Babu Gwamnan Kaduna Da Ya Yi Gyaran Da el-Rufai Ke Yi – Maikano

Gwamnan Kaduna

Daga Abubakar Abba,

Sanannen dan jarida kuma haifaffen Jihar Kaduna kuma tsohon shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni (SWAN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Abudullahi Maikano Usman, yayi nuni da cewa, ayyukan da Gwamnan jihar Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya ke yi a halin yanzu, gaskiyar magana gyaran ne da ba a taba yin sa a Kaduna ba kuma ko da an taba kamantawa, to sai dai can baya zamanin Marigayi Firimiyan Arewa Sardauna Sir Ahmadu Bello.

A hirarsa da LEADERSHIP A YAU a Kaduna ya ci gaba da cewa, tun daga lokacin Sardauna, babu wani gwamna na jihar Kaduna wanda ya yi gyaran da Gwamna el-rufai ya ke yi a halin yanzu.

Mai Kano wanda ta taba rike mukamin shugaban hadaddiiyar kungiyar masu shirya finafinai ta kasa wato MOPPAN ya ci gaba da cewa, “Abinda ya sa na ce haka shi ne, na farko dai aiki ne a zahirance sannan kuma ana gudanar da shi tsakani da Allah babu tsoro kuma ba son zuciya”

“Abinda ya sa na fadi haka, shi ne gyaran ya taba babba ya taba karami, ya shafi talaka kuma ya tabo mai hannu da shuni, inda ya ce, wannan ya nuna cewa El-Rufai yana aiki ne domin ci Kaduna da daukacin al’umar jihar, to ka ga kuwa, el-rufai ba karamin namiji ba ne ba”.

Ya kara da cewa, jajirtaccen shugaba shine zai iya dauko aikin da babu wani da bai shafa ba kuma ka na ji ka na gani, za a yi wannan gyaran domin zai amfani daukacin jama’ar jihar.

Ya yi nuni da cewa, “Wani abu na yaba wa el-Rufai shi ne, na hangen nesa da ya ke yi, inda ya yi nuni da cewa, titunan da ake yi, nayi imani har ga Allah abinda na gani da ido na, musamman bangaren kwaltar da ake yi a Kaduna a yanzu, to gaskiyar magana, in dai ba wani abu na gangan ba, kwaltar da ake yi a jihar Kaduna sai dai Mahadi ka ture kuma aikin na kwalta, ba wai wanda za a yi gobe ko jibi a dawo ana yin face-face ba”.

Maikano ya yi nuni da cewa, ayyukan el-rufai na sake fasili da gyaran garin, ya dauko su daga shiyya ta daya zuwa shiyya ta biyu da ta uku da ke a jihar, inda ya kara da cewa, ka ga ba inda ba a taba ba, kuma wani abu shi ne, inda aka zabe shi da inda ba a zabe shi ba, kai har ma wanda ya fito ya ce, bai kaunar sa, shi el-rufai, ba ruwansa da wannan, aiki zai yi masa a matsayinsa na shugaba kuma zababben gwamna.

Ya cigaba da cewa, “Zan baka misali, babu wata mazaba a fadin Kaduna, misali bangaren kiwon lafiya wanda Malam bai taba ba, to ai ba a dukkan mazabun ya ci zabe ba, amma da inda ya ci zaben da inda bai ci ba, duk ya yi masu aiki, to ka ga wannan, shi ne shugaba, domin el-rufai, bai da riko, ba hassada da wani bai da bakin ciki da wani, da wanda ya yaba masa da wanda ya kushe shi, to duk ya dauke su a matsayin shi ne shugaba”.

Da aka tambaye shi kan ko ayyukan na gwamnatin jihar sun taimaka wajen rage zaman kashe wando, musamman a tsakanin matasan Jihar, Maikano ya ce, “Ni kaina na zanta da wasu yaran a wasu wurare, musamman a Sabon garin Zariya, wallahi akwai wanda ya gaya min cewa, duk shan shi, tufatarwarsa da dawainiyar iyalansa gaba daya, kusan Malam el-rufai ya dauke masa, dalilin ginin kasuwar Sabon garin Zariya, ya ce kuma ya na da yakinin ko an gama aikin el-rufai zai kara kirkiro da wasu ayyukan da matasan jihar za su ci gajiyar ayyukan”.

Da aka tambaye shi ko wanne kira zai yi ga wanda zai gaji el-rufai ko zai dora daga inda el-rufai ya tsaya, Maikano ya yi fatan duk wanda zai gaje el-rufai Allah ya bashi ikon dorawa daga inda ya tsaya, inda ya kara da cewa, to amma, duk wani gwamna da zai zo ya shugabanci Kaduna to gaskiyar magana, idan bai wuce abinda el-rufai ya yi ba, bai kuma kamanta ba abinda el-rufai ya yi ba, ina ganin sai an kai ga ana jifansa, saboda mu yanzu a kaduna idon mu ya bude, ba wani gwamna da zai zo ya ce mana ai ba kudi domin a yanzu haka Malam ya kafa turbar samun kudi a Kaduna ya kuma kafa fandishon da jikokinmu da tattaba kunnenmu zasu ci gajiya domin ya yi mana aiki bilhakki da gaskiya sannan kuma komai a bayyane yake.

Exit mobile version