Hukumar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta karyata rahotannin da ake ta yadawa cewa, an sami wani jami’in dan sanda ya kashe kansa, saboda an yi masa canjin wurin aiki daga Abakaliki zuwa garin Maiduguri.
A cewar hukumar Sajen Donatus Oyibe, bai kashe kansa ba don samun canjin wurin aiki da rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, ta yi masa.
Oyibe dan asalin karamar hukumar Ebonyi ne ta jihar, ana ta dai yada rahotanni cewa dan sandan ya tinjima cikin rijiya a daren Lahadi, bayan ya je da nufin debo ruwa.
Jami’in hulda na ‘yan sandan jihar ASP. Loveth Odah yace, Donatus na daga cikin rukunin ‘yan sandan Mobal da aka tura Maiduguri kwanan nan kuma yana cikin hazikan ‘yan sandan jihar.
Odah ya kara da cewa, sun sami rahoto daga ‘yar sa mai suna Ukamaka, inda ta shaida cewa, mahaifin ta ya dauki bokiti ya ce zai debo ruwa a rijiya. Daga nan har bayan tsawon lokaci aka ji shiru.
A yanzu haka dai hukumar ‘yan sandan ta tabbatar da mutuwar dan sandan, yayin da aka tsamo gawar sa.