Babbar Sallah: Gawuna Ya Bukaci A Tsananta Addu’ar Fatan Ganin Karshen Annobar Korona

Gawuna

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya taya al’ummar Musulmi murna zagayowar Babbar Sallah, ya kara bayyana muhimmancin wannan rana tare da bukatar kara Jajircewa da rokon Allah. Kamar yadda Daraktan yada labaransa Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.

Daga nan sai ya bukaci al’ummar Musulmi da su rungumi kyawawan koyarwar ma’aiki ta hanyar kara jajircewa, sadaukar da kai, gaskiya da tausayawa kamar yadda ya koyar.

Kamar yadda muke murnar zagayowar Babbar Sallah, “Ina rokon al’ummar Musulmi da su kara himmatuwa wajen addu’ar ganin karshen annobar Korona. Haka kuma ya kara da cewa a kiyaye matakan kariya daga annobar Korona a lokutan bukukuwan Sallah ta fuskar daukar matakan kariya domin dakile yaduwar wannan mummunar annoba,” in ji shi.
Haka kuma Gawuna ya tabbatar wa da al’umma cewar Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kara jajircewa domin ciyar da Jihar zuwa Mataki na gaba.
Haka kuma ya jadadda bukatar al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen yi wa kasa addu’o’i domin samun damar magance matsalolin da suka dabaibaye ta.

Exit mobile version