Connect with us

LABARAI

‘Babu Barkewar Kwalara A Jihar Borno’

Published

on

Ranar Talata ce gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa, babu wani al’amrin dake da alaka da barkewar kwalara a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Haruna Mshelia wanda ya kira taron ‘yan jarida dangane da al’amarin, ya bayyana cewa, duk an dauki matakan da suka kamata domin tabbatar da babu wani abu a kan barkewar cutar.
Ya bayyana cewa, an samu rasuwar mutum 61 a shekarar 2017 a jihar saboda al’amarin daya shafi kwalara, ya kuma nuna jin dadinsa saboda ba wani bayanin daya danganci barkewar cutar a wannan shekara wadda muke ciki.
Ya kara bayanin an samu wata matsala mai dangantaka da zawo mai ruwa, abinda ya shafi mutum1068 a kananan hukumomi goma na jihar, tun da aka fara ruwan sama cikin watan Mayu na wannan shekara, zuwa yanzu abin bai samu baci ba wanda har ya kai ga kwalara.
Ya ci gaba da bayanin “Kamar wannan lokaci ko wacce shekara muna samun matsalar zawo mai ruwa, wanda kwayar cutar Bacteria ce sanadin hakan ta hanyar kashin da ake yi a fili, ana samun haka sosai a kauyuka saboda yadda akee yin kashi a fili.”
Bugu da kari kamar yadda ya kara jaddadawa cin abincin da baya da yau ga kuma shan ruwan da ba shi da tsafta, (ba tare da an tafasa shi ba) shi ma yana zama sanadiyar kamuwa da cutar kwalara.
Ya ce, “Ko wanne lokaci a shirye muke a kan wannan al’amari, saboda mun ba jami’anmu horo wadanda za su iya kai agaji, akwai wata tawaga ta musamman wadda aka kafa saboda irin hakan. Muna dasu a bangaren kananan hukumomi da kuma jiha, wadanda suke jihar sun fi na kananan hukumomi sanin makamar aikin sosai.” Inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: