Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdulkadir Mohammed, ya sanya kafa ya shure jita-jitar da ke bazuwa a farfajiyar garin na Bauchi da ke cewa akwai rashin jituwa a tsakaninsa da wani jigo ta fuskar tallafa wa al’ummar Bauchi, wato Alhaji Bala Wunti.
Gwamnan yana mai cewa ma, ba kawai ga Alhaji Wunti ba, shi bai da wata matsala da wani dan asalin jihar Bauchi da ke aikin taimakon al’umma a kowani yanki ya ke, don haka ne ya nuna batun a matsayin jita-jita marar kan gado.
Ya na kuma kara wa ma da cewa, shi fa gwamnatinsa a kowani lokaci tana matukar goyon baya da mara wa dukkanin aiyukan taimakon al’umma da jin kansu wanda ke zuwa daga da ko ‘yar jihar Bauchi da suke da zimmar taimaka wa al’umma a ciki da wajen jihar, ya ce babu dalilin da zai sanya ya kyamaci masu irin wannan aikin da jama’a ke mora.
Gwamnan yana mai jawabi ne a lokacin da ya amshi bakwancin tawagar iyalan Shaikh Dahiru Usman Bauchi da suka kai masa ziyarar barka da Sallah a gidan gwamnatin Bauchi.
Gwamnan ya sha alwashin bada tasa gudunmawar ga aikin kwaskwarima wa masallacin Sheikh Dahiru Bauchi da shi Alhaji Bala Wunti ke yi Fisabilillah.
Daga nan sai ya gode wa shugaban addinin Sheikh Dahiru Bauchi a bisa goyon baya da ya ke baiwa gwamnatinsa na addu’o’in samun nasara a kowani lokaci, sai ya sake rokon karin addu’o’in.
“Ni babu wani rashin jituwa a tsakani na da Bala Wunti kamar yadda ake ta yada farfaganda kan aikin gyaran masallacin Shaikh Dahiru Usman Bauchi wanda shi Wunti din ke yi. A hukumance Bala Wunti ya sanar da ni kan wannan aikin har ma na jinjina masa bisa hakan.
“Bala Wunti yana daga cikin irin mutane da muke bukatar su wanzu a jihar mu, ina mai cikakken mara baya wa aiyukan da yake gudanar mana a jihar Bauchi.
“Don Allah ku isar da sakon godiya da yabo ga Shaikh Dahiru domin ya min alkairai da daman gaske,” a cewar Gwamna Bala Muhammad.
Tawagar wacce ta zo a karkashin Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, sun yi amfani da damar wajen yin addu’a ta musamman wa gwamnatin Bala Muhammad.
Wakilinmu ya labarto cewa ana yawan yada batun rashin fahimta da jituwa a tsakanin Bala Muhammad da Bala Wunti, shi dai Bala Wunti ma’aikaci ne a hukumar NNPC wanda ya shahara wajen aiwatar da aiyukan jin kai da taimaka wa jama’a a Bauchi, a bisa irin aiyukan da wasu suka ga yana yi sai aka fara jita-jitan wai yana neman takarar gwamnan jihar Bauchi ne.
Lamarin da wasu kuma suka dauka suka daura da cewar ma akwai rashin fahimta ko jituwa a tsakaninsa da gwamnan jihar wato Bala Muhamamd a shi kuma ya karyata hakan.
Garban Kauye Farawa Ne Allurar Dinke Barakar Kumbotso – Muslihu Yusuf Ali
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana zaben Sabon shugaban Karamar...