Connect with us

RAHOTANNI

Babu Ci Gaban Da Ya Kamata A Shekaru 21 Na Damokwaradiyyar kasar Nan -Husaini Mairiga

Published

on

An bayyana tsawon shekaru 21 da aka shafe da komowar kasar nan tsarin Damokwaradiyya ba tare da yankewa ba da cewa babu wani takamaiman ci gaba da aka samu ta fuskar ci gaban al’umma a fannoni da dama.

Wani Jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Husaini Isah Mairiga ne ya bayyana hakan da yake bayani dangane da tsarin Damokwaradiyya a kasar nan, cikin zantawars da wakilinmu a makon da ya gabata.

Husaini Mairiga, wanda ya taba zama Shugaban bangaren APC mai jama’a na jihar Kano, ya yi nuni da cewa a yanzu siyasar da ake yi ba ta akida da zabin jama’a ba ce, musamman idan aka kwatanta da irin siyasar da aka yi a baya na jamhuriyya ta farko da wadanda suka biyo bayanta kafin wannan.

Ya ce siyasun na baya sun doru ne akan akida da zabin al’umma da son ci gaban kasa da na al’ummarta, amma sai dai abin takaicin shi ne a wancan lokacin da an soma tafiya sai sojoji su kawo nakasu na yin juyin mulki.

Alhaji Husaini Isah Mairiga, wanda dan siyasa ne na jiya da yau ya yi, wanda ya yi siyasa a lokutan baya da ake da jam’iyyu masu manufa, wanda al’umma ne suke haduwa su kafasu, ya ce lokacin baya jam’iyya ce ta ke sama da mai mulki, kuma dan takara duk wanda ya cancanta kuma al’umma suka zabe shi ya yi takara, shi ne zai shiga zabe.

Amma ya ce yanzu a wannan tsari da ake ciki an gindaya sharuddan da sai mai takardu na ilimin boko mai zurfi shi ne zai nemi shugabanci, komin kwarewar mutumin da bai yi karatun zamani mai zurfi ba, komin cancantarsa, ba zai tsaya takara ba.

Sannan kuma sai mutum yana da kudi zai iya takara, haka kuma Gwamnoni da sauran masu mulki, yanzu su ne a gaba da jam’iyya, su ke bada umurni, ba ra’ayin al’umma ba, shi ya sa ake samun koma-baya.

Ya kara da nuni da cewa, yawan jam’iyyun siyasa da gwamnati ta ke kafawa su ma ba su da wani muhimmanci ga Dimokwaradiyya domin yawancinsu ana yinsu ne domin amfana da kudade da gwamnati ke ba su don gudanarwa.

Alhaji Husaini Isah ya ce a wannan dogon lokaci na dorewar Dimokwaradiyya da aka samu na shekaru 21 bada yankewa ba, shi ne kadai za a iya tutiya da cewa an sami nasara, ta daukar tsawon lokaci ba tare da an sami katsalandan din masu Khaki ba na kawo cikas a tafiyar, amma a fannin ci gaban rayuwar al’umma, ba wata kyakkyawar nasara da aka samu, domin abubuwa sai dada tabarbarewa suke yi, musamman a fannin tsaro, ilimi, lafiya da harkokin kasuwanci, talauci na dada kaifi da sauran fannoni, hatta a siyasar ma an koma ana tsarin in baka-ci -ba –ka ci, wanda yake dada jefa kasar a cikin koma-baya.

Alhaji Husaini ya ce, ba ci gaba a wannan kasar a halin da ake ciki na Dimokwaradiyya, a ce a kasafin kudi an ware wa fannin Ilimi N48b, Lafiya an ware N44b, amma Majalisar kasa an yi mata kasafin N125b. Wanda dukkan ‘yan Majalisun ba su wuce mutum 500 ba.

Alhaji Husaini Isa Mairiga ya ce,yana ganin za a iya samun gyara don ci gaban Dimokaradiyya a kasar nan idan har za a kula a dauki matakai da suka hada da rage yawan jam’iyyu. Gwamnati ta cire hannu a siyasa a bar ta ga zabin al’umna. A gyara tsarin mulki, duk mai mulki da ke kan wata kujera ta siyasa ya sauka idan ya sauya jam’iyya.

Sannan Gwamnati ta cire tsarin nan na sai wanda ke da takardun boko ne zai yi takara, a bar duk wanda ya cancanta ya yi takara, daga kan shugabancin karamar Hukuma zuwa Majalisar jiha bisa cancanta, ba tare da gindaya sharuddan takardu ba, in ya so a matakin Majalisun tarayya da Sanata a iya neman takardu, su ma saboda cudanya da ake da sauran sassa na kasa da na duniya. Sannan a tabbatar da ana zabe na gaskiya, abin da jama’a ke zaba shi ake ba su, wannan ne zai bunkasa ci gaban Dimokaradiyya a kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: