Belwa da Ganye a majalisar wakilai ta kasa AbdulRazak Namdas, ya bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar gwamna a babban zaben 2023 da ke tafe.
Wannan dai shi ne karo na biyu, da’ake zabin AbdulRazak Namdas, a matsayin dan majaiisa mai wakiltar kananan hukumomin hudu dake arewacin jihar Adamawa a matsayin wakili, ya ce yanakan tuntubar masu ruwa da tsaki domin daukan matakan da ya dace.
Namdas, ya bayyana hakan ne a wani ganawar da yayi da ‘yan jaridu lokacin bukin cika shekaru 52, ranar juma’ar da ta gabata, ya ce ya cancanci tsayawa takarar, ganin ya taba neman kujerar shekaru 10 da su ka gabata.
Ya ce “a shekarar 2011, na tsaya takara a matsayin mataimakin ga Injiniya Markus Gundiri, munyi sai da aka kammala zaben.
Da shima ke magana a taron mataimakin shugaban riko na jam’iyyar APC a arewa maso gabas Farfesa Mamman Tahir, ya godiwa Allah ya baiwa Namdas daman ganin shekaru 52, ya kuma yi fatan Allah ya bashi daman ganin wasu shekarun.
Ya kuma bada tabbacin jamiyyar zata bada dama ga duk yayanta da ke bukatar neman kowace kujera, ba tare da katsalanda ko wani sharadi da yarjeneniya ba.
Haka shima shugaban rikon jam’iyyar APC ta jihar Ibrahim Bilal, ya yaba da rawar da Namdas ke takawa, da irin gudumuwar da yake baiwa jam’iyyar a jihar, ya ce Namdas ya nuna cikakken dan dimokradiyya ne na kasa baki daya.