Kafar yada labarai ta AP, ta ba da labari kwanan baya cewa, karin yawan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 ta karu matuka kafin bikin cika-ciki ko “Thanksgiving.
Babbar likitar yaki da COVID-19 a fadar White House Deborah Burks, ta yi gargadi ga Amurkawa cewa, kamata ya yi su kayyade taruwa yayin bikin, amma Amurkawa ba su amince da wannan shawara ba, ciki hadda ita kanta dakta Burks.
Bayan wannan biki, Burks ta halarci wani bikin aure a jihar Delaware, kuma iyalai biyu masu zuriyoyi uku sun rufa mata baya a bikin.
Cibiyar CDC ta Amurka ta nemi Amurkawa da kada su kai ziyara yayin bukukuwa, kuma ta hana yin taru tsakanin iyalai daban-daban a cikin gida daya. Amma ziyarar Burks ta sabawa shawarar cibiyar CDC.
Abokan aikinta a fannin kiwon lafiya suna ganin cewa, kamata ya yi ta bi ka’ida mafi tsanani, lura da taimako mafi muhimmanci da ta baiwa gwamnatin kasar, wajen yakar cutar, da hana yawan yaduwar ta a kasar. (Amina Xu)