Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule tayi kira ga iyayen yara dasu rika bayyana matsalolin da ya shafi ya’yan su masamman wadanda akayiwa Fyade ko cin zarafin.
Hajiya Silifat ta ce ba alheri ba ne a zalunce yara aci zarafin su sannan iyayensu su boye saboda gudun tozarci. Ya zamo ke nan an daurewa wadanda ke aikata irin wannan gindi .
Amma duk lokacin da aka yiwa wata yarin ya fyade iyayen ta su fito su bayyanawa Duniya Gwamnati zata dauki dukkan matakin da ya dace.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana hakane a lokacin da ta halarci taron gamgamin wayar da kan iyaye mata kan ire-iren wannan wanda tashar NTA ta shirya a garin Lafia.
Ta kuma yi kira ga iyaye da su rika tura yaran su makaranta kada su dogara da tallace tallace domin babu abin da zai haifar a garesu, Ilumi shine gin shikin cigaban kowata al’umma.
Uwargidan Gwamnan tayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu kyamaci harkan fyade da cin zarafin mata.
Shima a nasa jawabin Shugaban gidan Talabijin na NTA Malam Hamza Makarfi yayi godiya ga Uwargidan Gwamnan saboda yadda ta rungumi yaki da masu aikata mummunar aikin fyade da cin zarafin.
Malam Hamza Makarfi ya ce gidan Talabijin ta shirya wannan gangamin ne saboda al’umma su kyamaci irin wannan mummunar aiki.
Ya ce cin zarafin ba alheri bane a rayuwar kowa ta al’umma saboda yana da kushe rayuwa da maida komai baya. Da lalata yara kanana.
Malam Hamza Makarfi ya yabawa Hajiya Silifata Abdullah Sule saboda yadda take taimakawa marasa galihu take samarwa mata da matasa ayyukan yi domin dogaro da kai.
Hamza Makarfi ya yabawa Gwamna Abdullah Sule saboda yadda yake tafiyar da Gwamnati domin cigaban jihar Nasarawa.