Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewar babu isassun cibiyoyin kiwon lafiya wadanda suke na matakin farko da za su iya kula da mutanen Nijeriya.
Ehinare ya bayyana cewar gwamnati za ta kawao karshen wannan matsalar ce nan ba da dadewa ba.
Ya ce barnatar da kudaden gwamnati musamman ma wadanda aka ware domin gina wurare kamar haka shine babban matsalar da take gurgunta shi wannan fanni na kula da lafiyar al’umma matakin farko..
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a kasarnan sun bayyana cewa rashin inganta cibiyoyin kiwon lafiya da suke matakin farko na daga cikin dalilan da suke kisan mata akalla kashi 80 cikin 100 a Nijeriya.
Tolu Fakeye ya sanar da hakan ne a taron kungiyar likitocin da suka kware a kimiyyar hana yaduwar cututtuka ta kasa (EPiSON) da aka yi a garin Jos, jihar Filato.
EPiPSON tare da hadin guiwar PACFaH@Scale ne suka shirya shi taron domin tattauna irin gudunmawar da kungiyar za ta iya yi a wajen tsara hanyoyi da za su hana ci gaba da yaduwar cututtuka a Nijeriya da kuma magance su.
Da yake jawabinsa Fakeye ya ce rashin samun shugabani na gari da sace kudaden da ake warewa cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin matsalolin da suke gurgunta harkar samar da kiwon lafiya a cibiyoyin tun bayan kafa su.
Ya kuma kara da cewar sauran matsalolin da suka mamaye cibiyoyin kiwon lafiya sun hada da rashin kwararrun ma’aikata, rashin ingantattun wuraren aiki, da kuma rashin kayayyakin aiki da dai sauran su.
Idan ba a manta ba shekaru hudu da suka wuce gwamnatin Buhari ta bayyana cewa za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 10,000 a kasarnan.
Sai dai kuma bayan wadannan shekaru cibiyoyin kiwon lafiyar na nan a cikin matsalolin da suke domin gwamnati bata tabuka wani abin a zo a gani ba, tun bayan wancan furucin da ta yi.
“A dalilin haka ne ya sa unguwar zoman gargajiya da magungunan gargajiya suke yin tasiri sannan manya manyan asibitocin da suke kasar nan suke fama da yawan cinkoson mutane.
Bayan haka Fakeye ya ce domin na tabbatar da an samu mafita game da wannan matsalar kamata ya yi ma’aikatan kiwon lafiya, malaman jami’o’i, da duk sassan gwamnati su hada hannu domin farfado da shi wannan fanni.