Khalid Idris Doya">

Babu Dan Arewa Ko Kudu Mai Gwagwarmaya Don Yankinsa Illa Don Muradun Kai – Sanusi

Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi mai murabus, ya shaida cewar, masu tutiyar buga-bugar kare muradu da kimar yankunansu a fadin Nijeriya, ba don yankunansu su ke yi ba, illa don ciyar da aljihunansu da iyalansu gaba kawai.

Sarki Sanusi, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne, ya na wannan jawabin ne a yayin taron shekara-shekara da kungiyar Kiristoci ta ‘Covenant Christian Centre’ ta shirya a Jihar Legas ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Babban taron, Poju Oyemade ne ya shirya shi domin raya bikin cikar Nijeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka.

Advertisements

Nijeriya dai ta fuskanci kalubalen rikice-rikicen addini da na kabilanci, wanda har hakan ya sanya kalibu da dama ki kiran a zabi nasu a lokuta da daman gaske.

A lokacin da a ka tambayi tsohon sarkin shin ta yaya za a daidaito da lamuran nan a samu habaar zaman lafiya da kwanciyar hankali, Sanusi ya shaida cewa, dole ne ’yan Nijeriya su aminta kan cewa masu rike da mukaman siyasa su kasance ’yan kasa masu nagarta da za su kasance jakadu na kwarai ga addininsu ko kabilarsu da su ka yi imani da su, amma ba tare da nuna bambanci ba.

Ya ce, masu tutuyar wai su na kare muradun yankin arewaci, kudanci ko gabashi kan mukaman siyasa, ba haka ba ne, sun fi karkata kan cika aljihunansu da dukiya a maimakon tunawa da yankunan da su ka fito da su ke tutuyar kiyaye mu su muradun.

A cewarshi, “rikicin kabilanci da na addini bai da wani yawa daga ’yan Nijeriya, shugabanin kasar ke kambamawa. Mu na da shaidun da ke nuni da cewa shugabanin kasar ne ke kashe-mu-raba da dukiyar kasar.

“Ba na tsammanin mutane da su ka ce su na fada don Hausa, Igbo ko Yoruba da gaske wannan ne muradunsu na zahiri. Ina nufin da zarar su ka yi ta kumfar bakin kare kimar yankunansu ko kabilarsu, da zarar su ka kale kan kara sai a karshe zancen ya kare kawai su da iyalansu.

“Babu wani mutum daya tak daga cikinsu na hakika da ke wakiltar Arewa, Kudu ko Gabas. Su na dai tutiyar hakan, idan kun duba cikin mukarraban. A tarihin Nijeriya, babu wata gwamnati da ta zo ba tare da tafiya da kowane yanki na kasar nan ba.

“Abu na farko da za a fahimta shi ne, dole ne a cire jin cewa rike mukaman siyasa ne ke sanya mutum ya wakilci al’umma,” in ji shi.

Don haka ne ma ya nemi a daina wani nuna banbanci yanki kawai idan za a nemi mukamin siyasa yana mai cewa masu ma yin hakan fa wa kawukansu kawai suke yi don cimma muradunsu na kashin kai ba wai na yankunan da su ka fito ba.

A gefe daya tsohon sarkin ya jinjina tare da yaba wa gwamnatin tarayya a bisa cire tallafin mai da ta yi a kwanakin baya. A cewarshi, matakin da gwamnatin ta dauka zai taimaka matuka gaya wajen janyo sakamako mai kyau ga kasar, amma ya kara da cewa, akwai kalubale kan gwamnati na tabbatar da cewa, ba a cigaba da karkatar da dukiyar da a ka samar daga janye tallafin mai ba, domin talakan kasar ya samu cin moriyar hakan kuma ya fahimci sahihancin cire tallafin a nan gaba.

Exit mobile version