Abdullahi Muhammad Sheka" />

Babu Gwamnatin Da Ta Yi Wa POS Tsari Kamar Ta Ganduje – Bizi

DAKTA AMINU AMINU BIZI fitacce kuma masani a kan harkokin hada-hadar kudade da sauran mu’amalolin kudi, kazalika wakilin Babban Bankin Kasa (CBN) a harkokin hada-hadar kudade ta zamani, sannan Babban Manajan Darakta na Kamfanin Bizi Mobile, wakilin bankuna ta fuskar gudanar da bitoci na wakilai daban-daban na harkokin hada-hadar kudade irin na zamani. A tattaunawarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, ya bayyana matakin harajin da Babban Bankin Kasa, ya gindaya da cewa, doka ce wadda aka yi tun a shekarar 2012, sannan ya jinjina wa kokarin Gwamnatin Jihar Kano, bisa batun tsaftace harkokin hada-hadar kudade ta hanyar POS. Ga dai yadda tattaunawar tasu kasance:

 

Duk da kasancewarka sananne ta fuskar harkokin yada labarai, amma dai za mu so ka gabatar wa da mai karatu kanka?

Alhamdulillahi!Kamar yadda aka sani sunana Dakta Aminu Aminu Bizi, Masani a harkokin hada-hadar kudade da sauran mu’amalolin kudi, wakilin Babban Bankin Kasa (CBN) a harkar hada-hadar kudade ta zamani, Babban Manajan Daraktan Kamfani Bizi Mobile, wakilin Bankuna ta fuskar gudanar da bitoci ga wakilai daban-daban (Agent-Agent) na harkokin hada-hadar kudade irin na zamani.

 

Za mu so ka yi mana karin haske a kan shirye-shiryen baje kolin bankuna da aka gudanar a kwanakin baya a Kano?

Gaskiya ne, kamar yadda aka sani an gudanar da wannan bikin baje koli wanda aka fara bara, wanda mai Martaba Sarkin Kano, a matsayinsa na Masani a wannan bangare ya bayar da kofar Fadarsa, inda aka gudanar da wannan bikin baje koli, wanda akalla an bude wa jama’a asusun ajiya da ya haura dubu 40 a cikin mako guda.

Ganin yadda aka samu nasara a karon farko yasa aka bukaci sakewa a karo na biyu, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Jihar Kano, duk da cewa shi wannan ba a ce ba a samu nasara ba, amma dai an dan gamu da ‘yar tangarda, amma dai shi ma an samu nasarar bude asusun ajiya da yawa da kuma sama wa jama’a lambar BBN.

 

An ji Babban Bankin Kasa ya bujiro da sabuwar dokar harajin fitar da kudade da kuma ajiyarsu a Bankunan  wasu Jihohi shi da na kasar nan, shin me za ka ce kan wannan sabuwar doka?

Kamar yadda aka sani, ita wannan doka ba yau ko yanzu aka fara ta ba, an kafa wannan doka tun shekara ta 2012, wanda aka cigaba da wayar da kan mutane wanda har kullum muna fada wa mutane cewar, akwai lokaci da zai zo wanda kuma Allah shi ne zamani, duk yadda zamani ya zo ba yadda za ka yi da shi illa sai ka bi shi, domin idan ma ba ka bi shi ba, ina mai tabbatar maka da cewa, zai yi tafiyar ruwa da kai.

Wannan tasa nake kira ga al’umma ‘yan’uwana, musamman mutanen Arewa, Uwa-Uba Kano da su yi hakuri a fahimci wannan tsari, domin ina tabbatar ma da cewa, a kan wannan tsari babu gudu babu ja da baya, dole sai an aiwatar da wannan tsari. Babu wani dalili da zai sa Gwamnati ta janye wannan kudiri da ta gabatar, fatana a nan kawai shi ne jama’a su fahimci tsarin domin amfana da abin da ya kunsa.

 

Kasancewarka Masani a wannan bangare, me zai hana ka yi wa jama’a dalla-dalla ko watakila Allah zai sa su fi fahimtarka fiye da bayanin Babban Bankin Kasa?

Abin da ake magana a kai shi ne, mun sha fada wa jama’a cewa, wani lokaci zai zo da ba za ma ka ga kudin lakadan ba, hakan ta fara bayyana musamman idan kana bukatar canji. Bari ka ji yadda al’amarin yake, kudin nan fa kudi ake sa wa a buga su, da za a yi maka gwari-gwarin abin da ake kashewa a kan buga kowace ta kardar Naira, wani cewa zai yi karya ne.

Saboda haka, tunda Allah ya kawo mu zamani wannan wayar ta zo ina zaune cikin dakina zan iya dauko kudi daga asusun ajiya ta bankina na tura wa wani, domin biyan wani ciniki ko makamancin haka.

Idan har Allah ya kawo mu irin wannan lokaci, ban ga dalilin da zan je banki na rungumo kudi Naira Miliyan goma domin biyan kudin gidan da na saya a wurin wani ba? Bayan zan iya yin tiransifa daga wayar hannuna cikin kwanciyar hankali ko na yi boko ko ban yi boko ba, babban Bankin Kasa, ya saukaka abubuwan nan. Dole ce tasa domin buga takardun kudin ba zai cigaba da yiwuwa ba alhalin da tattalin arziki ke ciki. Kamar yadda aka sani tattalin azikin kasar nan ya dogara kacokan a kan Man Fetur, amma yanzu ba shi duniya take ya yi ba, wannan harkokin hada-hadar kudaden irin ta zamani shi duniya ke ya yi.

