• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

by Rabilu Sanusi Bena
3 months ago
Kannywood

Daya daga cikin manyan furodusoshin da ke jan zarensu a Masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda, a wata tattaunawa da ya yi da Jarumar Kannywood Hadiza Gabon, a cikin shirinta mai taken ‘Gabon’s Room Talk Show’, ya bayyana batutuwa da dama; kama daga burin da yake da shi a masana’antar da kuma irin dimbin kabakin arzikin da ya ce akwai a masana’antar.

Maishadda, wanda ya shafe shekaru fiye da 15 a matsayin mai daukar nauyi (Furodusa) ya ce; matukar ka samu kanka a wannan masana’anta ba tare da ka sharbi kabakin romon arzikin da Allah ya ajiye a cikinta ba, to abu daya ne zuwa biyu; watakila ka samu dama, amma ba ka yi amfani da ita yadda ya kamata ba, ko kuma ba ka yi abin da ya dace a lokacin da ka samu kanka a masana’antar ba.

  • Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
  • Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tunda farko, da yake amsa tambaya a kan dalilin da ya sa ba a gan shi a wajen bikin mawaki Dauda Adamu Kahutu Rarara da Amaryarsa, Aisha Humaira ba, sai ya kada baki ya ce; ba komai ne ya hana shi halartar bikin ba, illa wata tafiya da ta kama shi zuwa birnin Legas, a daidai lokacin daurin auren masoyan.

“Maganar rashin halartar daurin auren Rarara da Aisha Humaira ina da dalili, sakamakon tafiya da na yi zuwa Legas a lokacin da aka daura auren. Bikin Rarara, bikinmu ne; domin kuwa asali ma ni ne sanadiyar da ma’auratan suka hadu tun da farko, a wani lokacin baya, mun taba yin aikin waka tare da Rarara; inda ni na dauki nauyin wakar a wancan lokaci, to bayan mun kamala; sai na nemi mutane su yi mana ‘reposting’ na wannan wakar a shafukansu na sada zumunta.”

“Daga cikin wadanda suka yi wannan ‘reposting’, akwai ita Aisha Humaira, to a wancan lokacin ni na nuna wa Rarara irin kokarin da ta yi wajen yada wakar ga mutane, ya kuma ji dadi sosai, daga nan ne na bukaci idan za mu yi wata wakar a sanya ita Humairan a ciki, saboda a wancan lokacin kamar kawa take a wajena; shi ne ma har muka yi aikin wakar ‘Dogara ya dawo’ tare da ita”, in ji Maishadda.

Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana.

Bashir ya kara da cewa, yanzu kamar yadda ake daukar fim din ‘Alakata da Nana Firdausi’, har wasu ma ke tunanin ko akwai maganar aure a tsakaninmu, duk da dai Allah ne ke yi; saboda yanzu haka, matata ’yar fim ce. Don haka, zuwa yanzu dai babu wani batu na aure tsakanina da Nana, kawai dai muna da fahimtar juna tsakaninmu, sannan kuma na yi amanna da yanayin aikinta, saboda duk wani aiki da za mu yi tare da ita; ina yaba aikin nata kwarai da gaske, saboda yadda ta ke mayar da hankali wajen ganin ta yi abin da ya dace, musamman ma aikin kamfanina.

Lokacin da yake amsa tambaya a kan burin da yake da shi a wannan masana’anta, Bashir ya ce; babu wani burin da yake da shi a yanzu da ya wuce a ce watarana ya dauki nauyin fim a wata kasa daban, ba Nijeriya ba; musamman Kasar Indiya. 

“Burina yanzu a Masana’antar Kannywood, bai wuce ganin na zama ‘International Furodusa’ ba, wato ya kasance ina yin fina-finai ba a iya nan gida Nijeriya ba, har ma da kasashen duniya; musamman ma Kasar Indiya”, in ji shi.

“Domin kuwa, in dai ana iya yin fim a samu riba a Kasar Indiya, to ni ma ina fatan watarana a ce nayi, hakan ya sa tun a yanzu na fara gayyato wasu daga cikin jaruman da ba Arewacin Nijeriya suke aiki ba, kamar irin su Kanayo O. Kanayo da sauran makamantansu; domin su zo su taya ni aiki. Burin da nake da shi ga wannan masana’anta mai albarka, ba zai fadu ba; domin idan da zan samu dama, zan yi abin da zai sa Kannywood ta shiga duniya kowa da kowa ya santa”. 

Ya ci gaba da cewa, harkar fim; ba karamar harka ba ce a idon duniya, kamar yadda wasu ke tunani. Dalili kuwa shi ne, a fim ne za ka samu daukaka, kudi da kuma masoya, sannan kuma a nan ne za ka bugi kirjin cewa; an san fuskarka, haka zalika an san sunanka, har inda ba ka yi tsammani ba, kuma a harkar fim ne kadai za ka taka kafarka inda ba ka taba tsammanin cewa; za ka iya takawa ba, misali a Nijeriya, duk inda gwamna ke tunanin an san shi, haka nan dan fim ma zai yi wannan tunani, domin kuwa ta hanyar fim sunansa ya zaga ko’ina.

A karshe, Bashir Abubakar Maishadda, wanda ake yi wa lakabi da ‘King Of Bod Office’, ya yi kira ga mutane da su daina raina mutum a duk inda suka gan shi, domin kuwa ba su san abin da zai zama a nan gaba ba, har ma ya yi misali da kansa, inda ya ce a farkon lokacin da ya shigo masana’antar, mutane da dama sun sha tsangwamar sa tare da toshe wasu hanyoyin da suke tunanin zai iya koyon wani abu, amma kuma yanzu da Allah ya mayar da shi abin da ya zama, sai suke mamaki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

October 4, 2025
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

September 28, 2025
Next Post
Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar

Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version