Babu Kunya In Ana Rayuwa Cikin Kristi

Kristi

Wurin Karatu – 1 Bitrus 4:16

“Amma in wani ya sha wuya a kan shi kirista ne, to kada ya ji kunya, sai dai ya daukaka Allah Saboda wannan suna” (1 Bitrus 4:16)

Shalom!

Kowane irin rayuwa mutum ke yi, zabi ne. Duk rayuwan da mutum ya zaba wa kansa ko mai kyau ko marasa kyau, a karshe zai bada lissafi a gaban Allah Ubangiji a Raman tashin matattatu. Duk wanda ya zabi rayuwa irinta jiki ko ta Ruhaniya a karshe akwai sakamako.

Manzo Bitrus ya tabbatar mana a chikin wannan ayar da cewa; duk wanda “ya sha wuya a kan shi Krista ne, to kada ya ji Kunya, sai dai ya daukaka Allah saboda girman sunansa.”

Watau matuka mutum Kristan ne na gaskiya, to ya kwana da sani cewa akwai shan wuya sabili da suna Yesu Almasihu. A chikin Linjila Yesu Almasihu ya dau lokaci yana koyaswa Almajiransa da mabiyansa cewa, za a tsananta masu domin sunansa. Yesu ya umurci mabiyansa dasu kaunaci magabtansu (Matiyu 5:43 – 48). Yesu Almasihu ya bai wa Kristan duniya wannan umurnin ne domin yana sane da gaban da zai shiga tsakani Kristan duniya da wadanda basu yi imani dashi Yesu Almasihu. Domin Yesu da kansa ya tabbatarwa Kristan duniya da cewa kune, “Gishiri da hasken duniya” (Matiyu 5:13 -16). Watau duk Krista na gaskiya na da wata rayuwa na musama da ya bambanta shi da kowane irin mutum a duniya.

Rayuwa Kristan duniya bata boyuwa a ko ina a kuma kowane lokaci. Rayuwa chikaken Krista tana daidai ne da yadda gishiri ke a chikin abinci da bata boyuwa domin dandanonta amma a bayane ne, matuka mutum zai ci abincin. Kuma rayuwan Krista na gaskiya na nan a bayane kama yadda hasken wuta kan bayana a chikin duhu. Kama babu yadda duhu ta iya boye haske ko lullubeta, to haka ne rayuwan Krista na gaskiya bata boyuwa a ko ina, matuks Krista ya bayana a ko ina.

Rayuwan Krista na gaskiya wata irin rayuwa ne irin ta tsarki. To duk mutumin da ke da rayuwa irinta tsarki a chikin duniya na da chikaken kalubali da marass tsarki. Yesu ya tabbatar mana da cewa babu yadda haske da duhu zasu yin tarayya da juna.

Abinda ya bambanta Krista da kowane irin mutum shine, rayuwa kauna ga kowane irin mutum. Yesu Almasihu ya umurci Kowane Krista na gaskiya da cewa, “Su kaunaci magabtansu kuma su yi wa masu tsananta masu addu’a”. Wannan umurnin da Yesu Almasihu ya bai wa Kristan duniya shine bambancin da ke tsakanin Krista da kowane irin mutum. Domin baya yiwuwa, a ce mutum ya kaunaci magabtansa ko kuwa ya yi wa wanda tsananta masa addu’a. Babu mai iya yin wannan rayuwar sai dai Kristan duniya na gaskiya.

Bambanci rayuwan Krista tawurin ikon Allah, wata rayuwa ne da ke kunshe da albarku masa yawa. Watau rayuwan Krista chikin Kristi, wata rayuwa ne chikin ruhaniya da ya bambanta Krista da masu rayuwa a chikin jiki. Domin Krista na rayuwarsa a chikin Ruhaniya ne. Rayuwa chikin Ruhaniya na da sabani da irin rayuwa irin ta jiki. Domin da haka duk masu rayuwa chikin jiki, doles me su sami sabani da kowane Kristan da me rayuwa chikin Ruhaniya.

Rayuwan Kristan gaskiya a kullum na hannun riga, da kowane irin mutumin da ba Krista bane.

A chikin rayuwa Krista watau yakamata rayuwa ne a chikin Kristi, domin da haka ba abin kunya ba ne. Domin rayuwa ne mai albarka, kuma rayuwa ne da ke, da tabbacin cheto. Domin da haka babu yadda Krista zai ji kunya ko tsoron yin rayuwarsa a matsayin Krista.

Tarihi ta shaida cewa rayuwan kristan na gasiya ya zama  abin misali ga kowane zamani baya zama abin misali bane amma misali ne ga kowa.

In kuwa rayuwa Krista abin misali ne, to ashe rayuwan Krista abin sha’awa ne da kuma kwaikoyo.

Duk Kristan da ke jin kunya rayuwarsa a matsayinsa na Krista, to ba chikaken Krista bane. Domin rayuwan kristan gaskiya abin alfahari ne da me kunshe da farin chiki. Rayuwan Krista na gaskiya, wata rayuwa ne da ke kunshe da ababuwan da duniya ba zai, iya bai wa Krista ba, sai dai tawurin imaninsa chikin Yesu Kristi mai cheton duniya. Ko da shike raywan Krista na chikin hatsari a duniya domin kiyeyan da ake yi mashi, amma kuma ba abin kunya bane. Domin da haka muna kira ga kowane Krista da a yi rayuwa irin ta Kristi, watau rayuwa chikin tawaliu, kauna, gaskiya da kyawawan misalai ga magabtansa da kuma yiwa masu tsananta masu addu’a. Domin wannan umurni ne daga Ubangiji Allah. Kuma doles ne Krista ya zama gishiri da hasken duniya a ko ina domin ya bambanta kansa daga kowane irin mutum. Domin tawurin kyawawan rayuwa me za a sank da cewa kai chikaken Kristan.

Ya Allah ka bamu ikon rayuwa irinta Yesu Almasihu da kuma rayuwa irinta tsarki da biyyaya ga Allah Ubangiji. Amin Thuma Amin.

Shalom! Shalom!! Shalom!!!

Exit mobile version