 

Kukan da Jama’a suke yi musamman ‘yan kasuwa shi ne, cajin da ake kan kowacce Naira dubu 500,000,00 ya wuce hankalin jama’a?

Madallah an zo wurin, ba cewa aka yi idan za ka ajiye ko daukar Naira dubu 500,000, sai ka biya ba, a’a abin da ya kai Naira dubu 500,000, da doriya shi ne aka ce za ka biya kaso 2% na wannan abin da ya haura a kan Naira dubu 500,000  din, wannan ne kadai banki zai caje ka. Wannan tasa dole a yi wa kafafen yada labarai godiya domin kokarin da kuke yi na wayar da kan al’umma kan duk wani al’amari da ya bayyana. Duk wanda ya zo cira ko ajiyar Naira dubu 500,000 cas ko dari ba wanda zai caje ka, wannan shi ne abin da dokar ta ce. Saboda haka, muna da shawarwari da za mu baiwa Babban Banki, domin samun saukin gudanar da wannan tsari.

 

An ji bullar wata jita-jita cewa, masu amfani da POS a Unguwanni dole su je su yi rijista, shin da wace Hukuma ko Kamfani za su yi wannan rijista, kuma mene ne dallin yin hakan?

Alhamdulillahi, wannan wata gabace da duniya ya kamata ta san me ake ciki, babu shakka Gwamnatin Jihar Kano, ta yi rawar gani matuka, domin kuwa na fada cewa, dukkannin  Gwamnatocin Kasar nan, babu wadda ta ti kyakkyawan tsari a kan harkar POS, kamar Gwamnatin Ganduje. Kasancewar Gwamnatin Ganduje, ta yi la’akari da matsalolin da ke cikin harkar POS, musamman ganin yadda ‘yan damfara suka shiga cikin harkar wadda ake cutar da al’umma kwarai da gaske, musamman mutanenmu na kauyuka da Kananan Hukumomi, wadanda ba su yi ilimin boko ba, wadanda ba su baiwa lambar sirrin ajiya muhimmanci ba. Za ka iske Ma’aikata 100, a wata Karamar Hukumar, idan an yi albashi su baiwa mutun guda katin cirar kudadensu ya taho wurin Agent, domin  cirar masu albashinsu sai su ba shi lambar fin dinsu. Idan aka yi rashin sa’a, ba Allah a zuciyar Agent din, idan ya fahimci lambar fin din da sauran wasu abubuwa da ake bukata ajikin katin fitar da kudaden mutane, abin da zai biyo baya shi ne, sai dai ka ji fita alat ana kwashe ma kudi daga asusun ajiyarka.

Saboda ganin wannan matsala, Gwamnatin Ganduje ta karkashin Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki ta Jihar Kano, ta bi diddigin yadda ake samun lasisin fara amfani da POS, kasancewa ana samun korafe-korafe domin masu amfani da wannan POS, sun shigo da yawa, saboda haka Babban Bankin Kasa, ta shaida wa wakilin Jihar Kano cewa, akwai wakilin CBN (consultan), Bizi Mobile, idan aka same shi za a samu dukkanin bayanan da ake bukata domin tsaftace harkar PSO.

Wannan tasa Ma’aikatar Harkokin Kasuwanci da Ciniki ta Jihar Kano, ta neme ni wanda aka fito da tsare-tsare, a ka’ida ina son a fahimci wannan abin da zan fada, dokar Babban Bankin Kasa ta ce, banki ba zai ba ka POS ba, har sai kana da shaidar amincewa daga Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki ta Jihar Kano, wannan doka tana nan kuma ga kwafinta nan zan ba ku ‘Yan Jarida, an bar abubuwa kara zube, su bankuna kudi ne kawai a gabansu.

Ita kuma Gwamnati tana kare hakkin al’ummarta ne, wani abin takaici shi ne, akwai wasu kananan Kamfanoni masu kanaanan lasisi su ma Bankin CBN, ta ce za su iya ba da POS, kuma dukkaninsu daga Legas suke, sun shigo wasu ko Ofis ba su da shi a Kano, wannan ya kamata jama’a su san wannan ba karamar barazana ba ce.

Don haka, an karya dokar domin cewa aka yi, ba za ka baiwa mutum POS ba, sai ka ga takarda daga Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki, wannan ta sa tunda Gwamnatin Kano, ta amince da ba mu aikin, guda daga cikin tsare-tsaren da za mu fara aiwatarwa shi ne, za mu yi dukkanin abin da ya kamata, domin kare mutuncin al’ummar Jihar Kano, wannan tasa ba wai kawai ka zo ka biya
kudin rijsita shi ne matakin karshe na ba ka shaida ba, a’a sai mun ba ka faom ka je mai unguwarka ya tabbatar da amincewa da kai tare da samun wani mutum guda sananne wanda zai zamo ma garanto tare da sa hotonsa ko wani ID card amintacce.

A karshe, muna fatan samun hadin kan al’umma tare da goyon bayan tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kano, domin tsafatace wannan harka da a halin yanzu ke neman zama ruwan dare gama duniya wadda kuma ke cike da matsaloli masu yawa.

 

Za a cigaba in sha Allahu.

 

Exit mobile version